Dangote Ya Dawo Sayar da Fetur a Tsohon Farashi ga Sababbin Gidajen Mai

Dangote Ya Dawo Sayar da Fetur a Tsohon Farashi ga Sababbin Gidajen Mai

  • Matatar mai ta Dangote ta dawo da sayar da fetur a farashin N774 kan kowace lita a wasu zababbun gidajen mai da ke Najeriya
  • An takaita sabon tsarin ga wasu manyan yan kasuwa da suka kulla alaka da matatar domin saukaka farashin man fetur
  • Masu ruwa da tsaki sun fara sharhi a kan dawo da farashin, inda ake ganin zai rawar gani a kasuwar man fetur a kasar nan

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos - Matatar mai ta Dangote ta dawo da sayar da man fetur karkashin sabon tsarin rarrabawa da Hukumar kula da harkokin mai ta tsakani da 'kasa ta amince da shi.

Sabon tsarin ya kawo sauyi daga tsohon tsarin dama wa da kananan ‘yan kasuwa masu zaman kansu damar sayen fetur kai tsaye daga matatar.

Kara karanta wannan

Kwanaki 3 da shiga watan Ramadan, mutane sun fara fuskantar matsala a jihar Kano

Dangote ya dawo da sayar da fetur a kan N774
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote (hagu), gidan man NNPCL (dama) Hoto; Dangote Industries/NNPC imited
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa a yanzu, manyan ‘yan kasuwa da masu rumbunan ajiya wato defo da aka tantance ne kawai za su iya daukar kaya kai tsaye daga matatar.

Dangote ya dawo da sayar da fetur kan N774

Ita kuwa jaridar The Guardian ta wallafa cewa masu sa ido a harkokin masana’antu sun bayyana cewa komawa ga tsarin da matatar Dangote ta yi zai taimaka matuka.

Ana ganin zai kara daidaita farashi, rage tashin gwauron zabo da farashin ke yi da kuma ƙarfafa amincewa a dukkannin sassan kasuwar man fetur ta ƙasa.

Kamfanonin da aka ba damar daukar man fetur kai tsaye sun hada da Mobil/11 Plc, Total, Matrix, Rainoil, Nipco da Northwest, Ardova.

Sauran su ne kamfanonin man fetur na Bovas, Pivot, AA Rano, AYM Shafa, NNPC Limited da MRS.

Majiyoyi sun ce wannan tsari ya yi kama da wanda aka fara amfani da shi a watan Oktoban 2025, lokacin da aka bai wa wasu manyan ‘yan kasuwa kalilan damar.

Kara karanta wannan

DSS na shirin gayyatar yaran El Rufa'i, matar Dadiyata ta yi magana kan dauke mijinta

'Yan kasuwa za su mori tsarin matatar Dangote

A karkashin wannan sabon shiri, ‘yan kasuwar mai masu zaman kansu, daga ciki har da mambobin IPMAN da PETROAN, za su rika sayen fetur ne daga defo maimakon daga matatar kai tsaye.

Wani dan kasuwa a fannin ya bayyana matakin a matsayin dabarar kare jarin masu defo tare da tabbatar da wadataccen rabon kaya a fadin kasa.

Shugaban shafin Petroleumprice.ng, Olajide Jeremiah, ya tabbatar da cewa farashin da dauko man na nan a kan N774 kan kowace lita.

Sai dai an tsaurara sharuddan, domin dole mai saya ya mallaki defo mai aiki ko kuma ya kasance daga cikin manyan ‘yan kasuwar da aka amince da su.

Albishirin Dangote ga 'yan Najeriya

A baya, kun ji cewa attajirin dan kasuwa a nahiyar Afrika, Aliko Dangote, ya yi albishir ga 'yan kasa game da farashin Naira idan aka kwatanta da Dala.

Ya yaba wa manufofin gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Bola Tinubu yana cewa sauye-sauyen tattalin arziki sun fara ba da sakamakon da ake bukata.

Ya kara da cewa saboda ayyukan matatar Dangote, akwai yiwuwar farashin Dala ya fado daga nan zuwa karshen shekarar 2026, inda ya ce komai zai iya daidaita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng