Wata Sabuwa: NNPP Ta Fallasa Makarkashiyar da Gwamnatin Abba Ke Yi Mata a Kano
- Jam'iyyar NNPP mai adawa a Kano ta nuna matukar damuwarta kan wasu abubuwan da ta ce gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir na yi mata
- NNPP ta yi zargin cewa gwamnatin ta taso mambobinta a gaba ciki har da wadanda suka yi aiki a karkashinta a matsayin kwamishinoni da masu ba da shawara
- Jam'iyyar ta tunatar da gwamnatin cewa abubuwan da take yi ba su dace da dimokuradiyya ba, kuma mukaman gwamnati ba na din-din-din ba ne
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Jam’iyyar NNPP reshen Kano ta yi zarge-zarge kan gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
NNPP ta zargi gwamnatin Abba da yi wa mambobinta bita da kulli a abin da ta bayyana a matsayin "farautar siyasa."

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na jam'iyyar NNPP, Engr. Ibrahim Karaye ya fitar a ranar Asabar, 11 ga watan Fabrairun 2026.
Wane zargi NNPP ta yi kan gwamnatin Abba?
NNPP ta yi zargin cewa ayyukan gwamnatin sun saba wa tsarin dimokuradiyya kuma ba su kamata ba.
Jam’iyyar ta yi zargin cewa gwamnatin jihar, wacce ta ce an kafa ta ne a karkashin inuwar NNPP kafin daga bisani ta yi watsi da jam’iyyar, ta fara janye kujerun aikin Hajji da aka riga aka ware wa wasu mambobinta.
Ta ce mambobinta da aka fara janye kujerun da aka ba su sun hada da tsofaffin kwamishinoni, masu ba da shawara, da kuma shugabannin jam’iyyar.
A cewar Ibrahim Karaye, wadanda abin ya shafa, a matsayinsu na ’yan asalin jihar Kano, suna da damar morar irin wadannan abubuwan, rahoton Daily Post ya tababtar da hakan.
Haka zalika, jam’iyyar ta zargi gwamnatin da cin zarafi da kuma tsoratar da tsofaffin masu rike da mukaman siyasa domin su dawo da motocin gwamnati da aka ba su lokacin suna kan aiki, inda ta bayyana motocin a matsayin wani bangare na hakkokinsu da ya kamata su samu a lokacin aiki.

Kara karanta wannan
Gwamnati ta gyara halin tubabbun 'yan ta'adda sama da 100, za su dawo cikin mutane

Source: Facebook
NNPP ta ba da shawara
NNPP ta bukaci gwamnatin jihar da ta daina daukar matakan da ta ce za su iya gurgunta tsarin dimokuradiyya, inda ta kara da cewa ya kamata a gudanar da siyasa cikin girmama juna da kiyaye mutuncin juna.
Daga karshe, ta yi kira ga mahukunta da su girmama hakkin tsarin mulki na ’yancin yin tarayya, tare da gargadin cewa mukaman siyasa ba na din-din-din ba ne.
Gwamna Abba ya yi magana kan zabe
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi magana kan zabubbukan cike gurbi da aka gudanar a jihar.
Gwamna Abba Kabir ya yaba wa hukumar zabe mai zaman kanta a jihar da kuma hukumomin tsaro bisa yadda suka gudanar da shi cikin lumana da tsari.
Hakazalika, Gwamna Abba ya bayyana cewa kwanciyar hankalin da aka samu a rumfunan zabe ya nuna yadda al’umma suka kara fahimtar siyasa da kuma ingancin shirye-shiryen tsaro da aka tanada a zaben.
Asali: Legit.ng
