Halin da Ake Ciki yayin da El Rufai Ke Ci Gaba da Zama Tsare a Hannun ICPC

Halin da Ake Ciki yayin da El Rufai Ke Ci Gaba da Zama Tsare a Hannun ICPC

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, yana tsare a hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC
  • Hukumar ICPC ta cafke tsohon gwamnan na Kaduna ne tare da tsare shi domin gudanar da bincike kan wasu zarge-zarge da ake yi masa
  • Ci gaba da rike shi na zuwa ne bayan ya samu beli daga wajen hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC bayan ya kwashe kwana biyu a can

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, na ci gaba da sake zama a tsare a hannun hukumar ICPC.

Ana sa ran zai kwashe dare na biyu a hannun hukumar ICPC, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.

Hukumar ICPC na ci gaba da tsare El-Rufai
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai Hoto: @elrufai
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta kawo rahoton cewa har zuwa yammacin ranar Alhamis, 19 ga watan Fabrairun 2026 babu wani rahoton tabbatar da an sake shi.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fusata da rigimar APC ta lakume rayukan mutane 2, ya ba da umarni

Nasir El-Rufai na hannun hukumar ICPC

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawar ta tabbatar da tsare shi tun da fari a cikin wata sanarwa da shugaban sashen yaɗa labarai da sadarwa na hukumar, Mista Okor Odey, ya sanya wa hannu.

ICPC ta fitar da sanarwar ne a shafinta na X kan tsare tsohon gwamnan na jihar Kaduna.

“Hukumar ICPC tana sanar da cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, yana hannunmu har zuwa lokacin tashi daga aiki a yau Laraba, 18 ga watan Fabrairu, 2026. Malam Nasir El-Rufai yana tsare ne a hukumar dangane da wasu bincike da ake gudanarwa."

- Okor Odey

Ana ci gaba da binciken El-Rufai

To sai dai kuma, majiyoyi masu masaniya kan lamarin sun bayyana cewa har yanzu masu bincike suna tattaunawa da tsohon gwamnan.

Wata majiya ta ce:

“Suna gudanar da tsarin bincike na yau da kullum, wanda ya haɗa da yi masa tambayoyi, karɓar bayanansa a karkashin doka, da kuma duba takardun kuɗi da na ayyukan da aka gudanar a lokacin gwamnatinsa.”

Kara karanta wannan

Babbar magana: Jami'an ICPC sun kai samame gidan El Rufai, sun je neman wani abu

Kayode Ogundamisi ya tabbatar da irin wannan zance a yammacin Alhamis a shafinsa na X.

Ci gaba da tsare El-Rufai a hannun ICPC ya biyo bayan abubuwan da suka faru a farkon wannan makon, bayan ya amsa gayyatar hukumar EFCC kan zargin karkatar da kuɗaɗe da ya shafi lokacin mulkinsa tsakanin 2015 zuwa 2023.

ICPC ta tsare El-Rufai a hannunta
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a dakinsa na littafai Hoto: @MuyiwaAdekeye
Source: Twitter

Hukumar EFCC ta fara tsare El-Rufai

'Dan siyasar ya kwashe dare biyu a babban ofishin EFCC da ke Abuja ana yi masa tambayoyi kan wasu ma’amaloli da ayyukan da aka gudanar a lokacin mulkinsa.

Hukumar EFCC ta ba wa El-Rufai belin gaggawa a yammacin ranar Laraba bayan kammala zagayen farko na tambayoyin.

To sai dai jim kaɗan bayan nan, wasu jami’ai masu ɗauke da makamai da aka jibge a wajen ofishin hukumar suka sake kama shi dangane da wani binciken na daban.

Hakeem Baba-Ahmed ya fadi matsalar El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mai ba mataimakin shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya yi magana kan Nasir El-Rufai.

Kara karanta wannan

Ramadan: Dakarun Hisbah sun cafke gandaye da rana gotai gotai a Kano

Hakeem Baba-Ahmed ya soki tsohon gwamnan na Kaduna, kan matakan da yake ɗauka yayin da yake fuskantar zarge-zargen cin hanci da rashawa.

Tsohon hadimin mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa Nasir El-Rufai mutum ne mara daukar shawara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng