Majalisa Ta Amince da Nadin Malamin Addini a Matsayin Mataimakin Gwamna a Najeriya

Majalisa Ta Amince da Nadin Malamin Addini a Matsayin Mataimakin Gwamna a Najeriya

  • Majalisar dokokin jihar Bayelsa ta amince da nadin sabon mataimakin gwamn wanda Douye Diri ya yi don maye gurbin wanda ya rasu
  • Nadin ya biyo bayin bayan rasuwar Lawrence Ewhrudjiakpo wanda ya yi bankwana da duniya bayan ya yanke jiki ya fadi a watan Disamban shekarar 2025
  • Majalisar dokokin ta Bayelsa ta amince da nadin Fasto Peter Ekpe a matsayin wanda zai hau kan kujerar mataimakin gwamnan jihar

​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Bayelsa - Majalisar dokokin jihar Bayelsa ta amince da naɗin sabon mataimakin gwamnan jihar.

Majalisar dokokin ta amince da nadin Peter Akpe a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar.

Jihar Bayelsa ta yi sabon mataimakin gwamna
Sabon mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Fasto Peter Ekpe Hoto: @staypatient
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce majalisar ta tabbatar da naɗin Peter Akpe ne yayin zamanta na ranar Talata, 24 ga watan Fabrairun 2026 da safe.

Wane ne Peter Ekpe?

Kara karanta wannan

Amurka ta kawo shawara kan hukuncin wanda ya taba mutuncin Manzon Allah SAW a Najeriya

Peter Akpe, wanda babban fasto ne, ya yi aiki a matsayin shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Jihar Bayelsa a ƙarƙashin Gwamna Douye Diri kafin naɗin nasa.

Kasancewarsa babban malamin addini da cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) ta naɗa, Akpe ya yi aiki a ɓangarori daban-daban da suka haɗa da aikin gwamnati da kuma siyasa.

Jaridar TheCable ta ce ya yi aiki a hukumomin ma’aikatan gwamnati na jihohin Rivers da Bayelsa kafin ya tsunduma cikin harkar siyasa gadan-gadan.

Peter Ekpe ya goge a siyasa

Fasto Peter Akpe ya kasance ɗan majalisar dokokin jihar Bayelsa na tsawon wa'adi biyu daga shekarar 2011 zuwa 2019, inda ya riƙe muƙamin shugaban masu rinjaye a tsawon lokacin da ya yi a majalisar.

Haka zalika, ya taɓa yin kwamishina tsakanin shekarar 2008 zuwa 2011 a karkashin gwamnatin Seriake Dickson.

Wannan amincewa ta majalisa ta share fagen rantsar da shi a matsayin sabon mataimakin gwamna.

Ekpe ya maye gurbin Lawrence Ewhrudjakpo

Naɗin Fasto Peter Akpe ya biyo bayan rasuwar Lawrence Ewhrudjakpo, tsohon mataimakin gwamnan jihar, wanda ya rasu a watan Disambar da ya gabata.

Kara karanta wannan

Abin da Tinubu ya gayawa Gwamna Abba kan siyasar Kano bayan kalaman Kwankwaso

Sanata Lawrence Ewhrudjakpo dai ya yanke jiki ya fadi a ofishinsa da ke cikin gidan gwamnatin Bayelsa, inda aka garzaya da shi asibitin tarayya (FMC) amma rai ya yi halinsa.

Jihar Bayelsa ta yi sabon mataimakin gwamna
Fasto Peter Ekpe wanda majalisar Bayelsa ta amince da nadinsa a matsayin mataimakin gwamna Hoto: @TheresaTekenah
Source: Twitter

Karanta wasu labaran kan jihar Bayelsa

Tinubu ya yi ta'aziyyar mataimakin gwamna

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya nuna alhininsa kan rasuwar mataimakin gwamnan jihar Bayelsa.

​Shugaba Tinubu ya mika sakon ta'aziyyarsa ga gwamnati da al’ummar jihar Bayelsa kan rasuwar marigayi Lawrence Ewhrudjakpo.

Mai girma Bola Tinubu ya bayyana marigayi Ewhrudjakpo a matsayin jajirtaccen mutum mai gaskiya da rikon amana, wanda ya yi wa jihar Bayelsa da Najeriya hidima cikin kishin kasa da sadaukarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng