Jami’in DSS Ya Bindige Wani da Ya Yi Kokarin Shiga Gidan Trump da Makami
- Jami’an hukumar DSS sun harbe tare da kashe wani matashi dauke da makami da ya kutsa cikin harabar gidan Mar-a-Lago na Donald Trump
- Hukumar ta ce lamarin ya faru da misalin karfe 1:30 na safe, sai dai a lokacin Trump ba ya wurin, domin yana birnin Washington
- Wani mai suna Ryan Routh ya taba shirya kisan Trump a 2024, yayin da wani matashi Matthew Crooks ya taba harbe shi a Pennsylvania
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Florida, US - Jami’an Hukumar DSS a Amurka sun ce sun harbe tare da kashe wani mutum dauke da makami wanda ya shiga harabar gidan shugaban Amurka, Donald Trump.
Lamarin ya faru ne a yau Lahadi 22 ga watan Fabrairun shekarar 2026 a gidan shugaban kasar da ke Mar-a-Lago a Florida.

Kara karanta wannan
Trump ya durawa alkalai ashar bayan hana shi daukar mataki kan Najeriya da kasashe

Source: Getty Images
DSS ta bindige wani mutum a Florida
An bayyana cewa Trump yana birnin Washington a lokacin da lamarin ya faru, wanda aka ce ya auku da misalin karfe 1:30 na safe agogon yankin, cewar Reuters.
Kakakin hukumar, Anthony Guglielmi, ya ce jami’ai sun dauki matakin ne bayan mutumin ya karya shingen tsaro tare da shiga yankin da aka killace.
Sanarwar ta ce an hangi wanda ake zargin, matashi dan shekaru kimanin ashirin da haihuwa, kusa da kofar arewa dauke da abin da ya yi kama da bindigar farauta da kuma jarkar mai.
Jami’an tsaro sun tunkari mutumin inda daga bisani suka bude wuta a kansa, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa nan take.

Source: Twitter
Wane hali jami'an hukumar DSS ke ciki?
Hukumar ta tabbatar da cewa babu wani jami’in tsaro da ya samu rauni a yayin musayar wutar da aka yi a wajen wanda ya yi ajalin mutumin da ake zargi.

Kara karanta wannan
DSS na shirin gayyatar yaran El Rufa'i, matar Dadiyata ta yi magana kan dauke mijinta
Rahotanni sun nuna cewa Trump ya sha fuskantar yunkurin kashe shi a baya, ciki har da wasu makirce-makirce da aka bankado, cewar CNBC.
A farkon wannan watan, wani mai suna Ryan Routh mai shekaru 59 an yanke masa hukuncin daurin rai da rai bisa shirya harin kashe Donald Trump a 2024.
Harin da Routh ya shirya ya biyo bayan wani yunkurin kisa da wani matashi mai suna Matthew Crooks ya kai masa a Pennsylvania yayin wani gangami.
A wancan harin, daya daga cikin harsasan ya gogi kunnen dama na Trump, sannan jami’an tsaro suka harbe Crooks nan take, yayin da dalilinsa bai fito fili ba.
Trump ya dura wa alkalai ashar
Mun ba ku labarin cewa Shugaba Donald Trump ya kaddamar da sabon harajin kashi 10 bayan kotun kolin Amurka ta yi watsi da harajin shigo da kaya da ya sa wa kasashe.
A martanin da ya yi a wani taro a fadar White House, Trump zagi alkalan kotun ya nuna cewa ba su da jarumtar daukar matakai masu tsauri.
Tun a shekarar 2025 Donald Trump ya kakaba wa Najeriya da wasu kasashen duniya haraji, lamarin da ya tayar da kura a fadin Amurka.
Asali: Legit.ng