Tinubu Ya ba Aminu Ado Bayero Jagorancin Ciyar da Talakawa a Ramadan

Tinubu Ya ba Aminu Ado Bayero Jagorancin Ciyar da Talakawa a Ramadan

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada mai martaba Alhaji Aminu Ado Bayero shugaban kwamitin ciyar da abinci a Ramadan
  • Rahotanni sun nuna cewa kwamitin ya hada da manyan malamai, jami'an gwamnati da 'yan siyasa, kuma an bayyana aikin da za su yi
  • Mambobin kwamitin sun ziyarci gidan Sarkin domin tattauna hanyoyin da za su bi wajen samun nasarar sauke nauyin da aka daura musu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, a matsayin shugaban kwamitin ciyar da jama’a a Ramadan na Ƙasa.

An bayyana naɗin a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Sarkin, Abubakar Balarabe Kofar Na’isa, ya fitar a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Duniya labari: Sanata a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya, ana ta rasa 'yan majalisa

Aminu Ado Bayero da 'yan kwamitin ciyarwa a Ramadan
'Yan kwamitin ciyar da abinci a Ramadan tare da Aminu Ado Bayero. Hoto: @SisinaAbdullah5
Source: Twitter

Masarautar Kano ta sanya wani sako da Abdullahi Sisina ya wallafa a X a shafinta, inda 'yan kwamitin suka ziyarcin Sarkin a fadarsa da ke Gidan Nasarawa, Kano.

'Yan kwamitin Aminu Ado Bayero

Tawagar da ta ziyarci Aminu Ado Bayero ta haɗa da babban limamin masallacin kasa na Abuja, Farfesa Muhammad Kabir, tare da jami’ai daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya, ciki har da babban sakataren ma’aikatar. Muhammad Adamu,

Sauran sun hada da mataimakin darakta na harkokin kayayyaki Alhaji Yahaya Abdulhadi, Malam Muktar Sarki, da Alhaji Alhassan Ibrahim.

A cewar sanarwar, an zaɓi Sarkin ne bisa cancanta da ƙwarewarsa wajen jagoranci mai inganci, inda aka jaddada cewa kwamitin na gwamnatin tarayya ne domin tallafa wa jama’a a watan Ramadan mai alfarma.

Aikin da Aminu Ado zai yi a Ramadan

Guarantee Radio ya wallafa a Facebook cewa Kwamitin zai kula da rabon muhimman kayan abinci kamar shinkafa, gero da man girki ga waɗanda suka cancanta a faɗin ƙasa.

Kara karanta wannan

Jihohin da suka rage lokacin tashi daga ofis alfarmar watan Ramadan a Najeriya

Sanarwar ta nuna cewa a shekarun baya, shirin ya fi mayar da hankali ne kan gayyatar wasu shugabanni domin buda-baki tare da shugaban kasa.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa sabon tsari ya faɗaɗa shirin domin ya haɗa da rabon abinci a dukkan shiyyoyi shida da ke fadin Najeriya.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya na yi wa jama'a bayanai. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Sauran 'yan kwamitin Aminu Ado

Kwamitin ya ƙunshi wakilan gwamnatin tarayya tare da haɗin gwiwar shugabancin masallacin kasa na Abuja da kuma mambobin Majalisar dokoki.

Cikin 'yan kwamitin har da Sanata AbdulRahman Kawu Sumaila da Hon. AbdulSamad Sambo Dasuki, tare da manyan sakatarori uku da daraktoci huɗu.

Jawabin sarki Aminu Ado Bayero

A nasa jawabin, Sarkin ya yaba wa gwamnatin tarayya bisa faɗaɗa shirin ciyarwar Ramadan, yana mai cewa wannan mataki ya zo a kan lokaci.

Ya nuna godiyarsa bisa damar da aka ba shi ta yin hidima ga jama'a, tare da bayyana fatan cewa za a ci gaba da shirin domin samar da sauƙi ga ’yan Najeriya.

Kiran Sheikh Bashir ga Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa Sheikh Bashir Aliyu Umar ya yi martani kan kalaman shugaban kasa Bola Tinubu kan neman a masa afuwa.

Kara karanta wannan

Babban albishirin Dangote ga 'yan Najeriya kan farashin Naira a 2026

Malamin ya bayyana cewa babban aikin da ya kamata shugabanni su mayar da hankali a kai shi ne sauke hakkin da ya ke kansu ba neman gafara ba.

Ya kuma yi tsokaci kan yadda ake yawan kira ga al'umma da malamai su rika yi wa shugabanni addu'ar samun nasarar gudanar da mulki lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng