An kai Hari Gidan Sheikh Bashir Sokoto bayan Shan Ruwan Farko a Ramadan
- Malamin Musuluncin nan, Sheikh Bashir Ahmad Sani Sokoto ya yi magana kan cewa wasu mutane sun kai masa hari a gidansa
- Rahotanni sun nuna cewa malamin ya sanar da cewa an kai masa hari ne a rabar 1 ga watan Ramadan 1447 a gidansa da ke Sokoto
- Ya roki Allah SWT ya karbi ibadun da al'umma ke yi a Ramadan tare da cewa zai fara gudanar da tafsirin kamar yadda ya saba
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Sokoto - Sheikh Bashir Ahmad Sani Sokoto ya bayyana cewa wasu mutane na bibiyar rayuwarsa, suna yunkurin kashe shi.
A bayanin da ya yi, ya ce ba wannan ne karon farko da ake kai masa hari ba, ya ce ya yi magana a karon farko, ya yi shiru a na biyu, wannan ne na uku.

Source: Facebook
A bidiyon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa maharan sun kai farmaki ne a gidan sa da ke Gwiwa a Sokoto
Yaushe aka kaiwa malamin hari?
Rahotanni sun nuna cewa kai wa Sheikh Bashir Sokoto hari ne da dare jim kadan bayan shan ruwa a ranar 1 ga Ramadan na 1447/2026.
Malamin ya bayyana cewa ba wanda zai tsorata shi da irin wadannan hare haren da ake kai masa. Domin ba gudu ba ja da baya a kan abubuwan da ya ke yi.
Ya ce:
"Watakila rai na suke nema."
Ya kara da cewa idan haka ne:
"Mafarauta sun yi sake dan zaki ya girma."
Ya idan sun shirya, ga shi sai su zo su kashe shi. Amma kuma su san su shirya sosai domin ba zai zuba ido ba.
Malamin ya ce ya kamata masu shirya kai masa hari su san cewa ba alheri suke son kawowa jihar Sokoto ba. Ya ce idan tura ta kai bango, zai fito da wasu abubuwa da ya dade yana boyewa da za su ba mutane mamaki idan suka ji su.
Magana kan tafsiri da malamin ke yi
A cewar malamin ya shafe shekaru yana tafsirin Ramadan kuma ba zage-zage ko cin mutuncin mutane ya ke yi ba. Ya ce kullum kokari suke wajen karantar da mutane Alkur'ani mai girma da Hadisi a Sokoto da kewaye.
Sheikh din ya ce ya san abin da ke yi wa mutane ciwo game da shi, shi ne yadda ya samu karɓuwa a cikin gari da ƙauyuka.
Ya ce kusan kauyuka 65 da mutane kusan 300,000 sun tarbe su a kauyuka ba tare da cewa za su zo ba a lokacin wata ziyara.
Sheikh Bashir ya ce wasu da ba su samu ganinsa ba har kuka suke, wasu kuma su kashe kudi daga nesa suka ke har gidansa a Sokoto.

Source: Facebook
Addu'ar zaman lafiya a Sokoto
Ya roki Allah ya kawo zaman lafiya ga jihar Sokoto, Kaduna, Niger Kebbi, Zamfara da Kano da ma Palastinu Allah ya kawo musu zaman lafiya.
Malamin ya bayyana cewa ba ya tsoron mutuwa domin komai a hannun Allah ya ke, kuma annabawa ma da salihan bayi sun rasu.
Ya ce yana da tabbas cewa zai mutu, kuma ba zai mutu ba har sai kwanan shi ya ƙare, haka zalika mai neman rayuwarsa ma zai mutu. Kuma Allah zai yi Shari'a ta adalci a kan wanda ya kashe wani.
Malamai sun fara tafsiri a jihohi
A wani labarin, mun kawo muku rahoto manya malaman Musulunci a Najeriya sun fara gudanar da tafsirin Ramadan na shekarar 2026.
Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe da Farfesa Ibrahim Makari na tafsirin bana a birnin tarayya Abuja a wurare daban-daban.
Yayin da Farfesa Mansur Ibrahim Sokoto ke tafsirin Ramadan a masallacin Abu Huraira a Sokoto, Sheikh Sani Yahaya Jingir na yi a jihar Filato.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


