Tsugunne ba Ta Kare ba; El Rufai Na Tsare hannun ICPC, Wata Hukuma Ta Sa Lokacin Kai Shi Kotu

Tsugunne ba Ta Kare ba; El Rufai Na Tsare hannun ICPC, Wata Hukuma Ta Sa Lokacin Kai Shi Kotu

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, na ci gaba da zama a tsare a hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC
  • Hukumar DSS ta sanya lokacin gurfanar da tsohon gwamnan a gaban kotu kan wasu zarge-zarge da take yi masa
  • DSS ta gabatar da tuhume-tuhume uku a gaban kotu kan El-Rufai bisa zarge-zargen da ke alaka da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Hukumar tsaro ta farin Kaya (DSS) za ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a ranar 25 ga Fabrairu, 2026.

Hukumar DSS za ta gurfanar da Nasir El-Rufai ne gaban kotu kan zargin laifuffukan da suka shafi yanar gizo da barazana ga tsaron kasa.

Hukumar DSS za ta gurfanar da El-Rufai a gaban kotu
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai Hoto: @MuyiwaAdekeye
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta ce Mai shari'a Joyce Abdulmalik ta babbar kotun tarayya da ke Abuja ce ta sa wannan rana, bayan da shugaban alkalan kotun, mai shari'a John Tsoho, ya tura karar gare ta.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Jami'an ICPC sun kai samame gidan El Rufai, sun je neman wani abu

DSS ta shigar da tuhume-tuhume kan El-Rufai

Tun da farko, hukumar DSS ta shigar da tuhume-tuhume guda uku (3) a ranar Litinin kan El-Rufai, sakamakon zargin sa da hannu wajen saurare ko leken asirin wayar mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu.

A tuhuma ta farko DSS tana zargin cewa a ranar 13 ga Fabrairu, yayin da yake jawabi a matsayin bako a shirin Prime Time tashar Arise TV a Abuja, El-Rufai ya amince cewa shi da wasu mutanensa sun saurari wayar Nuhu Ribadu ba tare da izini ba.

Wannan laifi ne a karkashin sashe na 12(1) na dokar hana laifuffukan Intanet ta shekarar 2024, jaridar The Sun ta kawo labarin.

Ana zargin El-Rufai da sauraron wayar NSA

A tuhuma ta biyu ana zargin tsohon gwamnan da cewa a lokacin wannan hira a Arise TV, ya bayyana cewa ya san wani mutum kuma yana hulɗa da shi, wanda ya saurari wayar NSA ba tare da izini ba, amma El-Rufai ya ƙi kai rahoton wannan mutum ga hukumomin tsaro.

Kara karanta wannan

Halin da ake ciki yayin da El Rufai ke ci gaba da zama tsare a hannun EFCC

El-Rufai zai gurfana a gaban kotu
Nasir El-Rufai yayin hira da gidan talabijin Hoto: @elrufai
Source: Twitter

A tuhuma ta uku DSS tana zargin cewa El-Rufai da wasu mutanen da har yanzu ba a kama su ba, sun yi amfani da wasu na’urorin fasaha waɗanda suka kawo barazana ga tsaron ƙasa tare da sanya fargaba a zukatan ’yan Najeriya ta hanyar leƙen asirin wayar NSA.

Wannan ya saɓa wa sashi na 131(2) na dokar sadarwa ta Najeriya ta shekarar 2003.

ICPC ta tabbatar da tsare El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC ta tabbatar da cafke tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai.

Jami'an ICPC sun cafke tsohon gwamnan ne bayan ya kwashe kwanaki biyu a hannun hukumar EFCC kan binciken da take yi a kansa dangane da wasu zarge-zarge.

Shugaban sashin yada labarai na ICPC, J. Okor Odey, ya bayyana cewa sun karɓi El-Rufai a daga hannun hukumar EFCC a daren Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026, domin ci gaba da bincike

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng