Kwanaki 3 da Shiga Watan Ramadan, Mutane Sun Fara Fuskantar Matsala a Jihar Kano

Kwanaki 3 da Shiga Watan Ramadan, Mutane Sun Fara Fuskantar Matsala a Jihar Kano

  • Mutane sun fara shiga matsalar karancin kwai a sassan jihar Kano kwanaki uku kacal da fara azumin watan Ramadan
  • Bayanai sun nuna cewa matsalar ta samo asali ne daga yadda masu kiwon kaji suka fara rage ayyyukansu saboda matsin tattalin arziki
  • Wani dillalin kwai a Kano, Ibrahim Idris ya ce a duk shekara, ana samun karin bukatar kwai a watan azumi da kashi 50 cikin 100

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Kwanaki uku da fara azumin Ramadan, al'adar nan ta zumunci da aka saba gani a Kano, watau shirya buda baki ta fara fuskantar ƙalubale sakamakon ƙarancin ƙwai a kasuwanni.

Kano, na daga cikin biranen da ake ganin ƙwai na taka muhimmiyar rawa wajen shirya buda-baki (Iftar), wanda mutane ke taruwa idan an sha ruwa su ci abinci tare.

Kara karanta wannan

Ramadan: Gwamna ya amince da ciyar da talakawa, ya yi wa malaman addini tagomashi

Kwai.
Tulin kwai a wani gidan kaji a jihar Kano Hoto: Binta Abdullahi Idrees
Source: Facebook

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa kwai, wanda ya kasance hanya mafi sauki wajen samun sinadarin furotin ga talakawa, yanzu ya zama abu mai wahalar samu.

Abin da ya jawo karancin kwai a Kano

Rahotanni sun nuna cewa farashin ƙwai ya tashi matuƙa, har ya kai ga iyalai da dama ba za su iya saya ba a wannan lokaci mai albarka.

Matsalar ta samo asali ne daga matsin tattalin arziki da ya durƙusar da harkar kiwon kaji tun kafin a ga jinjirin watan Ramadan.

Ibrahim Idris, babban dillalin ƙwai a unguwar Tudun Yola, ya bayyana cewa tsadar kiwon kaji ce babbar matsalar ta kawo karancin kwai a halin yanzu.

A cewarsa, a duk lokacin Ramadan ana samun ƙaruwar buƙatar kwai da kusan kashi 50 cikin 100, amma a wannan shekarar ana samar da ƙwai ƙasa da da yadda aka saba da kashi 40.

Kara karanta wannan

Kano: Dalilin da ya sa za a dauke wuta a wasu yankuna a watan azumin Ramadan

Masu kiwon kaji sun ragu a Kano

Ya ce manoma da dama sun rufe gonakinsu saboda tsadar abincin kaji da sauran kuɗaɗen kula da su, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

Ya ƙara da cewa a yankuna kamar Kumbotso, Gezawa da Rimin Gado, mutane sun rage yawan kajinsu tun kafin Ramadan, domin ba su iya ɗaukar nauyin ciyar da su.

“Idan yawan kwan da ake samarwa ya ragu tun daga tushe, mu dillalai ba mu da abin da za mu kawo birni,” in ji shi.

Kwai ya fara karanci a kasuwanni

A kasuwanni da shagunan abinci a Fagge da Kabuga, ana ganin tasirin matsalar a fili a watan na azumi.

Sadiq Ibrahim, mai shagon sayar da kayan masarufi a Tudun Yola, ya ce farashin kiras na kwai ya tashi daga N5,500 zuwa N6,500, duk da haka babu kaya.

Ya ce mutane na tambayar ƙwai a kowane lokaci, amma amsar ita ce babu. “Har na kasa gaya musu inda za su samu,” in ji shi.

Kara karanta wannan

Mummunar gobara ta sake sake tashi rigi rigi a wata babbar kasuwa a Kano

Jihar Kaduna.
Taswirar jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Rahotanni sun nuna cewa hanyoyin samar da ƙwai daga Jos a Jihar Plateau da kuma Jihar Ogun, waɗanda ke tallafa wa samarwar cikin gida, su ma sun kasa biyan buƙatar Kano.

NOA ta gargadi 'yan kasuwa saboda azumi

A wani labarin, kun ji cewa hukumar NOA ta bayyana cewa boye kayan abinci da kara farashi ba bisa ka'ida ba na iya jefa mutane a wata sabuwar tsadar rayuwa a watan azumi.

Hukumar NOA ta samu rahotanni cewa wasu ’yan kasuwa na ɓoye muhimman kayayyakin abinci da ake yawan amfani da su a lokacin azumi.

Shugaban NOA ya ce ɓoye kaya da gangan na rushe ƙoƙarin da ake yi na daidaita tattalin arziki, yana ƙara hauhawar farashi tare da tsananta wahalar da mutane ke fuskanta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262