Ana Jiran Sanarwar Sarkin Musulmi, Gwamnatin Kano Ta ba da Shawarwari 4 kan Azumin Ramadan

Ana Jiran Sanarwar Sarkin Musulmi, Gwamnatin Kano Ta ba da Shawarwari 4 kan Azumin Ramadan

  • Gwamnatin jihar Kano ta fitar da shawarwarin lafiya ga al'ummarta yayin da ake shirye-shiryen fara azumin watan Ramadan
  • Ma'aikatar Lafiya ta Kano ta bukaci masu manyan cututtuka kamar Sugar, hawan jini da Ulcer su nemi shawarin likita kafin fara azumi
  • Ta kuma gargadi jama’a da su rage fita ko zama a ƙarƙashin tsananin hasken rana, musamman a lokutan zafin rana, domin gujewa rashin ruwa a jiki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Gwamnatin Kano ta shawarci mazauna jihar da su kula da lafiyarsu domin kaucewa shiga matsala ta daban a watan azumin Ramadan da ke dab da shiga.

Gwamnatin ta ba al'ummar Kano wannan shawara ne ta hannun ma'aikatar lafiya ta jihar a wata sanarwa da ta fitar yau Talata, 17 ga watan Fabrairu, 2026.

Kara karanta wannan

Jerin sharudda 15 da Sarkin Musulmi ya gindaya wa malaman da za su yi tafsiri a Ramadan

Gwamna Abba.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a taron addu'o'in neman zaman oafiya da hadin kai Hoto: Sanusi Bature
Source: Facebook

A rahoton da Tribune Nigeria ta kawo, Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano, (SMOH), ta yi kira ga al’ummar jihar da su fifita kula da lafiyarsu gabanin fara azumin Ramadan.

A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ma’aikatar, Nabilusi Abubakar K/Na’isa, ya sanya wa hannu, ma’aikatar ta jaddada muhimmancin bin ƙa’idojin kiwon lafiya a lokacin azumi domin kauce wa matsalolin da za a iya gujewa.

Shawara ga masu manyan larurori

Ma’aikatar ta shawarci mutanen da ke fama da cututtuka kamar ciwon sugar, Ulcer hawan jini da sauran makamantansu da su nemi shawarar likita kafin fara azumi.

Sanarwar ta ce ƙwararrun ma’aikatan lafiya za su iya ba da shawarwari kan yadda za a daidaita shan magunguna, tsarin abinci da kuma yadda za a yi azumi cikin aminci gwargwadon yanayin lafiyar mutum.

Ma'aikatar lafiya ta Kano ta kuma gargadi jama’a da su rage fita ko zama a ƙarƙashin tsananin hasken rana, musamman a lokutan zafin rana, domin gujewa rashin ruwa a jiki da sauran matsalolin da zafi ke haifarwa.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito kan zargin gwamnati na ba majalisar harkokin Musulunci ta Najeriya makudan kudi

Ta bayyana cewa tsawaita zama cikin zafi yayin azumi na iya haddasa asarar ruwa mai yawa a jiki da kuma wasu haɗurran lafiya masu tsanani, in ji Guardian.

Shawarwari 4 daga gwamnatin Kano

Domin tabbatar da azumi cikin ƙoshin lafiya, ma’aikatar ta ba da shawarwari kamar haka:

1. Shan isasshen ruwa tsakanin lokacin buɗa-baki (Iftar) da sahur (Suhoor)

2. Cin abinci mai gina jiki da daidaito

3. Shan magunguna kamar yadda likita ya umarta

4. Garzayawa asibiti nan take idan an ji jiri, matsananciyar kasala ko wata alama ta rashin lafiya da ba a saba gani ba

A ƙarshe, ma’aikatar ta sake jaddada aniyarta ta kare lafiyar al’ummar Kano, tare da yi musu fatan yin ibadar Ramadan cikin koshin lafiya da kuma samun lada mai yawa.

Watan Ramadan.
Musulmi na tsakiyar ibadar addu'a a masallaci Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An ga watan Ramadan a Saudiyya

A wani rahoton, kun ji cewa hukumomi a kasar Saudiyya sun sanar da cewa an ga jinjirin watan Ramadan a yammacin ranar Talata, 17 ga watan Fabrairun shekarar 2026.

Hakan na zuwa ne yayin da watan Sha'aban ya cika kwana 29 kuma al'ummar Musulmi a fadin duniya suka fita duba wata da yammacin yau Talata.

Ana sa ran fadar mai alfarma Sarkin Musulmi za ta fitar da sanarwa a hukumamce kan lokacin da musulmim Najeriya za su fara azumin Ramadan na bana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262