Musulmi na tsaka da Azumi, An Nada Sabon Limami a Masallacin Annabi Muhammad S A.W

Musulmi na tsaka da Azumi, An Nada Sabon Limami a Masallacin Annabi Muhammad S A.W

  • Saudiyya ta nada Sheikh Saleh Al-Maghamsi a matsayin limami a masallacin Annabi Muhammad S.A.W da ke birnin Madinah
  • Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da hukumar kula masallatai biyu masu alfarma ta fitar yau Asabar, 21 ga watan Fabrairu, 2026
  • Sheikh Saleh Al-Maghamsi, ya fito ya nuna godiya ga Allah da kuma shugabannin Saudiyya bisa amincewar da aka yi masa tare da ba shi amana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Saudi Rabia - Masarautar Saudiyya ta sanar da nadin limamin masallacin Annabi Muhammad (Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi) da ke birnin Madinah.

Masallacin Annabi S.A.W (Al-Masjid an-Nabawi) da ke Madinah Al-Munawwarah na daya daga cikin masallatai uku mafiya daraja a addinin musulunci.

Sheikh Saleh Al-Maghamsi.
Sabon limamin masallacin Annabi S.A.W da ke Madinah, Sheikh Saleh Al-Maghamsi Hoto: @Insharifain
Source: Twitter

Hukumar kula da masallatai biyu masu alfarma a Saudiyya ta tabbatar da nadin limamin masallacin Annabi a wata gajeruwar sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, Inside The Haramain.

Kara karanta wannan

Gwamna ya dauko fitacciyar jarumar fina finai, ya ba ta babban mukami

An nada limamin masallacin Annabi S.A W

A sanarwar wacce ta fitar yau Asabar, 21 ga watan Fabrairu, 2025, ta ce masarautar Saudiyya ta amince da nadin Sheikh Saleh Al-Maghamsi a matsayin sabon limamim masallacin Annabi.

Sheikh Al-Maghamsi sananne ne a matsayin malamin addini kuma mai wa’azi wanda ya shahara wajen tafsiri da karantarwa a ƙasar Saudiyya.

Naɗin nasa a matsayin limami a Masallacin Annabi (SAW) ana kallonsa a matsayin babbar karramawa da kuma amincewa da ilimi da ƙwarewarsa a fagen addinin musulunci.

A sanarwar, masarautar Saudiyya ta bayyana cewa:

"An fitar da wata sanarwar doka wadda ta tabbatar da naɗa Sheikh Saleh bin Awad Al-Maghamsi a matsayin limamin Masallacin Annabi (SAW)."

Sheikh Saleh ya yi wa Allah SWT godiya

Sabon limamin na Al-Masjid an-Nabawi, Sheikh Saleh Al-Maghamsi, ya fitar da sanarwa inda ya nuna godiya ga Allah da kuma shugabannin Saudiyya bisa amincewar da aka yi masa.

A cikin sanarwar, Sheikh Al-Maghamsi ya ce:

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba Aminu Ado Bayero jagorancin ciyar da talakawa a Ramadan

“Dukkan yabo ya tabbata ga Allah wanda da ni’imominsa ne ake cika ayyukan alheri.
"Allah Ya saka wa Mai Kula da Masallatai Biyu Masu Tsarki, Sarki Salman bin Abdulaziz, da kuma Yarima mai daraja, Mohammed bin Salman, Yariman Mai Jiran Gado bisa wannan amana mai daraja da suka dora min ta naɗa ni a matsayin Imam a Masallacin Annabi.
"Kuma muna roƙon Allah Maɗaukaki Ya ba mu dacewa a cikin abin da Yake so kuma Yake yarda da shi.”
Masallacin Annabi SAW.
Masallacin Annabi Muhammad SAW da ke birnin Madinah a kasar Saudiyya Hoto: Inside The Haramain
Source: Facebook

Ladanin Masallacin Annabi SAW ya rasu

A wani rahoton, kun ji cewa daya daga cikin masu kiran sallah a Masallacin Annabi SAW, Sheikh Faisal Nouman, ya riga mu gidan gaskiya.

Sheikh Faisal Nouman ya samu mukamin mai kiran sallah a masallacin Madina a shekarar 1422AH, daidai da 2001, inda ya shiga cikin jerin bayin Allah da aka amince da su.

Rahotanni sun nuna cewa malamin ya fito ne daga gidan da suka gaji kiran sallah, inda kakansa da mahaifinsa suka taba rike wannan matsayi mai daraja

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262