Hukumar JAMB ta Musanta Tilasta wa Musulmai Cire Hijabi a Wajen Rajistan UTME

Hukumar JAMB ta Musanta Tilasta wa Musulmai Cire Hijabi a Wajen Rajistan UTME

  • Hukumar JAMB ta ce ba ta taba umartar dalibai su cire hijabi yayin rajistan UTME da ake yi a kasar ba
  • Hakan ya biyo bayan bidiyo da ya nuna zargin wariya ga Musulmai a ABUAD, kamar yadda rahotanni suka nuna
  • Hukumar ta bayyana cewa abin da ake bukata kawai shi ne kunnuwa su bayyana a hoton da za a yi amfani da shi

FCT, Abuja - Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta Kasa (JAMB) ta bayyana cewa ba a bukatar dalibai su cire hijabinsu yayin rajista ko daukar hoton fasfo da za a yi amfani da shi a jarabawa.

JAMB ta yi wannan karin haske ne bayan wani bidiyo ya yadu a shafukan sada zumunta, inda aka nuna zargin cewa an nuna wariya ga wata daliba Musulma a Jami’ar Afe Babalola (ABUAD).

Martanin JAMB kan zargin tilastawa mata cire hijabi
Hotuna daban-daban na rajistan JAMB, har da na masu bukata ta musamman | @JAMBHQ
Source: Twitter

Idan ba ku manta ba, akan samu yanayin da ke da alaka da nuna wariyar addini a cibiyoyin jarrabawa na JAMB a shekarun baya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya za ta soke amfani da Naira daga shekarar 2027? Gaskiya ta fito

Bidiyon da ya jawo cece-kuce

A cikin bidiyon da wani mai amfani da kafar sada zumunta mai suna AsakyGRN ya wallafa, wani mutum ya koka cewa an tilasta wa ‘yar uwarsa cire hijabi kafin a dauki hotonta domin rajistar jarabawar JAMB.

A cewar mutumin:

“Na raka ‘yar uwata cibiyar JAMB domin ta karbi fom. An ce mata sai ta cire hijabi kafin a dauki hotonta.”

Ya kara da cewa bayan an dauki hoton, an nemi ta sanya hannu a wata takarda da ta shafi sanya hijabi, yana tambayar ko dai yanzu ana nuna wariya ga Musulmai ne saboda sanya hijabi.

JAMB ta yi bayani

A wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar a shafinta na X, JAMB ta ce ba ta taba fitar da wata doka da ta haramta wa dalibai sanya hijabi ba.

Hukumar ta bayyana cewa a duk duniya, a yayin daukar hoton bayanan halitta (biometric) domin fasfo na kasa da kasa ko neman biza, dole ne kunnuwa su bayyana.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fusata kan kashe kashe a taron APC, ya dauki kwakkwaran mataki

A cewar sanarwar:

“Wannan bukata ta fasaha ce kawai domin tabbatar da sahihin gane fuska da kuma tantance mutum, ba wai domin tilasta cire hijabi ba.”

Abin da ya faru a ABUAD

Da take karin haske kan lamarin ABUAD, JAMB ta ce an mutunta matsayar addinin dalibar yadda ya kamata.

Ta ce an nemi ta rubuta da kanta cewa ta zabi kada ta bi ka’idar bayyana kunne yayin daukar hoto, domin a samu cikakken bayani a takardu kuma a guji bata suna ko fahimtar da ba ta dace ba a nan gaba.

Sanarwar ta kara da cewa:

“Ta amince, kuma daga bisani an dauki hotonta cikin nasara, duk da cewa hakan ya dauki lokaci da kokari.”

JAMB ta jaddada cewa ba a bukatar dalibai su cire hijabi. Abin da ake bukata kawai shi ne kunnuwa bayyana yayin daukar hoto, wanda za a iya yi ba tare da cire hijabi gaba daya ba.

Kara karanta wannan

DSS na shirin gayyatar yaran El Rufa'i, matar Dadiyata ta yi magana kan dauke mijinta

Kiraye-kirayen JAMB ga jama'a

Ta kara da cewa wannan tsari na daukar bayanan halitta abu ne na yau da kullum kamar yadda ake yi a ofisoshin jakadanci yayin neman fasfo ko biza a sassa daban-daban na duniya.

Hukumar ta bukaci jama’a su guji yada bayanan da ba su da tushe, tare da neman karin haske daga hukumomi idan aka samu shakku.

Haka kuma ta sake jaddada kudirinta na mutunta hakkoki da akidun dukkan dalibai ba tare da la’akari da addini ko asali ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng