El Rufai Na Tsare a ICPC, Malamin Musulunci Ya Fallasa Abin da Ya Yi a Kaduna
- Malamin addinin Musulunci a jihar Kaduna, Sheikh Halliru Maraya, ya yi zarge-zarge kan Malam Nasir Ahmad El-Rufai
- Sheikh Halliru Maraya ya yi zargin cewa El-Rufai bai yi wa Kiristoci adalci ba wajen aiwatar da tsarin gwamnatinsa na daina daukar nauyin sauke farali
- Malamin ya kwararo yabo ga Gwamna Uba Sani kan matakin da ya dauka na dage daina daukar nauyin sauke faralin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Wani mamba a kwamitin musamman na aikin Hajji na jihar Kaduna, Sheikh Halliru Maraya, ya yi zargi kan tsohon Gwamna Nasir El-Rufai.
Sheikh Halliru Maraya ya yi zargin cewa El-Rufai ya nuna bambanci wajen aiwatar da dokar hana daukar nauyin mahajjata da ya kafa a shekarar 2015.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta kawo rahoton cewa malamin addinin Musuluncin ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a ranar Litinin, 23 ga watan Fabrairun 2027.
Sheikh Maraya ya bayyana cewa yayin da aka dakatar da daukar nauyin Kiristoci zuwa Jerusalem gaba daya, an ci gaba da daukar nauyin Musulmi karkashin wasu wasu rabe-rabe na daban.
El-Rufai ya dakatar da daukar nauyin sauke farali
Idan za a iya tunawa, a shekarar 2015 ne El-Rufai ya sanar da dakatar da daukar nauyin maniyyata zuwa aikin Hajji ko Umrah da kuma Kudus (Jerusalem), inda ya bayyana bukatar adana kudaden gwamnati da kuma rage bashin da ake bin jihar.
A lokacin, kowa ya fahimci cewa dokar ta shafi Musulmi da Kiristoci ne baki daya.
Me Sheikh Maraya ya ce El-Rufai?
Sai dai, yayin da yake jawabi a ranar Litinin, Sheikh Maraya ya nuna cewa yadda aka gudanar da tsarin ya sha bamban da yadda aka sanar da shi a farko, rahoton Daily Post ya tabbatar da hakan.
"A zahiri, tsarin ya nuna kamar ya shafi maniyyata Musulmi da Kiristoci baki daya. Sai dai, abubuwan da suka biyo baya sun nuna bambanci tsakanin abin da aka fada da kuma yadda aka aiwatar da shi."
- Sheikh Halliru Maraya
A cewar Halliru Maraya, yayin da aka dakatar da daukar nauyin Kiristoci zuwa Kudus a tsawon shekaru takwas na mulkin El-Rufai, an ci gaba da daukar nauyin tafiya zuwa Saudiyya karkashin rukunin "jami’ai" da kuma "mataimakan jami’ai".
Sheikh Maraya ya yi fallasa
Ya bayyana cewa kimanin mahajjata 985 ne aka dauki nauyinsu zuwa Saudiyya a wannan lokacin, wadanda suka hada da jami’ai 730 da mataimakan jami’ai 255.
Sheikh ya bayyana cewa rukunin "jami’ai" ya hada da ma’aikatan lafiya, malamai, da ma’aikatan gudanarwa da aka tura domin saukaka ayyukan hajji, yayin da rukunin "mataimakan jami’ai" ya kasance tamkar daukar nauyi ne kai-tsaye, wanda ya hada da kudin jirgi, masauki, abinci, da kudin guzuri.
Ga jadawalin yadda aka raba su a kowace shekara kamar yadda Maraya ya bayyana:
- 2015: Jami'ai 95
- 2016: Jami'ai 91, mataimakan jami'ai 40
- 2017: Jami'ai 89, mataimakan jami'ai 30
- 2018: Jami'ai 95, mataimakan jami'ai 45
- 2019: Jami'ai 90
- 2022: Jami'ai 100, mataimakan jami'ai 40
- 2023: Jami'ai 170, mataimakan jami'ai 100
Ya jaddada cewa a cikin wannan lokacin, babu wani bayani da ya nuna cewa gwamnati ta dauki nauyin Kirista ko guda daya zuwa Jerusalem.

Source: Twitter
Malamin ya yabi salon Gwamna Uba Sani
Sheikh Maraya ya kwatanta salon mulkin tsohuwar gwamnatin da ta Gwamna mai ci yanzu, Uba Sani, wanda kwanan nan ya dage takunkumin shekaru 11 da aka sanya wa daukar nauyin Kiristoci zuwa Kudus.
A cewar Halliru Maraya, matakin Gwamna Sani yana nuna adalci, rungumar kowa da kowa, da kuma mutunta hakkin dukkan 'yan kasa a jiha mai dauke da mabiya addinai daban-daban kamar Kaduna.
Jigo a ADC ya soke tsare El-Rufai
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigo a jam'iyyar ADC, Usman Austin, ya yi magana kan tsare Nasir El-Rufai da hukumar ICPC ke yi.
Usman Austin ya bukaci ICPC da ta gaggauta gurfanar da tsohon gwamnan na Kaduna, a gaban kotu ko kuma ta sake shi ya kama hanyar gaban shi.
Jigon na ADC ya jaddada cewa idan har akwai zarge-zarge a kan El-Rufai, to kamata ya yi a kai su gaban kotu domin a tuhume shi.
Asali: Legit.ng


