Majalisar Wakilai Ta Cimma Matsaya kan Dokar Zabe bayan Barkewar Rigima
- Majalisar wakilan Najeriya ta yi gyara ga bangaren tura sakamakon zabe a dokar zaben 2026 wadda ta amince da ita a baya
- A yayin zaman majalisar na ranar Talata, 17 ga watan Fabrairun 2026, an kai ruwa rana bayan da aka dauko batun yi wa bangaren kwaskwarima
- Mambobin majalisar na bangaren adawa sun nuna rashin amincewarsu da gyaran da ake yunkurin yi, inda suka fice daga zaman suna wake-waken adawa da matakin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Majalisar wakilan Najeriya ta janye matsayar da ta ɗauka a baya kan sashi na 60 (3) na dokar zaɓe.
Majalisar ta amince da nau’in da majalisar dattawa ta riga ta amince da shi, wanda ya ba da damar tura sakamakon zaɓe ta yanar gizo da kuma ta takarda.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa majalisar ta cimma wannan matsayar ne yayin zamanta na ranar Talata, 17 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan
Rigimar da ta kaure a Majalisar wakilai ta kara tsanani, wasu yan majalisa sun yi fushi
'Yan adawa sun yi bore a majalisa kan dokar zabe
Wannan amincewa ta zo ne a daidai lokacin da mambobin majalisar na ɓangaren adawa suka nuna rashin amincewarsu, inda suka fice daga zauren majalisar suna rera waƙar: “APC, ole! APC, ole!”
A baya, majalisar wakilan ta amince da sashe na 60 (3) wanda ya gindaya cewa:
“Jami’i mai jagorantar zaɓe zai tura sakamakon kowace mazaɓa ta yanar gizo zuwa shafin adana bayanan IREV, kuma hakan zai faru ne bayan an sa hannu tare da buga tambari a kan takardar sakamako ta EC8A, kuma bayan ’yan takara ko wakilansu sun sanya hannu a kai a mazaɓar.”
Majalisar wakilan tarayya ta sauya matsaya
To sai dai kuma, a lokacin zaman gaggawa da aka yi, majalisar wakilan ta amince da tsarin majalisar Dattawa wanda ya ba da wani sharadi game da tura sakamakon, jaridar Businessday ta kawo labarin.

Source: Facebook
Sabuwar sigar da aka amince da ita ta nuna cewa:

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Rigima ta kaure a Majalisar Wakilai, an fara tayar da jijiyoyin wuya a Abuja
“Jami’i mai jagorantar zaɓe zai tura sakamakon kowace mazaɓa ta yanar gizo zuwa shafin IREV bayan an kammala sanya hannu da tambari a takardar EC8A."
"Sai dai kuma, idan tura sakamakon ta yanar gizo ya gaza sakamakon matsalar sadarwa, har ta kai ga ba za a iya tura sakamakon da ke kan takardar EC8A ba, to wannan takardar (fom EC8A) ita ce za ta zama madogara ta farko wajen tattarawa da kuma sanar da sakamakon zaɓen."
Rigima ta kaure a Majalisar wakilai
A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu hayaniya a zaman gaggawa da aka shirya a majalisar wakilai don duba dokar zaben da aka amince da ita a baya.
Mambobin majalisar wakilan sun barke da hayaniya yayin da aka gabatar da kudirin janye matsayar da majalisar ta dauka a baya kan dokar zabe.
Abubuwa sun rikice a majalisar ne lokacin da shugaban majalisa, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya nemi a kada kuri’ar murya kan batun soke kudurin gyaran da suka yi a baya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng