Bayan Shekaru Ana Rigima kan Kujerarsa, Sarki Ya Raba Fada, Ya Bar Masu Duniyar
- An shiga jimami bayan sanar da mutuwar babban Sarki da ya shafe shekaru yana gwagwarmaya kan rikici game da kujerarsa da har yau ba ta kare ba
- Al’ummomin Egrangbene a Burutu, jihar Delta, sun sanar da rasuwar zababben Sarki, Henry Ambakederemo Okrikpa, yana da shekaru 70
- An ayyana zaman makoki gaba ɗaya a yankin, yayin da rikicin sarauta ya daɗe tun bayan naɗinsa a 2009, amma gwamnatin Delta ba ta amince da shi ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Asaba, Delta - Bayan shafe shekaru da dama ana rigima kan kujerar sarauta, Sarki ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da jinya.
Al’ummomin Egrangbene masu cin gashin kansu da suka haɗa da Masarautar Egrangbene a ƙaramar hukumar Burutu a jihar Delta, sun sanar da rasuwar marigayin.

Source: Facebook
An tabbatar da mutuwar Sarki a Delta
Hakan na cikin wata sanarwa da Okruzi na al’ummomin Egrangbene, Cif Felix Krokeme Maku, ya sanya wa hannu, cewar Punch.
Majiyoyi sun ce zababben Sarki, Henry Ambakederemo Okrikpa ya rasu yana da shekaru 70 a duniya bayan ya sha fama da jinya na wani lokaci.
Marigayin wanda ake kira Egbine-Agbe, shi ne Sarki na ɗaya na masarautar da ake shirin kafawa bayan shafe shekaru ana rigima kan kujerar sarauta.
An bayyana cewa zababben Sarkin ya rasu yana da shekaru 70 a duniya, ya bar ‘ya’ya uku, jikoki da sauran dangi da dama.

Source: Twitter
Mutuwar Sarki: Al'ummar gari sun fara zaman makoki
Al’ummomin Egrangbene sun ayyana zaman makoki gaba ɗaya kafin shirye-shiryen jana’izar marigayin, tare da bayyana cewa za a sanar da ranar binne shi ta hannun Mai Riƙon Sarautar masarautar da ake shirin kafawa, Cif Oboye Omonibeke.
An tabbatar da cewa an dade ana fama da rikicin sarauta a cikin al’ummar tun daga ranar da aka zaɓe shi aka kuma naɗa shi a ranar 16 ga Satumba, 2009, cewar Vanguard.
Sai dai gwamnatin jihar Delta ba ta taɓa amincewa da sarautarsa ba sakamakon takaddamar da ta dabaibaye zaɓensa a matsayin Sarki wanda ya shafi mulkin tsofaffin gwamnoni da dama.
Marigayin ya rasu ne a bana bayan ya sha fama da jinya na wani lokaci, inda ya bar iyalansa da al’umma cikin jimami da suke ganin ba za su iya mantawa nan kusa ba.
Fasto ya mutu yayin huduba a Delta
A wani labarin, an ji cewa al'ummar Kiristoci sun shiga wani irin yanayi bayan sanar da mutuwar daya daga cikin manyan Fastoci yayin da yake murnar sabuwar shekara a jihar Delta.
Cocin Katolika ya tabbatar da rasuwar Limami Rabaran Stephen Chukwuma, wanda ya rasu a daren sabuwar shekara a lokacin da yake murnar za a bar tsohuwar shekara.
An tabbatar da cewa an gudanar da jana’iza a ranar 28 ga Janairu, 2026 a Cocin St. Paul’s Cathedral, Issele-Uku da ke jihar wanda ya samu halartar manyan mutane a fadin kasa.
Asali: Legit.ng

