Kotu za Ta Rataye Malamin Addini bayan Kashe Dalibi da Wuka
- Kotun jihar Akwa Ibom ta samu wani malamin addinin Kirista da hannu dumu-dumi a kashe wani dalibin jami'a da ke kusa da shi
- Rahotanni sun bayyana cewa a ranar 21 ga Disamba, 2020 faston ya cakawa dalibin wuka wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa
- Bayan shafe shekara kusan shida ana shari'a, kotu ta yankewa faston hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda samunsa da laifi
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Akwa Ibom - An yanke wa faston cocin Living Faith Church Chapel, reshen Ifa Ikot Ubo–Ifa Ikot Okpon a Uyo, Jihar Akwa Ibom, Emmanuel Umoh, hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Mai shari’a Gabriel Ette na Babbar Kotun Jihar ne ya yanke masa hukuncin bayan samunsa da laifin kashe ɗalibi a Jami’ar Uyo, Gabriel Bassey.

Source: Getty Images
Punch ta wallafa cewa an samu faston da laifin caka wa Edward wuƙa har lahira a ranar 21 ga Disamba, 2020, a Ifa Ikot Ubo cikin Ƙaramar Hukumar Uyo ta jihar.
Bayanin shaidu a kotu
Shaidu sun nuna cewa a ranar 21 ga Disamba, 2020, an ga wanda ake tuhuma ya shiga harabar gidan marigayin, bayan haka maƙwabta suka fara jin ihu ana kiran “Yesu” daga cikin gidan.
Tribune ta rahoto cewa jim kaɗan bayan haka, wanda ake tuhuma ya fito sanye da farar riga mai tabon jini, yana cewa ya faɗi ne yayin da yake ƙoƙarin ɗaura tuta.
Yadda aka samu gawar Edward
A ranar 26 ga Disamba, 2020, kwana guda bayan Kirsimeti, an gano gawar Edward a cikin ɗakinsa ta fara ruɓewa, an naɗe ta cikin tabarma, tana da raunuka da dama, kuma an samu wuƙa a gefensa.
Saboda faston ne mutum na ƙarshe da aka gani tare da Edward kuma an ga tabon jini a rigarsa, an kama shi tare da gurfanar da shi kan zarginsa da laifin kisa a ranar 6 ga Disamba, 2021.

Kara karanta wannan
DSS na shirin gayyatar yaran El Rufa'i, matar Dadiyata ta yi magana kan dauke mijinta

Source: Original
Domin tabbatar da tuhumar, masu gabatar da ƙara sun kawo shaidu shida, ciki har da mahaifin marigayin, Emana Bassey, wanda ya zama shaida na farko.
Za a rataye malamin addini
Mai shari’a Ette ya yi Allah-wadai da lamarin, yana nuna baƙin ciki kan yadda jagoran addini zai nuna rashin imani ya kashe rai har lahira.
Ya ce:
“Rai abu ne mai tsarki. Abin takaici ne matuƙa da ban mamaki yadda mutumin da ke ikirarin wakiltar Ubangiji a duniya zai kaskantar da kansa har ya tauye ainihin manufar aikinsa ta hanyar kashe rai."
“Bayan na same ka da laifi kamar yadda aka tuhume ka, na yanke maka hukuncin kisa ta hanyar rataya,”
Malamin addini ya yi wa Tinubu raddi
A wani labarin, mun kawo muku cewa malamin addinin Musulunci a jihar Kano, Sheikh Bashir Aliyu Umar ya yi wa Bola Tinubu Raddi.
Malamin ya yi martani ne kan rokon da shugaban kasa ya yi da cewa idan ya yi wa jama'a laifi su yafe masa yayin bude tafsiri a fadar Aso Villa.
Sai dai Sheikh Bashir Aliyu Umar ya ce kamata ya yi shugabanni su mayar da hankali wajen sauke nauyin da ke kansu ba wai neman a musu afuwa ba.
Asali: Legit.ng
