Dauda Lawal: Gwamnatin Tinubu Ta Mayar da Zamfara Saniyar Ware saboda Muna PDP

Dauda Lawal: Gwamnatin Tinubu Ta Mayar da Zamfara Saniyar Ware saboda Muna PDP

  • Gwamna Dauda Lawal ya ce Zamfara ba ta samu tallafin gwamnatin tarayya ba tun 2023 da Bola Tinubu ya hau mulki
  • Ya danganta hakan da kasancewarsa a jam’iyyar adawa ta PDP, inda ya ya ce akwai kudin tallafi da ake raba wa jihohi
  • Dauda Lawal ya bayyana cewa duk da haka gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da ayyuka ba tare da sabon bashi ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Zamfara – Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya yi zargin cewa jiharsa ba ta taba samun wani kudin tallafi daga gwamnatin tarayya ba tun bayan hawansa mulki a shekarar 2023.

Ya bayyana haka ne a lokacin da gwamnoni ke tururuwar komawa APC mai mulki domin samun tagomashin gwamnatin tarayya.

Kara karanta wannan

Ramadan: Ana shirin fara azumi, gwamnan Zamfara ya faranta ran ma'aikata da 'yan fansho

Gwamnan Zamfara ya zargi gwamnatin tarayya da nun wariya
Gwamna Dauda Lawal, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Dauda Lawal/Bayo Onanuga
Source: Facebook

Da yake magana a wata hira da DW Hausa, gwamnan PDP, ya ce akwai jihohi da suka samu makudan kudi daga gwamnatin tarayya.

Gwamnan Zamfara ya soki gwamnatin tarayya

Jaridar Leadership ta wallafa cewa Gwamna Dauda Lawal Dare ya bayyana cewa Zamfara ba ta samu ko sisi ba face kudin da doka ta tanada.

A cewarsa:

“Gwamnatin tarayya ba ta taba ba mu wani kudin tallafi ba kamar yadda ta yi wa wasu jihohi. Ina da sahihin bayani cewa wasu jihohi sun samu sama da Naira biliyan 500, amma jihata ba ta samu ko kobo daya ba.”

Ya kara da cewa yana ganin hakan na da alaka da kasancewarsa a jam’iyyar adawa, inda ya bayyana cewa:

“Ina ganin hakan ne saboda ba mu jam’iyya daya da su ba. Ni ina jam’iyyar adawa."

Rahotanni sun nuna cewa Gwamna Dauda Lawal ne kadai gwamna daga jam’iyyar adawa a yankin Arewa maso Yamma, yayin da sauran jihohin yankin ke karkashin APC.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta gano talakawan da suka fi bukatar taimako a Najeriya

Muna aiki a Zamfara - Dauda Lawal

Duk da haka, ya jaddada cewa rashin karin tallafi daga tarayya bai hana gwamnatinsa aiwatar da ayyukan raya kasa ba.

Gwamna Dauda Lawal ya ce ba a taba ba su kudin tallafi
Gwamna Dauda Lawal Dare na jihar Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Ya ce tun bayan da ya zama gwamna a 2023, ba su samu wani karin tallafi daga tarayya ba baya ga abin da doka ta ware masu.

Gwamna Lawal ya kuma bayyana cewa gwamnatinsa ba ta karbi wani sabon bashi domin tafiyar da harkokin jihar ba, duk da kalubalen da ake fuskanta.

Ya ce wannan na da alaka da bashin da gwamnatin da ta gabata ta karba, wanda har yanzu ake biya.

Game da makomarsa ta siyasa, gwamnan ya ce ba zai sauya sheka daga PDP nan take ba duk da matsalolin cikin gida da jam’iyyar ke fuskanta.

Gwamna Dauda zai gwangwaje ma'aikatan Zamfara

A baya, mun wallafa cewa Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da a biya albashi da kudin fansho na watan Fabrairu cikin gaggawa kafin fara azumin watan Ramadan.

Kara karanta wannan

Ana ruguza allunan tallata Tinubu a Zamfara, ran jam'iyyar APC ya baci

Rahotanni sun bayyana cewa gwamnan ya bayar da umarni ga Akanta Janar na jihar da ya saki kudin ba tare da bata lokaci ba domin ma’aikata da masu karbar fansho su samu saukin shirin azumi.

Wannan mataki na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da al’adu na jihar, Mahmud Dantawasa, ya sanya wa hannu a ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairun 2026.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng