An ga Watan Azumin Ramadan a Najeriya, Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwa

An ga Watan Azumin Ramadan a Najeriya, Sarkin Musulmi Ya Fitar da Sanarwa

  • Sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar III, ya tabbatar da ganin jinjirin Ramadan, ya ayyana 18 ga Fabrairu a matsayin ranar farko ta azumi
  • Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai El-Kanemi, ne ya sanar da ganin watan a madadin Sarkin Musulmi
  • An ce Sarkin Musulmi ya wakilta Shehun Borno ne saboda tafiyarsa ƙasa mai tsarki domin gudanar da ibadar Umrah

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Maiduguri, Borno - Kwamitin ganin wata a Najeriya ya fitar da sanarwa kan ganin watan Ramadan domin fara azumi a kasar.

Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III ya tabbatar da ganin jinjirin watan Ramadan a Najeriya a daren yau Talata 17 ga watan Faburairun 2026.

Sarkin Musulmi ya fitar da sanarwa kan azumin watan Ramadan
Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar III. Hoto: The Sultanate Council Media Team.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da shain kwamitin ganin wata a Najeriya ya wallafa a X a yau Talata 17 ga watan Faburairun 2026.

Kara karanta wannan

2026: Abubuwa 10 da ya kamata Musulmi ya sani kafin fara azumin watan Ramadan

Sarkin Musulmi ya tabbatar da ganin watan Ramadan

An tabbatar da ganin watan a yau Talata 17 ga watan Faburairun 2026 bayan wasu amintattu sun tabbatar da ganin wata a yankunansu.

Sanarwar da aka fitar da kawo karshen watan Sha'aban tare da tabbatar da shiga Ramadan wacce ta kasance mafi girma da daraja a cikin sauran watannin Musulunci.

"SANARWAR GANIN JINJIRIN RAMADAN!
"Assalamu alaikum,
"Mai Martaba ya tabbatar da ganin jinjirin watan Ramadan a Najeriya, kuma ya ayyana cewa gobe, 18 ga Fabrairu, za ta zama ranar farko ta Ramadan 1447AH."
Shehun Borno ya wakilci Sarkin Musulmi a sanar da ganin watan Ramadan
Shehun Borno, Mai Martaba Alhaji (Dr.) Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin El-Kanemi . Hoto: Borno state Government.
Source: Facebook

Shehun Borno ya sanar da ganin watan Ramadan

Wani mai amfani da shafin X, Imran Muhammad ya wallafa bidiyon sanar da ganin watan Ramadan da aka yi a daren yau Talata 17 ga watan Faburairun 2026.

Mai Martaba, Shehun Borno, Alhaji (Dr.) Abubakar Ibn Umar Garbai Al-Amin El-Kanemi shi ya tabbatar da ganin watan domin fara azumin Ramadan.

Basaraken ya sanar da ganin wata a madadin Sarkin Musulmi, Mai Alfarma, Muhammad Sa'ad Abubakar III bayan wakilta shi.

Kara karanta wannan

Saudiyya ta sanar da ranar fara azumi bayan ganin watan Ramadan

Majiyoyi sun tabbatar da cewa Sarkin Musulmi ya wakilta Shehun Borno bayan ya tafi kasar mai tsarki domin gudanar da ibadar Umrah.

Saudiyya ta tabbatar da ganin watan Ramadan

Mun ba ku labarin cewa Gwamnatin kasar Saudiyya ta sanar da cewa an ga watan Ramadan a yammacin yau Talata, 17 ga watan Fabrairun shekarar 2026.

Hakan na zuwa ne bayan fara duba jinjirin wata da hukumomin kasar suka yi bisa umarnin da gwamnati ta bayar ga 'yan kasar baki daya.

An samu rahotanni game da sakamakon duba watan Ramadan a wasu kasashen Musulmi da sauransu da ke fadin duniya a yau Talata 17 ga watan Faburairun 2026.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.