Akwai Matsala: Tsohon Kwamishinan INEC Ya Ba Tinubu Shawara kan Dokar Zabe
- Ana ci gaba da muhawara kan batun dokar zabe ta shekarar 2026 da Majalisar dattawa da Majalisar wakilai suka amince da ita
- Tsohon kwamishina a hukumar INEC, Mike Igini, ya ba da shawara ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan sanya hannu a dokar zaben
- Mike Igini ya tunatar da Shugaban kasar matsalar da dokar za ta iya haifarwa a kasar nan idan ya amince ya sanya mata hannu a haka
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon kwamishina a hukumar INEC, Mike Igini, ya ba da shawara ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan dokar zabe.
Mista Mike Igini ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya janye hannunsa daga sa hannu kan kudurin dokar zaɓe ta shekarar 2026.

Source: Facebook
Mike Igini ya yi wannan kiran ne ranar Laraba, 18 ga watan Fabrairun 2026 yayin wata hira da tashar Arise News.
Kalamansa na zuwa ne biyo bayan amincewa da kudurin da Majalisar dattawa ta yi, wanda ya haɗa da wasu tanade-tanade masu ruruta takaddama game da tura sakamakon zaɓe ta yanar gizo.
Wace shawara aka ba Shugaba Bola Tinubu?
Tsohon kwamishinan ya bayyana dokar a matsayin “hanyar samar da hargitsi” wadda za ta iya gurgunta tsarin dimokuradiyya na Najeriya.
“Hakika, shawara ta ga shugaban kasa ita ce; kai mutum ne mai tarihi. Ka kasance babba ga dama daga cikinmu a lokacin fafutuka, a lokacin da tafiyar Najeriya da makomar dimokuradiyya ba su da tabbas."
- Mike Igini
An tunatar da Tinubu tsohon tarihi
Igini ya kara tunatar da shugaban kasa fafutukar shekarar 2015 domin tabbatar da cewa zaɓe ya nuna muradin jama'a.
“Kuma ka tuna cewa, a lokacin da jam’iyyar PDP take kan mulki, wasu suna cewa za a yi amfani da ikon gwamnatin tarayya, amma wasu daga cikinmu mun tsaya mun ce a'a."
“A shekarar 2015, ikon jama'a ne ya yi tasiri, ba ikon gwamnatin tarayya ba. Ikon jama'a ta hanyar kuri'a shi ne ya kamata ya nuna abin da zai faru."

Kara karanta wannan
Rigimar da ta kaure a Majalisar wakilai ta kara tsanani, wasu yan majalisa sun yi fushi
"Ya kamata ka zama mutum mai kishin tarihi; duk abin da aka ajiye a gabanka (wannan dokar), mayar da shi, kada ka sanya masa hannu."
- Mike Igini

Source: Twitter
Igini ya soki bangaren shari'a
Da yake magana kan bangaren shari'a, Mike Igini ya ce a tarihi, kotuna sun gaza wajen kare masu kada kuri'a da kuma kiyaye dimokuradiyya.
“Babban zaɓin da muke da shi shi ne ɓangaren shari’a wanda dole ne ya tsaya tsayin daka wajen kare dimokuradiyya da bin doka da oda. Ba don ɓangaren shari'a ba, da ba mu kai inda muke a yau ba."
“Ina da dukkan bayanan gazawar da aka yi. Idan aka zo batun zaɓe, ɓangaren shari’a ba su yi ƙoƙari ba."
- Mike Igini
Majalisar wakilai ta yi gyara a dokar zabe
A wani labarin kuma, kun ji cewa a ranar Talatar nan, Majalisar wakilan Najeriya ta yi gyara ga kudurin dokar zabe na shekarar 2026.
Majalisar wakilan karkashin jagorancin Tajudeen Abbas ta janye matsayar da ta ɗauka a baya kan sashe na 60 (3) na dokar zaɓe.
Hakazalika, majalisar ta amince da nau’in da majalisar dattawa ta riga ta amince da shi, wanda ya ba da damar tura sakamakon zaɓe ta yanar gizo da kuma ta takarda.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
