Shugaban APC Ya Ziyarci Sheikh Daurawa bayan Sauya Shekar Abba Kabir
- Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya ziyarci shugaban hukumar Hisbah na jihar Kano, Aminu Ibrahim Daurawa
- Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa ya dauki nauyin adadin wasu dalibai a makarantar Zamzam da Sheikh Daurawa ke jagoranta
- Hakan na zuwa ne bayan jam'iyyar APC mai mulki ta gudanar da taron karbar gwamna Abba Kabir Yusuf a jihar Kano da ya sauya sheka daga NNPP
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Shugaban kwamandan Hisbah a Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya karbi shugaban jam'iyyar APC a Najeriya, Farfesa Nentawe Yilwatda a ofishinsa.
Bayan ziyarar, Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana cewa dangartakarsa da Sheikh Aminu Daurawa ta fara ne tun shekarun baya.

Source: Facebook
Shugaban APC ya ziyarci Daurawa

Kara karanta wannan
Kurunkus: Gwamna Abba ya bayyana ainihin dalilinsa na komawa APC a gaban Shettima
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, Farfesa Nentawe Yilwatda ya bayyana Sheikh Daurawa a matsayin jajirtaccen mutum, inda ya ce:
"A yau na kai ziyarar girmamawa ga kwamandan Hisbah na Kano, Imam Aminu Ibrahim Daurawa, mutum mai jajircewa wajen addini, tarbiyya da jin ƙai.
"Baya ga rawar da yake takawa a fili, yana tafiyar da makarantar Zamzam, wadda ta zama mafaka ga marasa galihu, 'yan gudun hijira da kuma waɗanda ba su samu kulawa ba."
Yayin da ya ke magana kan alakarsa da Sheikh Daurawa, shugaban APC ya ce:
"Dangantakarmu ta fara ne tun lokacin da nake ministan harkokin jin-ƙai da rage talauci, inda aka gina ta bisa mutunta juna kan akidunmu na addini da kuma imanin cewa hidima ga bil’adama ibada ne."
Batun daukar nauyin dalibai mata
Bayan tattaunawa da Sheikh Daurawa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya sanar da cewa ya dauki nauyin wasu dalibai 'yan makarantar Zamzam zuwa jami'a.
Ya ce:
"A yau na ɗauki alƙawarin ɗaukar nauyin ’yan mata 15 da aka gyara tarbiyyarsu, waɗanda suke da hazaka da ƙwazo, kuma yanzu sun cika sharuddan shiga jami’a.
"Na kuduri aniyar tallafa musu a karatun jami’a daga farko har zuwa kammalawa. Idan ka ilimantar da mace, ka ɗaga darajar al'umma ne, ka ƙarfafa al’umma, kuma ka gina ƙasa mai kyau."

Source: Facebook
Kokarin kara hadin kai a Najeriya
Shugaban jam'iyyar APC ya bayyana cewa ganawarsa da sauran shugabannin addini da jama'ar Kano manufa ce ta kara karfafa hadin kai.
Nentawe Yilwatda ya ce:
"Manufa guda ce: ƙarfafa haɗin kan jama’a, bunƙasa haƙuri da juna tsakanin mabiya addinai, da kuma karfafa zaman lafiya a ƙasarmu mai daraja. Kada bambance-bambancenmu su raba mu, su zama tushen ƙarfimmu."
An karbi Abba Kabir a APC
A wani rahoton, kun ji cewa shugabannin jam'iyyar APC a Najeriya sun karbi Abba Kabir Yusuf da sauran jami'ansa da suka sauya sheka daga NNPP.
Shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda, jagoran APC a Kano, Abdullahi Ganduje da wasu manyan 'yan siyasa sun halarci bikin da aka yi.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa ya koma APC ne saboda son kawo cigaba ga jihar Kano da ya ke fatan gani an samu.
Asali: Legit.ng
