Greenland, Denmark Sun Nuna Turjiya ga Amurka, Sun Ki Yarda da Bukatar Trump
- Kasashen Greenland da Denmark sun yi watsi da tayin Donald Trump na tura jirgin asibitin sojojin ruwan teku
- Greenland ta ce tsarin lafiyar jama’a a kasarsu kyauta ne, yana mai cewa ba sa bukatar wani shiri na musamman daga Amurka
- Ministan tsaron Denmark, Troels Lund Poulsen, ya jaddada cewa mazauna Greenland na samun kulawar da ta dace a gida
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Washington DC, US - Kasar Greenland da Denmark sun yi yiwa Donald Trump tsiya kan bukatarsa gare su.
Kasashen sun yi watsi da tayin Shugaban Amurka, Donald Trump, na tura jirgin asibitin sojojin ruwa zuwa tsibirin Arctic.

Source: Getty Images
Dalilin shirya tura jiragen sojojin ruwan
Rahoton ya ce an shirya tura jirgin ne domin kula da marasa lafiya da ya ce ba a kula da su yadda ya kamata, cewar AP News.
Trump ya bayyana cewa zai aike da “babban jirgin asibiti” zuwa Greenland domin kula da mutane da dama da ke fama da rashin lafiya, ba tare da bayar da karin bayani ba.
Sai dai Firaministan Greenland, Jens-Frederik Nielsen, ya wallafa a kafar sadarwa cewa, “Amsarmu ita ce a’a, mun gode,” yana mai cewa suna da tsarin kiwon lafiya na jama’a kyauta.
Ya kara da cewa a Greenland, kamar Denmark, kulawar lafiya kyauta ce ga ‘yan kasa, sabanin Amurka inda zuwa wurin likita ke bukatar biyan kudi.
Ministan tsaron Denmark, Troels Lund Poulsen, ya shaidawa gidan talabijin na DR cewa mazauna Greenland na samun kulawar da suke bukata a gida ko Denmark idan ana bukatar kulawa ta musamman.
Ya ce ba kamar akwai wata bukata ta musamman ba da za ta sa a kaddamar da wani sabon shirin kiwon lafiya a Greenland, cewar BBC.

Source: Getty Images
A ranar da Trump ya gabatar da tayin, sojojin Denmark sun kwashe wani ma’aikacin jirgin karkashin ruwa na Amurka kusa da Nuuk bayan ya nemi kulawar gaggawa.
Abin da kasashen ke kallo kan lamarin
Rundunar Hadin Gwiwar Arctic ta Denmark ta ce an dauki ma’aikacin zuwa asibiti a Nuuk bayan wata matsalar lafiya da ba a fayyace ba a cikin jirgin.

Kara karanta wannan
Trump ya durawa alkalai ashar bayan hana shi daukar mataki kan Najeriya da kasashe
Trump ya wallafa hoton da aka kirkira ta hanyar fasahar AI na jirgin ruwan asibiti na sojojin Amurka, USNS Mercy, yana mai cewa “yana kan hanya”.
Bai bayyana ko hakan na nufin an tura jirgin zuwa Greenland ba, amma ya ce ana aiwatar da shirin ne tare da wakilin Amurka na musamman a tsibirin.
Wakiliyar Greenland a majalisar Denmark, Aaja Chemnitz, ta ce duk da matsalolin da ke cikin tsarin lafiya, ya fi dacewa a warware su ta hadin gwiwa da Denmark.
A baya-bayan nan, Greenland ta rattaba hannu kan yarjejeniya da Copenhagen domin inganta yadda ake kula da marasa lafiya ‘yan Greenland a asibitocin Denmark.
Trump ya sha nanata cewa Amurka na bukatar iko da Greenland domin tabbatar da tsaron kasa, lamarin da ya jawo cece-kuce a siyasar duniya.
Kasashen Larabawa sun sura kan jakadan Amurka
Kun ji cewa kasashen Larabawa da Musulmi sun yi martani bayan kalaman jakadan Amurka a Isra'ila game da mamayar ƙasar a yankin.
Larabawan sun yi tir da kalaman jakadan, Mike Huckabee, kan batun fadada ikon Isra’ila a yankin Gabas ta Tsakiya.
Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi (OIC) ta bayyana kalaman a matsayin masu hatsari, tana cewa suna saba dokokin kasa da kasa.
Asali: Legit.ng
