Shugaban Gwamnonin Arewa Ya ba Daurawa Katafaren Gida Albarkacin Ramadan

Shugaban Gwamnonin Arewa Ya ba Daurawa Katafaren Gida Albarkacin Ramadan

  • Rahotanni sun nuna cewa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya isa jihar Gombe domin fara tafsirin Ramadan da ya saba yi duk shekara
  • Shugaban gwamnonin Arewa kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya ba malamin katafaren gidan da zai zauna
  • Sheikh Daurawa yana zama a gidajen da ake ba shi a lokacin da ya zo tafsiri jihar, amma bana gwamna ya ce ya kamata a gina masa gida

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa shugaban gwamnonin Arewa kuma gwamnan Gombe, Inuwa Yahaya ya ba shi gida a jihar.

An ba Sheikh Aminu Daurawa gida a Gombe ne bayan shafe sama da shekara 20 yana zuwa jihar tafsirin Ramadan duk shekara.

Kara karanta wannan

Babu wasa: Tinubu ya tara gwamnoni, ya gaya masu shirinsa don magance rashin tsaro

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da gwamna Inuwa Yahaya
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa a hagu da Gwamna Inuwa Yahaya a dama. Hoto: Imam Dr. Muhammad Aminu Ibrahim Daurawa|Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Legit Hausa ta bayyana cewa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya ya yi maganar gidan ne yayin tafsirin ranar 5 ga Ramadan 2026 kamar yadda ya wallafa a Facebook.

Gwamna Inuwa ya ba Aminu Daurawa gida

Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa 'yan kwanaki kafin shigar watan Ramadan shugaban gwamnonin Arewa, Inuwa Yahaya ya kira shi a waya cewa ya ba shi gida a Gombe.

Bayanin malamin ya samo asali ne bayan wani ya nemi a roki Allah ya ba shi gida yayin da ake tafsiri, sai malamin ya ce:

"Wannan munasabar ta sa za mu yi wa Mai girman gwamnan Gombe godiya.
"Ya kira ni saura kwana biyu na iso wannan gari, ya kira ni a waya ya ce to Malam na gina maka gida. So nake in ka zo ka wuce gidanka kai tsaye komai an gama."

Da ya ke bayani game da abubuwan da aka yi a gidan, Sheikh Daurawa ya ce gwamnan ya ce masa:

Kara karanta wannan

Buda baki: Shugaba Tinubu ya sha ruwa tare da wasu gwamnoni a watan Ramadan

"Komai an hada, an sa sola awa 24, an hada maka ruwa, an sa gado da katifa, an sa kujeru, an hada madafi, an yi komai, so nake da ka zo ka wuce gidanka."
Sheikh Aminu Daurawa yayin tafsiri a jihar Gombe
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa yana tafsiri a watan Ramadan a Gombe. Hoto: Imam Dr. Muhammad Aminu Ibrahim Daurawa
Source: Facebook

Daurawa ya je gidan da aka ba shi

Bayan bayar da labarin, Sheikh Aminu Daurawa ya bayyana cewa ya kira shugaban kwamitin da'awa Dr Muhammad Lawan sun je gidan da aka gina masa.

Ya kuma kara da cewa sun mika godiya ta musamman ga gwamna Inuwa Yahaya bisa karrama shi da katafaren gida da zai rika zama idan ya zo tafsiri jihar Gombe.

Baya ga haka, Sheikh Daurawa ya yi wa gwamnan fatan gamawa lafiya tare da rokon Allah ya kawo mutumin kirki da zai gaje shi idan ya kammala wa'adinsa na biyu a 2027.

Hukuncin karya azumi saboda wahala

A wani labarin, kun ji cewa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya amsa tambaya game da hukuncin karya azumi saboda tsananin wahala.

Kafin bayar da amsa Sheikh Daurawa ya bayyana cewa akwai bambanci tsakanin wahala da tsananin wahala a lokacin azumi.

Ya ce dole mai azumi zai sha wahala tunda ba zai ci abinci ba na wani lokaci, sannan ya kuma bayyana tsananin wahalar da za ta sa a ajiye azumi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng