Gwamnatin Najeriya Za Ta Soke Amfani da Naira daga Shekarar 2027? Gaskiya Ta Fito

Gwamnatin Najeriya Za Ta Soke Amfani da Naira daga Shekarar 2027? Gaskiya Ta Fito

  • An gudanar da binciken kwa-kwaf game da rade-radin cewa za a bar amfani da Naira a Najeriya daga shekarar 2027 da ke tafe
  • Bidiyo ya bazu a kafofin sadarwa yana kirarin cewa Najeriya za ta soke Naira a 2027 tare da maye gurbinta da kudin bai daya
  • Fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa kasashen ECOWAS na tattaunawa kan Eco, amma aiwatarwa na karkashin sharuddan tattalin arziki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - An yi ta yada wani bidiyo da ya bazu a kafofin sadarwa da ke ikirarin cewa Najeriya za ta soke kudin Naira.

Rahotannin sun bayyana cewa za a bar amfani da Naira ne shekarar 2027 tare da rungumar sabon kudin bai daya mai suna Eco.

An gano gaskiya kan rahoton cewa za a soke amfani da Naira a Najeriya
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, CBN. Yemi Cardoso. Hoto: Central Bank of Nigeria.
Source: Twitter

Rahoton TheCable ya ce an yi bincike inda ya tabbatar da cewa babu kamshin gaskiya game da rahoton da ake yada wa a Najeriya.

Kara karanta wannan

Manya sun fara nuna damuwa da jibge sojojin Amurka da aka soma a Najeriya

Yadda aka yada maganar soke Naira

Wacce ta yada bidiyon, mai suna “Flora the Digital Banker”, ta ce daga 2027 ba za a kara amfani da Naira ba saboda kasashen yammacin Afirka za su koma Eco.

Ta ce Najeriya da wasu kasashe 11 ciki har da Ghana, Senegal da Saliyo za su fara amfani da kudin guda daya kamar yadda Tarayyar Turai ke amfani da Euro.

Sai dai a ranar 14 ga Fabrairu 2026, fadar shugaban kasa ta bayyana cewa gwamnonin manyan bankunan kasashen ECOWAS na ci gaba da tattaunawa kan tsarin Eco.

Sanarwar ta ce kudin Eco na nan a matakin shiri kuma aiwatar da shi zai dogara ne da cika ka’idojin hadewar tattalin arziki da aka gindaya.

Babu gaskiya kan soke amfani da Naira zuwa Eco a 2027
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Abin da fadar shugaban kasa ta ce

Fadar shugaban kasar ta kara da cewa matakin farko zai shafi Najeriya, Ghana, Liberia, Saliyo, Guinea da Gambiya idan sun cika sharuddan da aka amince da su, kamar yadda ta wallafa a shafin X.

Kara karanta wannan

'Yana neman ruguza kasa': Gwamnati ta haramta amfani da dukan kafofin sadarwa

Wannan yana nufin cewa aiwatar da kudin ba lallai ba ne ya zama tilas ga kowa a lokaci guda, domin ya dogara da yanayin tattalin arziki.

Babu wata sanarwa daga fadar shugaban kasa, Babban Bankin Najeriya ko ECOWAS da ta ce za a soke Naira a 2027.

An dade ana tattaunawa kan kudin Eco tsawon shekaru, amma an sha dage kaddamar da shi saboda rashin cika sharuddan tattalin arziki.

A watan Agustan 2025, ECOWAS ta sanar da shirin kaddamar da Eco a ranar 1 ga Yuli, 2027, amma ba tare da soke kudaden kasashen kai tsaye ba.

Haka kuma taron ECOWAS na Disamba 2025 ya sake jaddada burin 2027, amma bai bayyana cewa za a maye gurbin kudaden kasashe nan take ba.

Saboda haka, babu wata hujja da ke nuna cewa Najeriya za ta soke Naira a 2027 domin rungumar kudin Eco kai tsaye kamar yadda aka yada.

Matsayar Tinubu kan cire tallafi, manufofin tattali

A baya, kun ji cewa Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa babu gudu, babu ja da baya a kan sauye-sauyen tattalin arzikin Najeriya.

Kara karanta wannan

An yi zanga zangar korar 'yan Arewa a Rivers, an fasa shaguna da lalata dukiya

Tinubu ya nemi Bankin Duniya da ya hanzarta tallafa wa ƙasar nan da sababbin hanyoyin kuɗi domin bunƙasa tattalin arziki.

Bankin Duniya ya ce Najeriya ta zama abin koyi a duniya kan aiwatar da gyare-gyaren tattalin arziki duk da wasu na kuka a gida.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.