Sarakuna Sun Shiga Uku, Gwamna Ya Yi Masu Barazanar Raba da Kujerunsu
- Gwamnan Akwai Ibom, Umo Eno ya yi barazanar kwace takardun sarautar sarakunan gargajiya a fadin jihar game da kayan gwamnati
- Eno ya ce duk basaraken ƙauye da ya kasa kare makarantu ko kayayyakin gwamnati ba shi da amfani a matsayinsa
- Ya umarci jami’ai su kira taron gaggawa da shugabannin ƙauyuka domin sanar da su sabon matakin da aka dauka
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Uyo, Akwa Ibom - Gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ya yi barazana ga wasu sarakunan gargajiya a jihar game da barnata kayan gwamnati.
Gwamnan ya ce zai janye takardun shaidar sarauta na duk wani basaraken ƙauye idan aka samu lalata dukiyar gwamnati a yankinsa.

Source: Facebook
Gwamna ya yi barazana ga sarakunan gargajiya
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin taron addu’ar wata-wata da aka gudanar a Fadar Gwamnati da ke Uyo, inda ya jaddada cewa ba za a lamunci barna ba, cewar Punch.

Kara karanta wannan
Rikicin APC: Majalisa ta fara yunkurin tsige mataimakin gwamna? Aiyedatiwa ya yi bayani
Ya ce duk ƙauyen da gwamnati ta kai ayyuka, amma aka bari ɓata-gari suna lalata kayayyaki, to za a hukunta shugaban ƙauyen ta hanyar kwace takardarsa.
A cewarsa, idan makarantar gwamnati mai kayan aiki na zamani ta lalace cikin sauƙi a ƙauyen mutum, hakan na nuna rashin kulawa daga shugabannin yankin.
Gwamnan ya umarci Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da Harkokin Sarauta, Frank Archibong, da shugaban ALGON na jihar, Dr. Uwemedimo Udo, su kira taro da shugabannin ƙauyuka domin yi musu bayani.
Ya kuma bukaci al’ummar jihar da su kasance masu lura da tsaro tare da kare dukiyar jama’a daga lalacewa.

Source: Facebook
Fasto ya ja hankalin al'ummar Akwa Ibom
Game da shirin samar da kananan ayyukan ruwa a kowace mazaba, Gwamna Eno ya ce kwamitin samar da ayyuka na hadin guiwa ne zai kula da aiwatar da su.
A yayin huduba mai taken “Unsearchable God,” daga littafin Romawa 11:33, Fasto Bolaji Adeisrael ya jaddada cewa hanyoyin Allah abin mamaki ne amma suna alheri ga bayinsa.
Taron addu’ar ya samu halartar mataimakin gwamna, Sanata Akon Eyakenyi, da sauran manyan jami’an gwamnati da shugabannin addini a jihar.
Wannan gargadin da gwamnan ya yi na zuwa ne yayin ake yawan samun lalata wa da sace kayayyakin gwamnati wanda ke jawo asara sosai ga al'umma, cewar TVC News.
Hakan ne ma ya jawo ake shawartar sarakunan gargajiya da masu ruwa da tsaki su sanya ido domin ganin an kare kayan gwamnati a yankunan jihar gaba daya.
Sarki ya mutu ana tsaka da rigimar sarauta
Mun ba ku labarin cewa an shiga jimami bayan sanar da mutuwar babban Sarki da ya shafe shekaru yana gwagwarmaya kan rikici game da kujerarsa da har yau ba ta kare ba.
Al’ummomin Egrangbene a Burutu, jihar Delta, sun sanar da rasuwar zababben Sarki, Henry Ambakederemo Okrikpa, yana da shekaru 70.
An ayyana zaman makoki gaba ɗaya a yankin, yayin da rikicin sarauta ya daɗe tun bayan naɗinsa a 2009, amma gwamnatin Delta ba ta amince da shi ba.
Asali: Legit.ng
