"Abin da Ya Kamata Ya Rika Hada Masu Arziki da Talakawa a Watan Ramadan," Gwamna Uba Sani

"Abin da Ya Kamata Ya Rika Hada Masu Arziki da Talakawa a Watan Ramadan," Gwamna Uba Sani

  • Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya taya daukacin al'ummar musulmi nurnar fara azumin watan Ramadan na shekarar 1447AH/2026
  • Uba Sani ya bukaci musulmi musamman masu arziki da su taimakawa talakawa domin neman lada a wurin Allah S.W.T
  • Gwamnan ya buƙaci dukkan mazauna Jihar Kaduna su ci gaba da yi wa jihar addu’ar zaman lafiya da haɗin kai

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya ja hankalin musulmi musamman masu rufin asiri domin su ribaci watan azumin Ramadan.

Sanata Uba Sani ya yi kira ga mazauna jihar Kaduna musamman attajirai da su buɗe gidajensu tare da raba abincin Ramadan ga marasa galihu.

Malam Uba Sani.
Mai girma gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani a fadar gwamnatinsa Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin saƙon barka da shigowar watan Ramadan da Gwamna Uba Sani ya wallafa shafinsa na Facebook, inda ya aike wa al’ummar Musulmi a Jihar Kaduna, Najeriya da ma duniya baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Ramadan: Kwankwaso ya tura sako na musamman ga musulmin Najeriya da na duniya

Ramadan: Shawarar Uba Sani ga attajirai

A cikin sanarwar, an ji gwamnan na cewa kamata ya yi jin ƙai da tausayi su zama ginshiƙin wannan wata mai alfarma da Ramadan.

Gwamnan Uba Sani ya bayyana cewa watan Ramadan ba kawai lokaci ba ne na kame kai daga ci da sha, sai dai “makarantar tarbiyya ce da kuma tsaftace zuciya.”

Ya ce Ramadan dama ce ga muminai su yi zurfin tunani, su kara dagewa da ibada, sannan su ƙarfafa fahimtar juna a matsayin al’umma ɗaya.

Mu buɗe gidajenmu da zukatanmu,” in ji gwamnan, yana kira ga jama’a su raba abinci, da wani sashe na dukiya ga masu buƙata, tare da girmama mutuncin kowane ɗan Adam.

Gwamna Uba Sani ya roƙi Allah Maɗaukaki da ya ba muminai ƙarfi, natsuwa da yalwar albarka yayin da suke aiwatar da ibadar azumi, wanda ya kasance daya daga cikin ginshiƙan Musulunci.

Uba Sani ya bukaci a sa Najeriya a addu'a

Kara karanta wannan

Ramadan: Gwamna Zulum ya ware Musulmi da Kiristoci 300,000, ya raba tallafin azumi

Baya ga haka, gwamnan ya buƙaci dukkan mazauna Jihar Kaduna su ci gaba da yi wa jihar addu’ar zaman lafiya da haɗin kai, yana mai cewa duk da bambance-bambancen addini da al’adu, sun kasance tsintsiya guda.

Uba Sani.
Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani yana ganawa da kwamishinoni Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

Ya kuma sake jaddada aniyar gwamnatinsa na inganta zaman lafiya, farfaɗo da tattalin arziki da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa ga kowa da kowa.

“Allah Ya sanya hasken wannan wata mai albarka ya haskaka zukatanmu, ya kuma jagoranci tafiyarmu ta bai ɗaya,” in ji shi.

Gwamna Zulum ya yi rabon tallafin azumi

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya kaddamar d rabon tallafin azumi ga Musulmai da Kiristoci a fadin jiharsa.

Gwamna Zulum ya ce an shirya wannan tallafi ne domin rage radadin matsin tattalin arziki da ke addabar al’umma masu rauni.

Babagana Zulum ya bayyana cewa kowane gida daga cikin gidaje 300,000 da za su amfana da tallafin zai samu buhun shinkafa, gero da sukari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262