Abin da Ya Sa Shehun Borno Ya Sanar da Ganin Watan Ramadan maimakon Sarkin Musulmi

Abin da Ya Sa Shehun Borno Ya Sanar da Ganin Watan Ramadan maimakon Sarkin Musulmi

  • Mai Martaba Shehun Borno, Alhaji Abubakar Umar Elkanemi ya sanar da ganin jinjirin watan Ramadan a Najeriya a jiya Talata, 17 ga Fabrairun 2026
  • Sai dai hakan wani sabon abu ne da ba a saba gani ba domin an saba jin sanarwa ne kai tsaye daga Mai Alfarma Sarkin Musulmi a garin Sokoto
  • Tuni dai mafi yawan musulmi a Najeriya suka tashi da azumi a yau Laraba, 1 ga watan Ramadan, 1447AH daidai da 18 ga watan Fabrairu, 2026

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Borno, Nigeria - Mai Martaba Shehun Borno, Abubakar Umar Elkanemi ya tabbatar da ganin jinjirin watan Ramadan da yammacin jiya Talata, 29 ga watan Sha'aban, 1447AH dai da 17 ga Fabrairun 2026.

Basaraken ya kasance shi ne mataimakin Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA).

Kara karanta wannan

Ramadan: Gwamna Zulum ya ware Musulmi da Kiristoci 300,000, ya raba tallafin azumi

Shehun Borno da Sarkin Musulmi.
Shehun Borno, Abubakar Umar Elkanemi da Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III Hoto: Daular Usmaniyya
Source: Facebook

A rahoton da Daily Trust ta dauko, Fadar Sarkin Musulmi ta tabbatar da ganin watan kamar yadda Shehun Borno ya sanar a wata sanarwa da shugaban kwamitin duban wata, Farfesa Sambo Wali Junaidu ya rattaba hannu.

Meyasa Shehun Borno ya sanar da ganin wata?

Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ta bayyana cewa Shehun Borno ya sanar da ganin watan Ramadan ne saboda Sarkin Musulmi ya yi tafiya zuwa kasar waje.

A cewar NSCIA, sakamakon Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III, ba ya kasar, shi yasa Shehun Borno kuma mataimakin shugaban Majalisar ya wakilce shi.

Mai martaba Shehun Borno shi ne na biyu a wannan kungiya da aka kafa a shekarar 1973 kamar yadda bayanai daga shafin NSCIA na yanar gizo ya nuna.

A daidai lokacin da za a fara azumin, an ji cewa Mai alfarma Sarkin Musulmi ya tafi Umrah a Saudiyya.

Kara karanta wannan

Ramadan: Coci ya yi abin alheri, ya raba wa Musulmi, makarantun tsangaya kayan abinci

Basaraken na Borno ya sanar da cewa an ga jinjirin wata a ranar Talata, 17 ga Fabrairu, wanda ya yi daidai da ranar 29 ga Sha'aban 1447AH.

Yadda aka ga jinjirin wata a Najeriya

Ya bayyana cewa an samu rahotannin ganin wata daga sassa daban-daban na kasar nan kuma Fadar Sarkin Musulmi ta tabbatar da hakan kuma ta amince da su.

Don haka ya umarci musulmi su tashi da azumi a ranar Laraba, 18 ga watan Fabrairu, 2026, ranar da ya ayyana a matsayin 1 ga watan Ramadan, 1447AH.

Fadar Sarkin Musulmi ta wallafa bidiyon sanarwar da Shehun Borno ya yi a madadin mai alfarma Sarkin Musulmi a shafin Daular Usmaniyya na Facebook a daren jiya Talata.

Tuni dai shugabanni da manyan jiga-jigai a Najeriya suka fara taya musulmi murnar zagayowar wannan wata mai albarka.

Duba wata.
Na'urar da ake amfani da ita wajen duban jinjirin wata a kasar Saudiyya Hoto: Inside The Haramain
Source: Twitter

Oluremi Tinubu ya taya Musulmi murna

Uwargidar shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu ta taya al'ummar musulmi murna, tare da rokonsu da su sanya Najeriya a cikin addu'o'i domin samun zaman lafiya da ci gaba.

Kara karanta wannan

An ga watan azumin Ramadan a Najeriya, Sarkin Musulmi ya fitar da sanarwa

Ta ce:

"Ina taya Musulmai murnar shiga wannan wata na Ramadan mai albarka. Ina addu'ar wannan wata mai tsarki ya kawo muku da iyalanku da kuma kasa baki daya zaman lafiya, farin ciki, da ci gaba."
"A cikin wannan wata na azumi, ina roƙon mu duka mu tuna da al'ummarmu a cikin addu'o'i don samun zaman lafiya da wadata mai yawa. Allah Madaukakin Sarki Ya karɓi addu'o'inmu, Ya gafarta mana zunubanmu."

Rukunin mutane 7 da za su iya shan azumi

A wani rahoton, mun kawo jerin mutane bakwai da addinin musulunci ya amince su ajiye azumi a watan Ramadan sakamakom wata lalura ko wasu dalilai masu karfi.

Shugaban Cibiyar Da'awa da Ilimi a Jami'ar Muhammadiyah Surakarta (UMS) ya bayyana cewa Allah SWT ya yi sassauci ga Musulmin da ba za su iya yin azumi ba.

Tsofaffi waɗanda ba su da ƙarfin jure yunwa da ƙishirwa saboda tsufana daga cikin rukunin mutanen da aka amince su sha azumi a watan Ramadan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262