Bincike Ya Tono Ministan Buhari da Wani Mutum Sun Fitar da Miliyoyi a Kifar da Tinubu
- Binciken da jami'an tsaron Najeriya ke ci gaba da yi ya gano mutane biyu da ake zargi da ɗaukar nauyin shirin juyin mulki da N835m
- Daga cikin abubuwan da aka gano, an ce tsohon gwamnan Bayelsa, Timipre Sylva, ya bayar da N785m daga cikin kudin da aka fitar
- Sojoji sun ce an kammala bincike, ana jiran umarnin kafa kotun soja domin ta duba lamarin tare da hukunta mutanen da ake zargi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Hukumomin tsaro da ke binciken zargin shirin hambarar da Shugaba Bola Tinubu sun gano wasu mutane biyu da ake zargi da shigewa gaba kan lamarin.
Ana zargin mutanen biyu da suka hada da tsohon Ministan mai da tura Naira miliyan 835 ta wasu kamfanoni masu zaman kansu domin ɗaukar nauyin shirin hambarar da mulkin Tinubu.

Source: Facebook
Jaridar Premium Times ta ce ana zargin tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Timipre Sylva, da bayar da kaso mafi tsoka na kudin, wato Naira miliyan 785.
Ana zurfafa bincike kan shirin juyin mulki
Rahoton ya ce masu bincike sun ce an tura kudin ne ta hannun Purple Waves Limited, wani kamfanin gine-gine da ke Abuja.
An kama sakataren kamfanin, John Ebokpo, kuma yana tsare a hannun jami’an tsaro inda ake kara matsa shi a kan batun. An ce Sylva, wanda ya taba rike mukamin karamin ministan albarkatun man fetur a karkashin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, shi ne babban mai daukar nauyin shirin.

Source: Facebook
Bayanan rajista a Hukumar Rajistar Kamfanoni (CAC) ba su nuna Sylva a matsayin darakta ko mai hannun jari a Purple Waves Limited ba.
Rahotanni sun ce wani jami’in tsaro ya ce an rufe ofishin tsawon watanni hudu zuwa biyar, daidai lokacin da aka fara kama masu hannu a zargin juyin mulkin.

Kara karanta wannan
Bayan kanannaɗe El Rufai, ana zargin gwamnatin Tinubu ta shirya cafke tsohon gwamna
An kara gano wani a shirin juyin mulki
Ana kuma zargin Moses Zakwa da bayar da Naira miliyan 50 ta hannun Clay Ring Services Limited, kamfani mai rajista a Legas inda aka bayyana shi a matsayin darakta.
Ba a samu cikakken bayani a kansa ba, yayin da ake ci gaba da samun bayanai sannu a hankali game da lamarin da ya daga hankalin jami'ai.
A watan da ya gabata, Hedikwatar Tsaro ta sanar da kammala bincike tare da mikawa hukumar da ta dace sakamakon binciken.
Sojoji sun ce an gano jami’ai da dama da ake zargi da shirin kifar da gwamnati, lamarin da suka ce ya saba da ka’idoji da kima na rundunar sojin Najeriya. Rahotanni sun ce ana tsare da mutane 40, daga ciki har da manyan jami’an soja, dan sanda daya da fararen hula da ake zargi da sa ido, daukar nauyi da yada farfaganda.
Timipre Sylva ya musanta zargin juyin mulki
A baya, mun wallafa cewa tsohon Karamin Ministan Man Fetur, Timipre Sylva ya musanta hannu a shirin kifar da gwamnatin Najeriya a karkashin Shugaba Bola Tinubu.
Sylva, tsohon gwamnan jihar Bayelsa na daya daga cikin wadanda ake yada jita-jitar cewa su na da hannu a shirin juyin mulki wanda aka so kaddamarwa a watan Oktaban 2025.
Mai magana da yawun tsohon Ministan, Julius Bokoru ya ce labarin ba gaskiya ba ne, wasu yan siyasa ne suka kirkira don bata wa Sylva suna da jingina masa mummunan lamari.
Asali: Legit.ng

