Ana Wata ga Wata: Jami'an DSS Sun Cafke El Rufai a Harabar Ofishin EFCC

Ana Wata ga Wata: Jami'an DSS Sun Cafke El Rufai a Harabar Ofishin EFCC

  • Jami'an DSS sun kama tsohon Gwamna Nasir El-Rufai nan take bayan fitowarsa daga ofishin hukumar EFCC a daren ranar Laraba
  • Ana zargin El-Rufai da sauraren kiran wayar NSA Nuhu Ribadu ba tare da izini ba wanda hakan ya saba wa dokokin yanar gizo
  • Kamun da DSS ta yi masa na nufin cewa El-Rufai zai fuskanci tarin shari'o'i a lokaci guda, yayin da ake jiran ranar da za a gurfanar da shi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - A daren Laraba, hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, jim kaɗan bayan EFCC ta sake shi daga rikon kwanaki biyu da ta yi masa.

El-Rufai ya kasance a hannun EFCC tun ranar Litinin kan zargin almundahanar kuɗaɗe, inda aka ba da shi beli da misalin ƙarfe 8:00 na dare.

Kara karanta wannan

El Rufai ya shafe kwanaki 2 a hannun EFCC, lauyansa ya fadi shirin da ke ƙasa

Jami'an SSS sun kama El-Rufai a harabar EFCC
Malam Nasir El-Rufai a cikin mota jim kadan bayan ya isa ofishin EFCC a Abuja. Hoto: @MuyiwaAdekeye
Source: Twitter

Jami'an DSS sun kama El-Rufai

Sai dai jami'an DSS da ke ɓoye sun yi masa kwanton ɓauna a harabar EFCC, inda suka yi awon gaba da shi zuwa hedikwatarsu da ke Asokoro, in ji rahoton The Cable.

Kama El-Rufai da hukumar DSS ta yi yana da alaƙa da zargin cewa ya sa an riƙa sauraren tattaunawar wayar mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ba tare da izini ba.

A ranar Litinin ne DSS ta shigar da ƙarar sa mai lamba (FHC/ABJ/CR/99/2026) a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan zargin aikata laifuffukan yanar gizo.

A ranar Juma'a, El-Rufai ya yi ikirarin cewa ya ji muryar NSA yana ba da umarnin a kama shi lokacin da yake filin jirgi.

Hukumar DSS ta ce kalaman nasa sun tabbatar da cewa ya sa an yi leken asirin sadarwar babban jami'in tsaron ƙasa, wanda hakan ya saɓa wa dokar "Cybercrimes Act 2024".

Kara karanta wannan

Yadda jama'a suka fito zanga zanga da El Rufa'i ya ziyarci EFCC

Masu shigar da ƙara sun ce matakin nasa ya raunana tsaron ƙasar Najeriya baki ɗaya.

Takaddamar da ta faru a filin jirgi

Wannan dambarwa ta samo asali ne tun ranar Alhamis, inda El-Rufai ya yi musayar kalamai masu zafi da jami'an tsaro a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Wasu shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa an ƙwace fasfon El-Rufai kafin magoya bayansa su fito su hana a tafi da shi, kamar yadda rahoton Legit Hausa ya nuna.

A tattaunawa da Arise News, El-Rufai ya ce ya ji Nuhu Ribadu yana waya, yana ba da umarni a kama shi.
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai a dakin watsa shirye-shirye na Arise News. Hoto: @elrufai
Source: Twitter

Siyasar 2027 da shiga jam'iyyar ADC

Premium Times ta rahoto cewa Nasir El-Rufai dai ya taɓa zama babban aminin Shugaba Bola Tinubu, amma alakarsu ta yi tsami tun bayan da aka ƙi rantsar da shi a matsayin minista.

A halin yanzu da El-Rufai ya fice daga jam'iyyar APC ya koma jam'iyyar ADC, kuma ya lashi takobin yin aiki da sauran ƴan siyasa domin ganin Tinubu bai zarce ba a zaben 2027.

Har yanzu dai tsohon gwamnan na jihar Kaduna yana fuskantar bincike kan zargin ɓatar da ₦423 billion lokacin yana gwamna.

Kara karanta wannan

El Rufa'i ya amsa gayyata, zai kai kansa ofishin EFCC a yau

Wannan kama shi da DSS ta yi ya nuna cewa tsohon gwamnan zai fuskanci shari'o'i masu yawa a lokaci guda, yayin da ake jiran sanar da ranar da za a gurfanar da shi a gaban kotu.

El-Rufai ya shafe kwana 2 a hannun EFCC

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Nasir El-Rufai ya sake kwana a hannun hukumar EFCC yayin da ake gudanar da bincike kan zargin bacewar N432bn.

Lauyan tsohon gwamnan na Kaduna ya bayyana cewa wanda yake karewa mutum ne mai daraja wanda ya dawo gida Najeriya don amsa gayyatar EFCC.

An samu rahoto cewa EFCC na shirin neman izinin kotu domin tsawaita tsare tsohon gwamnan da nufin kara titsiye shi kan zarge-zargen da ake yi masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com