'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Nuna Tsaurin Ido ga Sojoji, an Rasa Rayuka bayan Kazamin Artabu

'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Nuna Tsaurin Ido ga Sojoji, an Rasa Rayuka bayan Kazamin Artabu

  • 'Yan ta'addan Boko Haram sun shammaci dakarun sojojin Najeriya masu aikin samar da tsaro a jihar Adamawa
  • Tsagerun 'yan ta'addan sun farmaki wani sansanin sojoji a jihar Adamawa inda suka tafka barna mai girma duk da kokarin da jami'an tsaro suka yi
  • 'Yan ta'addan sun kashe dakarun sojoji tare da sace kayayyaki masu muhimmanci yayin farmakin da suka kai cikin dare

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Adamawa - 'Yan ta'addan Boko Haram sun kai wani harin ta'addanci na ramuwar gayya a jihar Adamawa.

'Yan ta'addan sun kashe sojoji uku da wata mace guda daya, a wani harin da suka mai a matsayin martani a gundumar Garaha da ke jihar Adamawa.

'Yan Boko Haram sun kashe sojoji
Shugaban sojojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa ’yan ta’addan sun kaddamar da wannan mummunan hari ne a daren ranar Asabar, 21 ga watan Fabrairun 2026 da misalin karfe 11:00 na dare.

Kara karanta wannan

Abin ya yi muni: 'Yan bindiga sun sake tafka ta'addanci ana cikin azumi a Zamfara

'Yan Boko Haram sun kai hari a Adamawa

'Yan ta'addan sun toshe hanyoyin shiga garin ta kowane bangare, inda suka rika harbi kan mai uwa da wabi kafin daga bisani su mamaye sansanin sojoji da ke wurin.

Wadanda suka tsira daga harin, wadanda aka tattauna da su, sun bayyana harin a matsayin wanda aka tsara shi daki-daki, inda maharan suka kona wata makarantar firamare.

Bayanai daga shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan sun far wa jami’an sojojin ne ba tare da sun shirya ba, abin da ya ba su damar samun nasara a kansu.

Sojoji sun gwabza da 'yan ta'addan Boko Haram

Isaiah Yerima ya bayyana cewa sojoji sun yi kokarin dakile harin amma ba su yi nasara ba, rahoton Daily Post ya tabbatar da hakan.

“Sojojin sun yi kokarin dakile harin ta hanyar musayar wuta, amma abin takaici, an mamaye daukacin sansanin sojan kuma aka kone shi kurmus.”
“Maharan sun yi wa sojojin kwantan bauna ne ta ta bangaren baya ta hanyar hanyar Lar, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar jami’an soja uku. Sannan an kashe wata mace farar hula sakamakon harsashin da ya sameta tana kokarin tserewa daga wurin tashin hankalin.”

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Ƴan bindiga sun kashe mutane 50, sun sace mata da yara a Zamfara

“Kamar yadda nake magana da ku yanzu, babu wani gini da ya rage a sansanin sojojin in ban da Cocin Living Faith. Sojojin sun rasa komai nasu, ciki har da abinci, tufafi, da sauran kayan amfaninsu.”

- Isaiah Yerima

'Yan Boko Haram sun kai hari a Adamawa
Taswirar jihar Adamawa, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan ta'adda sun kwashe makamai

An bayar da rahoton cewa maharan sun kwashe makamai daga sansanin sojan, ciki har da motar yaki mai sulke kafin su cinna wa sansanin wuta.

Yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban karamar hukumar Hong, Alhaji Usman Inuwa, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha da su bullo da wasu sababbin dabarun tsaro da za su tabbatar da dorewar zaman lafiya da jituwa a yankin.

'Yan ta'adda sun shigo Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, ya yi magana kan matsalar rashin tsaro.

George Akume ya jaddada cewa da yawa daga cikin ’yan ta’addan da ke da alhakin kashe-kashe a sassan ƙasar nan ba ’yan Najeriya ba ne, baƙin haure ne.

Sakataren gwamnatin tarayyar ya ya ce da yawa daga cikin waɗanda aka kama dangane da hare-haren baya-bayan nan ba ’yan Najeriya ba ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng