Bayan ICPC, El Rufai Ya Maka Hukumar DSS a Kotu, Ya Gabatar da Manyan Bukatu 3
- Malam Nasir El-Rufai ya nemi kotu ta soke tuhumar da hukumar DSS ke masa tare da biyan sa diyyar Naira biliyan biyu
- Lauyoyin Nasir El-Rufai sun gabatar da hujjoji guda 17 inda suka ce tuhumar ta saba wa hakkin dan adam da kundin tsarin mulki
- Mai Shari'a Joyce Abdulmalik ce za ta saurari wannan bukata a ranar 25 ga watan Fabrairu, 2026 a babbar kotun tarayya da ke Abuja
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya shigar da buƙata a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, yana neman alkali ya yi watsi da tuhumar da DSS ta shigar kansa.
Malam El-Rufai ya bayyana cewa tuhumar mai lamba FHC/ABJ/CR/99/2026 ba ta da tushe a shari'a, sannan tana matsayin cin zarafi da cin mutuncin tsarin shari'ar ƙasar nan.

Source: Twitter
Mai taimakawa El-Rufai kan yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ne ya sanar da wannan mataki, a cikin sanarwar da aka wallafa a shafin tsohon gwamnan na Facebook.
Manyan buƙatun da El-Rufai ya miƙa wa kotu
A cikin sanarwar, Muyiwa Adekeye ya bayyana cewa za a saurari ƙarar a ranar 25 ga Fabrairu, 2026, a gaban Mai Shari'a Joyce Abdulmalik.
Lauyoyin El-Rufai sun gabatar da hujjoji guda 17 domin neman kotu ta soke wannan ƙara, inda suke neman waɗannan abubuwa:
- Soke tuhumar: Neman kotu ta soke tuhumar saboda ba ta nuna wani laifi da doka ta sani ba, kuma an shigar da ita ne kawai domin cin zarafin sa.
- Wanke shi: Neman kotu ta wanke shi daga dukkan zarge-zargen tunda babu kwararan hujjoji a kansa.
- Biyan diyya: El-Rufai ya nemi kotu ta tilasta wa hukumar DSS biyan sa Naira biliyan biyu a matsayin diyya na ɓata masa suna da kuma amfani da ikon gwamnati ba ta yadda ya dace ba.
Muyiwa Adekeye ya bayyana cewa:
"An shigar da wannan buƙatar ne domin nuna cewa tuhumar da ake masa ta saɓa wa kundin tsarin mulki kuma ba ta da kwararan hujjoji."
Hujjojin da lauyoyin suka gabatar
Lauyoyin sun bayyana cewa wannan ƙara ta saɓa wa haƙƙoƙin El-Rufai na ɗan adam, ciki har da sashe na 36 (5) wanda ya ce kowa ba shi da laifi har sai kotu ta tabbatar, da kuma sashe na 39 da ya ba da ƴancin faɗar albarkacin baki.
Sun kuma jaddada cewa tuhumar ta saɓa wa sashe na 36 (12) na kundin tsarin mulki wanda ya haramta hukunta mutum kan laifin da ba a rubuta shi a matsayin laifi a cikin dokar ƙasa ba.
Haka kuma, lauyoyin sun sanar da shugaban hukumar DSS a hukumance game da waɗannan takardu da suka shigar, tare da bayyana sunayen dukkan lauyoyin da za su kare El-Rufai a kotu.

Source: Twitter
Kallo ya koma babbar kotun tarayya
Lauyoyin sun iƙirarin cewa hukumar ta DSS tana gudanar da wannan shari'a ne cikin mummunar manufa da kuma nuna son rai na siyasa domin murƙushe tsohon gwamnan.
Wannan takaddama dai ta samo asali ne daga hirar da El-Rufai ya yi a gidan talabijin na Arise News inda aka zarge shi da kutse a wayar Nuhu Ribadu, mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro.
Idon duniya yanzu ya karkata ga zaman kotun na gobe domin jin matakin da alkali zai ɗauka kan wannan buƙata ta El-Rufai na neman Naira biliyan biyu a matsayin diyya.
El-Rufai ya maka ICPC a kotu
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Malam Nasir El-Rufai ya shigar da kara gaban kotu kan samamen da hukumar ICPC ta kai gidansa na Abuja.
Tsohon gwamnan ya bukaci kotun ta ba da umarnin a biya shi diyyar Naira biliyan daya saboda bata masa suna da shiga gidansa ba bisa ka'ida ba.
El-Rufai ya gabatar da hujjojinsa a gaban kotu a kokarin tabbatar da cewa samamen da aka kai gidansa ya sabawa kundin tsarin mulki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

