Ramadan: Gwamna Ya Amince da Ciyar da Talakawa, Ya Yi Wa Malaman Addini Tagomashi
- Gwamnatin jihar Yobe karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni ta fadada shirin ciyarwa na lokacin azumin wata Ramadan
- An kara yawan wuraren da ake ba da abincin buda baki ga mutanen da suka yi azumi a wannan wata mai alfarma a fadin jihar Yobe
- Hakazalika, Gwamna Buni ya amince da ware kudaden da za a rika biyan alawus-alawus ga malamai masu gudanar da Tafsiri
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Yobe - Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da fitar da kuɗi sama da Naira miliyan 398 domin shirin ciyarwa na watan Ramadan na shekarar 2026 da kuma gudanar da Tafsirai a faɗin jihar.
Wannan shiri, wanda ma’aikatar al'amuran addini ta jihar Yobe za ta aiwatar, yana da nufin tallafa wa gajiyayyu da marasa ƙarfi a cikin wannan wata mai alfarma.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta ce a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin faɗaɗa shirin, gwamnan ya ƙara yawan wuraren ciyarwa daga 101 da suke a bara zuwa wurare 130 a faɗin kananan hukumomi 17 na jihar.
Yadda tsarin ciyarwar Ramadan yake
Kowane wurin ciyarwa zai riƙa bayar da abincin buɗa baki ga mutane 100 kowace rana a duk tsawon watan Ramadan.
An ware Naira miliyan 338 domin sayan raguna da kayan miya waɗanda za a yi amfani da su wajen dafa abinci a cibiyoyi 130 da aka ware a faɗin jihar.
Hakazalika an ware Naira Miliyan 60 domin biyan alawus-alawus ga malaman addinin Musulunci waɗanda za su gudanar da karatun Tafsirin Alkur'ani mai girma a duk tsawon watan na Ramadan.
Gwamnan ya kuma amince da raba buhunan shinkafa 2,300 da jarkokin man girki 400 ga waɗannan wurare 130 domin tabbatar da an gudanar da aikin ba tare da tangarda ba.
Gwamna Mala Buni ya samu yabo
Da yake jawabi ranar Juma’a yayin kaddamar da raba kayayyakin a birnin Damaturu, kwamishinan al'amuran addini, Yusuf Umar, ya yaba wa gwamnan bisa dorewa da kuma faɗaɗa wannan shiri.
“Wannan karramawa na nuna halin Gwamna Mai Mala Buni wajen jin kan talakawa, musamman a lokacin Ramadan. Faɗaɗa wuraren ciyarwar zai ba wa mutane da dama damar amfana."
- Yusuf Umar

Source: Facebook
An ja kunne kan karkatar da kayayyakin azumi
Kwamishinan ya yi gargaɗi ga kwamitocin da ke kula da wuraren ciyarwar da su kiyaye amanar kayayyakin da aka ba su.
“Ba za mu yarda da karkatar da kaya ko rashin kulawa ba. Dole ne dukkan jami’an da ke da hannu su tabbatar da gaskiya da riƙon amana wajen gudanar da ayyukansu.”
- Yusuf Umar
Ya kara da cewa shirin ciyarwa da Tafsirin ya zama wani babban ginshiƙin tallafi ga iyalai da dama a faɗin jihar, kuma za a tabbatar an bi ka’idodin gwamnati yadda ya kamata.
Gwamna Abba ya rage lokacin aiki saboda azumi
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya saukaka ma'aikatan gwamnati saboda azumin watan Ramadan.
Gwamna Abba ya amince da rage lokacin da ma'aikata za rika tashi daga wuraren ayyukansu a ranakun da ake gudanar da aiki.
A cikin sabon tsarin da Gwamna Abba ya kawo, ma'aikatan gwamnati sun samu ragin sa'a guda a lokacin tashi daga aiki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


