2026: Abubuwa 10 da Ya Kamata Musulmi Ya Sani kafin Fara Azumin Watan Ramadan
- Musulmai a fadin duniya sun fara duban jinjirin watan Ramadan a yau Talata domin fara gudanar da azumin wannan shekara ta 2026
- Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad Abubakar II ne yake sanar da ranar fara azumi a Najeriya yayin da a Saudiyya ma aka ga wata
- A cikin watannan rahoto, Legit Hausa ta jero abubuwa 10 da ya kamata Musulmi ya sani kafin fara azumi, tare da da shawarwarin masana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
A yayin da azumin Ramadan na 2026 ya iso, Musulmi a Najeriya da daukacin duniya na kan shirya tarbar wannan wata mai albarka, wata ibada da yawan sadaka.
A mafi yawan kasashe, yau Talata, 17 ga Fabrairu, 2026 ake duban watan Ramadan, kuma tuni wasu kasashen sun ga jinjirin watan, har sun sanar da ranar fara azumi.

Source: Getty Images
Abubuwa 10 da ya kamata Musulmi ya sani
A wannan gabar, Channels TV ta jero wasu muhimman abubuwa 10 da ya kamata Musulmi su sani kafin fara azumin watan Ramadan na 2026:
1. Ganin watan Ramadan
Ramadan, wanda shi ne wata na tara a kalandar Musulunci, yana farawa ne daga lokacin da aka sanar da ganin jinjirin wata.
2. Sanarwar ganin wata
A hukumance, Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’adu Abubakar III, wanda kuma shi ne shugaban Majalisar Ƙoli ta Harkokin Musulunci a Najeriya (NSCIA), shi ne yake yin sanarwar fara azumi a ƙasar nan.
3. Tsarkake niyyar fara azumi
Ana ƙarfafa wa Musulmi gwiwa da su tunkari azumin ta hanyar tsarkake niyya, yawaita karatun Alkur’ani, neman gafarar mutane, yin nazari kan halaye, da kuma kiyaye dukkan abin da shari'a ta ce a kiyaye a cikin wannan wata mai tsarki.
4. Neman kusanci ga Allah SWT
Ramadan, ba wai yakan ta'allaka ne a kan kauracewa ci ko sha ba, yakan zama lokaci na gyara halaye, kara kusanci ga mahallaci da kuma dukufa wajen neman Aljannah.
Tasirin Ramadan ga Musulmi
5. Tasirin Ramadan ga kasuwanci
A lokacin Ramadan, ana sa ran harkokin kasuwanci za su karu, inda za a ga iyalai na sayen kayayyakin abinci fiye da yadda aka saba, kuma hakan na iya kara kudin kayan, in ji rahoton Punch.
6. Yawan bada sadaka
Bayar da sadaka na daga cikin manyan ayyukan alheri a Ramadan. A watan ne ake so Musulmai masu hannu da shuni su karfafa bada zakkar kono da wuri, su kuma taimaka wa mabukata ta hanyar sadaka da kuma shirin ciyarwa.
7. Hakuri da jin-kai a Ramadan
Baya ga azumi, Ramadan lokaci ne da Musulmi ke kara koyon hakuri, nuna jin-kai da kuma kiyaye ibada, da ka iya dorewa a rayuwarsu har bayan azumin.

Source: Getty Images
8. Tururuwar Musulmi a Makkah da Madina
Idan lokacin Ramadan ya zo, ana samun tururuwar al'ummar Musulmi da ke zuwa Makka da Madina domin gudanar da ibadar Umrah tare da yin azumi a can.

Kara karanta wannan
Rigimar da ta kaure a Majalisar wakilai ta kara tsanani, wasu yan majalisa sun yi fushi
9. Kiyaye cin abinci a Ramadan
Masana abinci na shawarwar Musulmi su rika daidaita abincin da za su rika ci a lokutan Sahur da Buda Baki, domin kula da lafiyarsu. Hakanan, ana so a rika samun hutu, da zama wuri mai inuwa don kiyaye tsotsewar ruwan jiki.
10. Kyautata alaka
A cikin watan Ramadan, ana samun kyautatuwar alakar mutane. Iyalai, ko kuma al'ummar gari kan rika haduwa waje daya domin yin buda baki.
Ana samun masallatai da ke jagorantar buda baki, sannan Musulmi na haduwa a wuri daya don yin sallar Asham, Tahajjudi da kuma Itikafi, duk don neman yardar Allah.
An ga watan azumi a Saudiyya
A wani labari, mun ruwaito cewa, Saudiyya ta sanar da cewa an ga watan Ramadan a yammacin yau Talata, 17 ga watan Fabrairun shekarar 2026.
Hakan na zuwa ne bayan fara duba jinjirin wata da hukumomin kasar suka yi bisa umarnin da gwamnati ta bayar ga 'yan kasar baki daya.
An samu rahotanni game da sakamakon duba watan Ramadan a wasu kasashen Musulmi da sauransu da ke fadin duniya a yau Talata.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

