Babu Wasa: Tinubu Ya Tara Gwamnoni, Ya Gaya Masu Shirinsa don Magance Rashin Tsaro

Babu Wasa: Tinubu Ya Tara Gwamnoni, Ya Gaya Masu Shirinsa don Magance Rashin Tsaro

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gayyaci gwamnonin Najeriya domin yin buda baki na azumin watan Ramadan da Lent a Aso Rock
  • Mai girma Bola Tinubi ya tabo batun matsalar rashin tsaro a jawabin da ya yi ga gwamnonin a daren ranar Litinin, 23 ga watan Fabrairun 2026
  • Hakazalika, shugaban kasar ya kuma ba 'yan Najeriya tabbacin cewa zai cika musu alkawuran da ya dauka kafin ya hau kan karagar mulki

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Mai girma Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake yin magana kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita a Najeriya.

Shugaba Tinubu ya lashi takobin cewa gwamnatinsa za ta kafa 'yan sandan jihohi domin magance matsalar rashin tsaro da ke addabar kasar nan.

Shugaba Tinubu ya sha alwashin kafa 'yan sandan jihohi
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a wajen buda baki da gwamnoni Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta ce Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da ya karbi bakuncin gwamnonin jihohi a wani taron shan ruwa (buda baki) na mabiya addinai daban-daban da aka gudanar a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Abin da Tinubu ya gayawa Gwamna Abba kan siyasar Kano bayan kalaman Kwankwaso

Bola Tinubu ya yi buda baki da gwamnoni

An gudanar da taron ne a daren ranar Litinin, 23 ga watan Fabrairun 2026 domin yin buda bakin azumin Ramadan da na Kiristoci (Lent) tare da gwamnonin.

Shugaba Tinubu ya kuma bukaci gwamnonin da su ninka kokarinsu wajen ganin sun tallafa wa al’ummomin karkara, wadanda a wasu lokutan ake mantawa da su.

“A daren nan, na karbi bakuncin gwamnonin jihohinmu a taron budan baki na addinai daban-daban yayin da Musulmi ke azumin Ramadan, Kiristoci kuma ke gudanar da azumin Lent."
“A cikin wannan lokaci mai tsarki ga manyan addinai biyu na kasarmu, ana tunatar da mu cewa bayan siyasa da manufofi, mu mutane ne masu tunani."
“Na jinjina wa gwamnonin kan kokarinsu ya zuwa yanzu da kuma shirye-shiryen tallafi daban-daban da suka gudanar a wannan wata mai alfarma. Amma kuma na kalubalance su da su kara kaimi."

- Shugaba Bola Tinubu

Shugaba Tinubu ya ba 'yan Najeriya tabbaci

Kara karanta wannan

Abin da Tinubu ya fada wa Abba da sauran gwamnoni a wurin buda baki a Abuja

Shugaba Tinubu ya ba wa ’yan Najeriya tabbacin cewa zai cika alkawuran da ya dauka kafin ya hau karagar mulki a shekarar 2023.

“Na kuduri aniyar ceto wannan kasa. Kuma muddin muna aiki tare wajen samar da makoma mai kyau ga ’yan kasanmu, to mafi alherin abubuwa na nan tafe ga Najeriya.”
“Abin da na yi wa ’yan Najeriya alkawari ba za a dage shi ba. Tsaro shi ne tushen arziki. Idan babu shi, gonaki ba za su yi albarka ba, kasuwanci ba zai bunkasa ba, sannan iyalai ba za su iya yin barci cikin kwanciyar hankali ba."

- Shugaba Bola Tinubu

Shugaba Tinubu ya yi magana kan rashin tsaro
Shugaban kasa Bola Tinubu tare da wasu gwamnoni wajen buda baki Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Me Tinubu ya ce kan rashin tsaro

Shugaban kasar ya kuma sake jaddada kudirinsa na kafa 'yan sandan jihohi domin dakile matsalar rashin tsaro, jaridar The Punch ta kawo labarin.

“Za mu kafa ’yan sandan jihohi domin dakile rashin tsaro. Wannan ba maganar siyasa ba ce; magana ce ta abin da ya kamata a aikace."
"Magana ce ta bai wa jihohi damar samun kayan aikin kare mutanensu, yayin da muke karfafa tsarin kasarmu baki daya."

Kara karanta wannan

Buda baki: Shugaba Tinubu ya sha ruwa tare da wasu gwamnoni a watan Ramadan

“Dole ne mu kasance masu kokari wajen gyara duk abin da ba ya tafiya yadda ya kamata. Dole ne mu kasance masu hadin kai wajen kare abubuwan da muke kauna."
“Najeriya za ta kasance cikin aminci. Najeriya za ta kasance mai karfi. Kuma a tare, dole ne mu jajirce wajen ganin hakan ya tabbata.”

- Shugaba Bola Tinubu

APC ta hana sayawa Tinubu fom

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC mai mulki ta yi magana kan shirin wasu kungiyoyi na saya wa Shugaba Bola Tinubu fom din tsayawa takara.

Jam'iyyar APC ta bukaci duk wasu kungiyoyin da ke shirin sayawa shugaban kasar fom don tsayawa takara a zaben 2027 da su dakata.

Shugaban jam'iyyar APC, Nentawe Goshwe Yilwatda, ne ya bayar da umarni hana saya wa shugaban kasa fom din takarar 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng