Ramadan: Sanata Ya Kere Wasu Gwamnoni, Ya Tausayawa Talakawa saboda Azumi

Ramadan: Sanata Ya Kere Wasu Gwamnoni, Ya Tausayawa Talakawa saboda Azumi

  • Sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu a Majalisar dattawan Najeriya, Sanata Shehu Buba, ya gwangwaje mutanen mazabarsa da sha tara ta arziki
  • Shehu Buba Umar ya kaddamar da rabon tallafin shinkafa ga mutanen mazabarsa domim su samu sauki a watan azumin Ramadan na shekarar 2026
  • Sanatan bai tsaya iyakar nan ba, ya kuma wani kaso na shinkafar domin rabawa ga sauran yankunan Bauchi ta Arewa da Bauchi ta Tsakiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Bauchi - Sanata Shehu Buba mai wakiltar Kudancin jihar Bauchi a majalisa ya yi rabon tallafin shinkafa saboda watan azumin Ramadan.

Sanata Shehu Buba ya raba buhunan shinkafa guda 20,00 ga iyalai a jihar Bauchi domin tallafa musu a lokacin azumin watan Ramadan.

Sanata Shehu Buba ya raba shinkara a Bauchi
Sanata Shehu Buba a wajen kaddamar da rabon shinkafa a Bauchi Hoto: Mujaddadi Tv
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce Sanata Shehu Buba (mai wakiltar shiyyar Bauchi ta Kudu a karkashin jam’iyyar APC) ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 22 ga watan Fabrairun 2026 a garin Bauchi yayin kaddamar da raba tallafin.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fusata kan kashe kashe a taron APC, ya dauki kwakkwaran mataki

Sanata Buba ya raba tallafin shinkafar azumi

Ya bayyana cewa wannan tallafin zai taimaka wa Musulmi wajen gudanar da azumin Ramadan, sannan zai rage radadin matsin rayuwa ga iyalai masu rauni, jaridar Vanguard ta kawo labarin.

Sanata Shehu Buba ya ce za a raba shinkafar ne ga iyalan da suka cancanta a fadin kananan hukumomi bakwai na shiyyar tasa, wadanda suka hada da: Alkaleri, Bauchi, Bogoro, Dass, Kirfi, Tafawa Balewa, da Toro.

"Ina amfani da wannan damar na kaddamar da raba shinkafa da na tanada a matsayina na sanata. Yawan shinkafar buhu 20,000 ne mai nauyin kilo 25."
"Wannan ba shi ne karo na farko ba, kamar yadda masu magana suka fada, lokaci bayan lokaci muna kokarin mu ga mun samo abubuwan da za su taimakawa al'ummar mu, al'ummar jihar Bauchi ta Kudu don rage musu radadi na rayuwa, musamman a irin wannan wata."
"A matsayin wani mataki na mika hannun kyauta har zuwa wajen mazabata, mun ware buhuna 3,500 ga shiyyar Bauchi ta Arewa, sannan buhuna 3,000 ga shiyyar Bauchi ta Tsakiya."

Kara karanta wannan

DSS na shirin gayyatar yaran El Rufa'i, matar Dadiyata ta yi magana kan dauke mijinta

"Sauran buhunan kuma an ware su ne ga shugabannin jam'iyyar APC, zababbun kungiyoyi, da sauran masu ruwa da tsaki a fadin jihar."

- Sanata Shehu Buba

Sanata Buba Shehu ya yi rabon shinkafa
Wasu daga cikin buhunan shinkafar da Sanata Shehu Buba ya raba a Bauchi Hoto: Mujaddadi Tv
Source: Facebook

Sanata Buba ya bukaci a yi adalci

Sanata Shehu Buba ya umurci mambobin kwamitin raba tallafin da su tabbatar da adalci da gaskiya yayin gudanar da aikinsu.

Shugaban kwamitin rabon, Abdulkadir Gyengyen, ya yaba da wannan kokari, inda ya ba da tabbacin cewa za su sa ido sosai domin kauce wa karkatar da kayan tallafin.

Gwamnatin Yobe ta fadada shirin ciyarwa

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnatin jihar Yobe karkashin jagorancin Gwamna mai Mala Buni, ta ware kudi don shirin ciyarwa a watan azumin Ramadan.

Gwamnatin ta amince da fitar da kuɗi sama da Naira miliyan 398 domin shirin ciyarwa na watan Ramadan na shekarar 2026 da kuma gudanar da Tafsirai a faɗin jihar.

Hakazalika, gwamnan ya ƙara yawan wuraren ciyarwa daga 101 da suke a bara zuwa wurare 130 a faɗin kananan hukumomi 17 na jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng