Wata Sabuwa: Kwankwasiyya Ta Dura kan Tinubu bayan Sanya Hannu a Dokar Zabe

Wata Sabuwa: Kwankwasiyya Ta Dura kan Tinubu bayan Sanya Hannu a Dokar Zabe

  • Kungiyar Kwankwasiyya ta soki sahalewar gaggawa da Shugaba Tinubu ya yi wa gyaran Dokar Zabe da suka kira mai cike da ce-ce-ku-ce
  • Kungiyar ta ce karfin APC a majalisa da yawaitar sauya sheka na barazana ga daidaito da tsarin dimokuradiyya
  • Ta gargadi ‘yan siyasa su tuna amanar masu zabe, tare da kira ga jama’a su tsaya tsayin daka wajen kare dimokuradiyya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Kungiyar Kwankwasiyya ta yi martani bayan Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu a dokar zabe da aka gabatar masa.

Kungiyar Kwankwasiyya ta nuna damuwa kan abin da ta kira “sahalewar gaggawa” da Bola Ahmed Tinubu ya yi wa gyaran Dokar Zabe mai cike da ce-ce-ku-ce.

Kwankwasiyya ta soki Tinubu kan dokar zabe
Jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso da Bola Tinubu. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Hakan na cikin sanarwar da kakakin kungiyar, Dakta Habibu Sale Mohammed ya sanya wa hannu wanda The Guardian ta gano.

Kara karanta wannan

DSS na shirin gayyatar yaran El Rufa'i, matar Dadiyata ta yi magana kan dauke mijinta

Zarge-zarge kan gaggawar sanya hannu a dokar zabe

Tafiyar Kwankwasiyya ta ce duk da zanga-korafin jama’a da kiraye-kirayen kungiyoyin fararen hula, sahalewar shugaban kasa ta janyo tambayoyi kan makomar dimokuradiyya.

Ta bayyana cewa karfin da APC ke da shi a bangaren zartarwa da majalisar dokoki ya karu sakamakon sauya shekar wasu zababbun ‘yan adawa.

A cewar yan Kwankwasiyya, sauya shekar ba wai na siyasa kawai ba ne, illa yana haifar da tambayoyi kan gaskiya da bin ka’ida, domin kuri’ar da aka ba su ta jama’a ce, ba ta mutum ba.

Ta kara da cewa tsarin dimokuradiyya ya ginu ne kan daidaito da juna da kuma tsayuwar bangarorin adawa, amma idan aka raunana adawa, to ana rage karfin bincike da sa ido kan ayyukan gwamnati.

Tinubu ya sha suka kan sanya hannu a dokar zabe
Shugaba Bola Tinubu a ofishinsa yana sanya hannu kan wasu takardu. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Dokar zabe: Fargabar da Kwankwasiyya ta nuna

Kungiyar ta ce ce-ce-ku-cen da suka dabaibaye gyaran Dokar Zabe misali ne, inda duk da adawar jama’a da rubuce-rubucen masana, jam’iyya mai mulki ta samu abin da take so a majalisa.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Izala ta dakatar da tafsiri, ta kira taron gaggawa a Kaduna

Ta ce:

“Ce-ce-ku-cen da suka dabaibaye gyaran Dokar Zabe misali ne karara. Duk da korafi da aka yi a fadin kasa, matsaya daga kungiyoyin fararen hula masu kima, da kuma tattaunawar jama’a kan bukatar karin tabbacin gaskiya da rikon amana, jam’iyya mai mulki a karshe ta samu sakamakon dokar da take so.”

Kwankwasiyya ta gargadi cewa dimokuradiyya ba ta rushewa kwatsam, sai dai tana lalacewa sannu a hankali ta hanyar karfafa jam’iyya daya da rage tasirin muryar jama’a.

Ta kuma bukaci zababbun ‘yan siyasa su tuna cewa biyayyarsu ta farko ita ce ga al’ummar Najeriya, tare da kira ga jama’a su ci gaba da sa ido da kare cibiyoyin dimokuradiyya, cewar Daily Post.

Kwankwasiyya ta aika sako ga Amurka kan Kwankwaso

A wani labarin Kwankwasiyya ta aika sako Amurka bayan sanya sunan Rabiu Kwankwaso a jerin wadanda kasar ke zargi da hannu a tauye hakkin addini a Najeriya.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Shugaba Tinubu ya rattaba hannu kan sabuwar dokar zabe

Tafiyar Kwankwasiyya ta bayyana cewa ba a jihar Kano kadai aka kaddamar da shari'a ba, don haka ware mutum daya ba adalci ba ne.

Ta bukaci majalisar dokokin Amurka ta gaggauta cire sunan Kwankwaso daga cikin kudirinta domin hakan na iya yi masa illa a siyasance.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.