Ana Batun Dokar Zabe, Kotu Ta Ba Hukumar INEC Sabon Umarni

Ana Batun Dokar Zabe, Kotu Ta Ba Hukumar INEC Sabon Umarni

  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta samu sabon umarni daga wajen wata babbar kotun tarayya da ke Abuja
  • Babbar kotun tarayyar ta bukaci hukumar INEC da ta yi wa wata kungiyar siyasa rajista a matsayin jam'iyya
  • A hukuncin da koun ta yanke, ta umarci hukumar zabe da ta yi wa kungiyar rajista saboda ta cika sharuddan da doka ta tanada

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta yi rajistar kungiyar National Democratic Party (NDP) a matsayin jam’iyyar siyasa.

Kotun ta yanke hukuncin cewa kungiyar ta cika dukkan sharuɗɗan kundin tsarin mulki da na doka.

Kotu ta umarci INEC ta rajistar NDP a matsayin jam'iyya
Shugaban hukumar zabe ta INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan Hoto: @inecnigeria
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce mai shari'a M. G. Umar ne ya yanke hukuncin a ranar Litinin 16 ga Fabrairun 2026, biyo bayan karar da aka shigar a ranar 29 ga Disamba, 2025.

Kara karanta wannan

Ramadan: Dakarun Hisbah sun cafke gandaye da rana gotai gotai a Kano

Kotu ta umarci a yi wa kungiya rajista

A cikin kwafin hukuncin da manema labarai suka samu a ranar Alhamis, 19 ga watan Fabrairun 2026, kotun ta bayyana cewa masu shigar da karar sun cika sharudda.

Ta ce sun cika tanadin sassan 222-224 na kundin tsarin mulkin 1999 (wanda aka yi wa gyara), da kuma sassan 75 da 79 na dokar zaɓe ta 2022, gami da ka'idodin INEC na rajistar jam'iyyun siyasa.

Kotun ta bayyana cewa kungiyar siyasa ta masu shigar da karar, wato National Democratic Party (NDP), tunda ta cika dukkan sharuɗɗan doka, "ta cancanci a yi mata rajista a matsayin jam'iyyar siyasa."

Haka kuma, kotun ta yanke hukuncin cewa wajibi ne a kan INEC ta yi rajistar kungiyar a matsayin jam’iyyar siyasa kamar yadda doka ta tanada, jaridar The Punch ta kawo labarin.

An soke matsayar hukumar INEC

Mai shari'a Umar ya soke wasiƙar INEC mai lamba INEC/DEPM/AFR/979/1/144 mai kwanan watan 18 ga Disamba, 2025, wadda ta ƙi amincewa da rajistar ƙungiyar.

Kara karanta wannan

Katuwar bishiya ta kifo kan fasinjoji a mota, ta danne su sun mutu

Kotun ta bayyana wasikar a matsayin wadda ba ta da hurumi, kuma ba ta da wani tasiri a idon doka.

Bugu da ƙari, kotun ta fitar da umarni na tilas da ke tilasta wa INEC yi wa NDP rajista nan take a matsayin cikakkiyar jam'iyyar siyasa a Najeriya.

An sanya wa umarnin kotun hannu a Abuja ta hannun alkalin da ke sauraron ƙarar, sannan rajistaran kotun, Daisy Esa, ta buga masa tambari.

Kotu ta ba hukumar INEC umarni
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan Hoto: @inecnigeria
Source: Twitter

Kungiyoyi na son zama jam'iyyun siyasa

Wannan hukunci na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙaruwar ƙungiyoyin siyasa da ke neman tantancewa gabanin babban zaɓen 2027.

A cikin watannin baya-bayan nan, INEC ta tantance ƙungiyoyi da dama don yin rajista, kodayake guda biyu ne kawai aka yi wa rajista zuwa yanzu cikin dukkan waɗanda suka nuna sha'awa kuma suka cika sharuɗɗan farko.

Tsohon kwamishinan INEC ya shawarci Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Kwamishina a hukumar INEC, Mike Igini, ya jawo hankalin Shugaba Bola Tinubu kan dokar zabe.

Kara karanta wannan

Dokar zabe: Yadda APC ta bankara ta samu yadda ta ke so a majalisar tarayya

Mike Igini ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya janye hannunsa daga sa hannu kan kudurin dokar zaɓe ta shekarar 2026.

Tsohon kwamishinan na hukumar INEC ya bayyana cewa amincewa da dokar zaben zai iya jawo hargitsi a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng