Ramadan: Gwamna Abba Ya Tuna da Ma'aikata, Ya Yi Musu Tagomashi saboda Azumi
- Ma'aikatan gwamnati a jihar Kano sun samu sauki saboda shigowar watan azumin Ramadan mai alfarma
- Gwamnatin jihar Kano ta rage musu lokacin da za su rika tashi daga wuraren aiki domin samun sauki saboda shigowar Ramadan
- Sabodan tsarin lokacin aikin zai fara ne tun daga farkon watan azumin Ramadan har zuwa karshensa kafin a koma wanda ake amfani da shi a baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta amince da rage sa’o’in aiki ga ma’aikatan gwamnati.
Gwamnatin ta amince da rage lokacin tashi daga aikin ne domin karramawa da kuma saukakawa wa ma’aikata a lokacin watan azumin Ramadan na shekarar 1447AH (2026).

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce amincewar na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da kwanan wata 18 ga Fabrairu, 2026, wadda ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin na jiha ya fitar.
An rage wa ma'aikata lokacin aiki a Kano
Daraktar gudanarwa da ayyuka, Safiyya Suleiman, ce ta sanya wa takardar hannu a madadin shugaban ma’aikatan gwamnati.
A cewar takardar mai lamba HCS/LEV/2/V.II/177, ma’aikatan gwamnati za su samu rangwamen sa’a guda daga lokacin aikinsu na yau da kullum a duk tsawon watan azumi.
“Gwamnatin jihar Kano ta amince da rage sa’ar aiki guda ɗaya ga ma’aikatan gwamnati a lokacin azumin Ramadan na shekarar 1447AH."
- Safiyya Suleiman
Sabon jadawalin lokacin aiki a Kano
A ƙarƙashin wannan sabon tsari, lokacin aiki zai kasance kamar haka:
- Litinin zuwa Alhamis: Daga karfe 8:00 na safe zuwa 3:00 na rana (an rage sa’a ɗaya daga jadawalin da aka saba).
- Ranar Juma’a: Babu canji, za a fara daga karfe 8:00 na safe zuwa 1:00 na rana.
An aika da wannan umarni ga dukkan manyan jami’an gwamnati da hukumomi, ciki har da shugaban ma’aikata na fadar gwamnati, sakataren gwamnatin jiha, kwamishinoni, manyan sakatarori da shugabannin kotuna da na kamfanonin gwamnati.

Source: Facebook
Ana saukaka wa ma'aikata saboda Ramadan
Sanarwar ta bayyana cewa wannan sauyi ya yi daidai da al’adar da aka saba na ba da fifiko ga watan azumi mai alfarma.
“Wannan karramawa ce da ta yi daidai da al’adar ba da kulawa ta musamman ga watan Ramadan, domin bai wa ma’aikata damar gudanar da ibadun da ke tattare da wannan lokaci yadda ya kamata.”
- Safiyya Suleiman
Shugaban ma’aikatan ya kuma nuna fatan cewa za a yi amfani da wannan lokaci wajen yi wa jihar Kano da ma Najeriya baki ɗaya addu’ar dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Wannan umarni zai fara aiki ne daga ranar farko ta azumi har zuwa ranar ƙarshe.
Gwamnatin Kebbi ta rage lokacin aiki
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kebbi, karkashin jagorancin Gwamna Nasir Idris ta saukakawa ma'aikata saboda azumi.
Gwamnatin ta amince da rage sa’o’in aiki ga ma’aikatan gwamnati domin sauƙaƙa musu a lokacin azumin watan Ramadan.
Sabon lokacin aikin na ma'aikatan gwamnati zai fara ne daga karfe 8:00 na safe zuwa 2:00 na rana, daga ranar Litinin zuwa Alhamis.
Asali: Legit.ng

