Dokar Zabe: Yadda APC Ta Bankara Ta Samu Yadda Ta ke So a Majalisar Tarayya
- Jam'iyya mai mulki ta APC ta yi amfani da rinjayen da take da shi a Majalisun dattawa da wakilai wajen tabbatar da gyaran dokar zabe
- Sashe na 60(3) ya amince da tura sakamakon zabe ta na’ura, amma ya bar kofar amfani da takarda idan karfin hawa yanar gizo ya gaza
- APC ta samu rinjayen kashi biyu bisa uku a majalisun biyu bayan sauya sheƙar ‘yan adawa, wanda ya ba ta damar saun yadda ta ke so
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa
FCT Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki ta sake nuna karfinta a majalisar dokoki ta kasa yayin da ta jagoranci amincewa da sabon fasalin sashe na 60(3) na kudirin gyaran dokar zabe.
Wannan sashe ya shafi wajabcin tura sakamakon zabe kai tsaye ta na’ura daga kowace rumfar zabe zuwa dandalin IReV na hukumar zabe ta kasa (INEC).

Kara karanta wannan
Majalisar dattawa ta ji koken musulmai, ta gyara dokar zabe saboda azumin Ramadan

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa sabon tanadin ya ce jami’in zabe zai aika sakamako ta hanyar lantarki bayan ya sanya hannu tare da hatimi a kan fam din EC8A.
Majalisa: APC ta samu yadda ta ke so
The Guardian ta wallafa cewa za a bukaci wakilan jam’iyyu su sanya hannu a kan fam din idan suna wurin kafin a mika ga hukumar zabe.
Sai dai an kara sharadi cewa idan tura sakamakon ta na’ura ta gagara sakamakon matsalar sadarwa, to fam din EC8A da aka rattaba wa hannu shi ne zai zama tushen tattarawa da ayyana sakamako.

Source: Facebook
APC ta samu wannan nasara ne bayan yawan kujerunta ya karu a majalisun biyu sakamakon sauya sheƙar wasu ‘yan adawa.
Haka kuma hukuncin kotu da ya soke wasu nasarorin ‘yan jam’iyyar PDP a jihohi irin su Filato ya kara wa 'yan adawa rinjaye.
A majalisar wakilai mai kujeru 360, APC na da akalla kujeru 241, abin da ya wuce rinjayen kashi biyu bisa uku.
Jam'iyyar APC ta kara yawa a majalisa
A Majalisar dattawa kuwa, APC na da sanatoci 80 cikin 109, yayin da PDP ke da 21, sai LP da uku, APGA da biyu, da kuma NNPP mai kujera daya.
A zaman Majalisar dattawa, sanatoci 55 sun kada kuri’ar amincewa da sharadin da ke ba da damar amfani da takarda idan na’ura ta gaza, yayin da 15 suka yi adawa.
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana matakin a matsayin babbar kirkira tun 1960, yana mai cewa hakan zai ba jam’iyyu damar kare kuri’unsu.
Da fari Majalisar wakilai ta amince da wajabcin tura sakamako ta na’ura kadai. Amma a zaman gaggawa da Mataimakin kakakin majalisa, Benjamin Okezie Kalu, ya jagoranta, an janye.
Matakin ya haifar da ce-ce-ku-ce da zanga-zangar ficewar wasu yan majalisa, suna zargin APC da amfani da rinjaye wajen kakaba ra’ayinta.
Duk da haka, rinjayen da jam’iyya mai mulki ke da shi a majalisun biyu ya ba ta damar tabbatar da kudirin cikin sauki.
Majalisar dattawa ta ji koken Musulmi
A wani labarin, kun ji cewa Majalisar dattawa ta saurari koken 'yan Najeriya kan sanya ranakun babban zabe mai zuwa na 2027 a watan azumin Ramadan.
A zaman da ta yi a ranar Talata 17 ga watan Fabrairu, 2027, Majalisar ta gyara sashen da zai ba hukumar INEC damar canza ranakun da ta sanar idan da bukatar hakan.
Haka zalika yunkurin Sanata Enyinna Abaribe na gyara tanadin dokar tura sakamakon zabe ta intanet bai yi nasara ba bayan kada kuri'a, inda APC ta samu rinjaye.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

