Babban Alkali Ya Dauki Muhimmin Mataki kan Shari'ar Abubakar Malami da EFCC

Babban Alkali Ya Dauki Muhimmin Mataki kan Shari'ar Abubakar Malami da EFCC

  • An samu sabon alkalin da zai ci gaba da jagorantar kararrakin da hukumar yaki da cin hanci ta EFCC ta shigar kan tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami
  • Shugaban alkalan babbar kotun tarayya, mai shari'a John Tsoho, ya mika kararrakin gaban mai shari'a, Joyce Abdulmalik
  • Hukumar EFCC dai ta shigar da kararraki guda biyu kan tsohin Ministan na shari'a da wasu mutum biyu kan zarge-zargen da suka shafi almundahanar kudi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban alkalan babbar kotun tarayya, John Tsoho, ya mika kararrakin da EFCC ta shigar kan Abubakar Malami ga sabon alkali.

Mai shari'a John Tsoho ya mayar da kararrakin guda biyu da EFCC ta shigar kan tsohon Ministan na shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya (AGF), zuwa hannun wani sabon alkali.

Alkali ya sa lokacin sauraron shari'ar Malami da EFCC
Tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami Hoto: Abubakar Malami, SAN
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta ce an tura kararrakin zuwa hannun Joyce Abdulmalik, wacce ta sanya ranar 27 ga watan Fabrairun 2026 domin ci gaba da sauraron kararrakin.

Kara karanta wannan

Bayan ICPC, El Rufai ya maka hukumar DSS a kotu, ya gabatar da manyan bukatu 3

Alkali ya janye daga shari'ar Malami da EFCC

Wannan sauyi ya biyo bayan janyewar da Mai shari'a Obiora Egwuatu ya yi daga shari’ar.

Mai shari'a Obiora Egwuatu ya janye kansa ne daga jagorantar shari’o’in guda biyu a ranar 12 ga watan Fabrairu, inda ya dogara da dalilai na kashin kansa da kuma tabbatar da adalci, jaridar Businessday ta kawo labarin.

Hukumar EFCC tana tuhumar tsohon Ministan ne kan zarge-zarge guda 16 da suka shafi safarar kuɗaɗen haram.

EFCC na da tuhume-tuhume kan Malami

Hukumar yaƙi da cin hancin ta bayyana a watan Disambar 2025 cewa, ta gano kadarori na kimanin Naira biliyan 212 mallakar Malami a matsayin ɓangare na binciken da take gudanarwa kan lokacin da yake kan kujera.

An gurfanar da Malami ne tare da ɗansa, Abubakar Abdulaziz Malami, da kuma matarsa, Bashir Asabe, kan zargin safarar kuɗaɗe har N8,713,923,759.49.

Sai dai kamar yadda rahoto ya gabata, waɗanda ake tuhumar sun musanta aikata laifin a gaban hukuma.

Kara karanta wannan

Akwai kura: Wasu manyan alkalai a Najeriya na iya shiga matsala da NJC ta fara bincikensu

A wata ƙarar ta daban, EFCC tana neman kotu ta ba da umarnin kwace kadarori guda 57 waɗanda ake zargin an same su ne ta hanyar ayyukan haram.

Za a ci gaba da sauraron shari'ar Abubakar Malami da EFCC
Abubakar Malami a harabar kotu Hoto: @OfficialEFCCNg
Source: Facebook

Hukumar EFCC na shari'a da Malami

Tun da farko, mai shari'a Emeka Nwite ne ya jagoranci shari’o’in a lokacin hutu na kotun. Bayan hutun, mai shari'a John Tsoho ya tura maganar zuwa hannun Egwuatu, wanda daga baya ya janye tare da mayar da shari’ar zuwa ga shugaban alkalan.

A halin da ake ciki, Malami da ɗansa suna kuma fuskantar shari’a a gaban mai shari'a Joyce Abdulmalik kan wasu tuhume-tuhume guda biyar da suka shafi tallafa wa ta’addanci da kuma mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba.

Tsohon minista ya yi bayani a gaban kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami SAN, ya gayawa kotu hanyoyin da ya samu kudadensa.

Abubakar Malami ya shaidawa kotu cewa kadarorin da EFCC ke neman kwacewa a hannunsa, ya mallake su ne ta hanyoyi halastattu kuma bisa doka.

Tsohon Ministan shari'ar ya ce kudaden shigarsa da ribar da kasuwancinsa ke samarwa, sun isa suna nuna cewa an mallaki kadarorin da ake son kwacewa ne ta halastacciyar hanya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng