‘Dalilin Yi wa Jam’iyyar PDP Al Kunut a Shekarun Baya’: Sheikh Isa Pantami
- Farfesa Isa Ali Pantami ya yi magana game da shigar mutanen kirki cikin siyasa tsundum yana mai cewa burmawarsa na da dalilai masu karfi
- Pantami ya bayyana cewa kalubalantar shigarsa siyasa na nuna tasirin da yake da shi, yana cewa tsoron wannan tasiri ne ke sa wasu su nuna adawa
- Tsohon ministan ya kare kansa kan batun Al-Kunut da ya yi a da, yana cewa martaninsa ya samo asali ne daga furucin wani babban jami’in gwamnati
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon ministan sadarwa a Najeriya, Sheikh Isa Ali Pantami ya yi karin haske game dalilinsa na shiga siyasa da ake ta maganganu.
Farfesa Isa Ali Pantami ya bayyana cewa yana da kyau mutanen kirki da ake yi wa tsammanin alheri su shiga siyasa ba su yi kyamar ta ba.

Kara karanta wannan
"APC ba jam'iyyar waliyyai ba ce"; Ministan Tinubu ya yi fallasa kan jam'iyya mai mulki

Source: Facebook
'Dalilin tsoron shiga ta siyasa': Sheikh Isa Pantami
Tsohon ministan ya bayyana haka yayin hira da BBC Hausa wanda ta wallafa bidiyo a shafin Facebook a yau Asabar 21 ga watan Fabrairun 2026.
Shehin malamin ya nuna damuwa kan yadda ake ta magana bayan shigar shi siyasa inda ya ce an san tasirinsa ne shiyasa ake shakku.
Ya ce:
"Duk inda ka ga wani ya kalubalanci shigan wani, to wannan wanda ya shiga din matsala ne ga mai gidan wancan da ke magana.
"Shi ne damuwarsa, idan da ba matsala ba ce babu ruwansa, sannan na biyu ai ba yau masu addini suka fara yi ba, a Kano an yi babban Shehi ya tsaya takara ba daya ba biyu ba.
"A Niger an yi babban Shehi ya tsaya takara, amma me yasa na mu ya tsole ido saboda tasirin shigar ake tsoro, hakan kuma kara mana karfin mu shiga yake yi."

Source: Facebook
Pantami ya magantu kan yi wa PDP Al-kunut
Game da maganar Al-Kunut da ya yi wa PDP, Malam ya ce ransa ne ya baci a lokacin saboda hadimin shugaban kasa da kansa ya ce suna da hannu a rashin tsaro.
Farfesa Pantami ya ce babu yadda za a yi yana dan Arewa da ake kashe-kashe kuma na kusa da Shugaban kasa ya fito ya bayyana haka a ce ba zai yi martani ba.
Ya ce ko mai rike da mukamin a yanzu ne wani ya fito ya ce suna da hannu a rashin tsaro ne zai fito ya kausasa harshe game da lamarin.
Ya kara da cewa:
"Abin da ya sa na fara yin a lokacin,ba a 2014 ba ne a 2011 ne na yi maganar, a lokacin hadimin shugaban kasa kan tsaro, marigayi Andrew Azazi ya fito ya kira jam'iyyarsu ya ce da hannunsu ake kashe-kashe.

Kara karanta wannan
Kurunkus: Pantami ya wanke kansa kan batun haramta wa malamai shiga siyasa a baya
"Ni dan Arewa ne a yankinmu ake kashe-kashe ta yaya zai fadi haka a ce rai na ba zai baci ba, yau idan mai ba shugaban kasa shawara a yanzu, amini na ne, ya fito ya ce su suke yi, kana ganin zan bar su ne."
Sheikh Pantami ya magantu kan rawa a siyasa
Kun ji cewa Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya yi karin haske kan dalilin da ya sa yake shiga harkokin siyasa bayan ce-ce-ku-ce da ake yi.
Tsohon ministan ya musanta zargin cewa zai yi rawa a siyasa, yana cewa ko a lokacin da yake rike da kujerar minista bai taba aikata hakan ba.
Pantami ya ce zai iya yin duk wani abu domin maslahar al’umma, har ma ya ce idan hakan zai ceci rayuka, zai iya rawa ko ba don mulki ba.
Asali: Legit.ng
