Kwana Ya Kare: Ana Jimamin Rasuwar Sanata Ogbue, Najeriya Ta Sake Yin Babban Rashi
- Tsohon shugaban bankin UBA a Najeriya, Cif Israel C. Ogbue ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 99 a duniya
- A wata sanarwa da mahukuntan bankin suka fitar, sun bayyana marigayin a matsayin gogaggen ma'aikaci da ya bada gudummuwa mai yawa
- Bankin UBA ya miƙa ta’aziyyar ga ’ya’yansa, jikokinsa, danginsa da abokansa da sauran masu fatan alheri bisa wannan babban rashi
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Delta, Nigeria - Kwamitin daraktoci, shugabanni da ma’aikatan bankin UBA ya sanar da rasuwar tsohon Shugaban Bankin, Cif Israel C. Ogbue.
A wata sanarwa da bankin ya fitar a ranar Laraba, ya bayyana cewa Cif Ogbue ya rasu yana da shekaru 99 a duniya, kuma ya bar mata, ’ya’ya da jikoki.

Source: Facebook
UBA ya yabawa marigayi Ogbue
Sanarwar ta bayyana shi a matsayin gogaggen jagoran majalisar daraktoci kuma ƙwararren mai gudanarwa, kamar yadda Tribune Nigeria ta kawo.
Ta ce marigayin ya sadaukar da fiye da shekaru 60 yana hidima a sassan gwamnati da masu zaman kansu a Najeriya, inda ya bar tarihin riko da gaskiya, ladabi da kyakkyawan tsarin shugabanci.
Takaitaccen tarihin tsohon shugaban UBA
An haifi Cif Ogbue ranar 18 ga Fabrairu, 1927, a Onicha-Olona, Jihar Delta. Ya fara aikinsa ne a karkashin gwamnatin tarayya kafin ya tafi kasar Birtaniya domin ƙarin karatu.
Ya yi fice a aikinsa a Hukumar Inshora ta Ƙasa ta Najeriya (NICON), inda ya riƙe manyan mukamai har zuwa lokacin da ya yi ritaya a shekarar 1988.
Kwarewarsa a fannin shugabanci ta sa aka naɗa shi a kwamitocin daraktoci na manyan cibiyoyin hada-hadar kudi, ciki har da UBA.
Ya shiga Kwamitin Daraktocin UBA a 2005 a matsayin karamin darakta, sannan aka naɗa shi Shugaba a 2011, mukamin da ya riƙe cikin mutunci da hangen nesa har zuwa ritayarsa a 2013.
Baya ga nasarorin da ya samu a harkokin kasuwanci, Marigayi Ogbue ya kasance uba kuma jagora ga iyalinsa. Shi ne mahaifin Dr Awele Elumelu, kuma surukin shugaban rukunin UBA, Tony Elumelu.

Source: Facebook
Bankin UBA ya mika sakon ta'aziyya
Bankin UBA ya miƙa ta’aziyyar ga ’ya’yansa, jikokinsa, danginsa da abokansa, yana mai cewa:
“Muna murnar rayuwa mai cike da hidima, hikima da tasiri. Muna girmama gudummawarda ya bai wa bankin UBA da kuma harkokin kasuwanci a Najeriya.”
Sanarwar ta karkare da cewa nan ba da jimawa ba iyalansa za su sanar da shirye-shiryen jana’izarsa, kamar yadda The Cable ta kawo.
Sanata Barinada Mpigi ya rasu
A wani rahoton, kun ji cewa Sanatan da ke wakiltar mazabar Ribas ta Kudu maso Gabas a Majalisar Dattawa, Barinada Mpigi, ya riga mu gidan gaskiya.
Rahotanni sun ce Mpigi, wanda shi ne shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Ayyuka, ya mutu yana da shekaru 64 bayan ya sha fama da rashin lafiya
Shugaban kwamitin, Ogwoshi Onawo, ne ya bayyana labarin rasuwar a gaban ‘yan kwamitin inda suka nuna damuwa kan rashin da aka yi.
Asali: Legit.ng

