Ramadan: Ana Shirin Fara Azumi, Gwamnan Zamfara Faranta Ran Ma'aikata da 'Yan Fansho

Ramadan: Ana Shirin Fara Azumi, Gwamnan Zamfara Faranta Ran Ma'aikata da 'Yan Fansho

  • Ma'aikata da masu karbar fansho a jihar Zamfara za su fara azumin watan Ramadan cikin murna da walwala
  • Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya umarci a gaggauta biyansu albashin watan Fabrairun 2026 ba tare da bata lokaci ba
  • Dauda Lawal ya jaddada cewa babban kudirinsa shi ne tabbatar da jin dadi da walwalar ma'aikata, yayin da ya yi kira gare su da su yi wa jihar addu'o'i

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya amince da biyan albashi da fansho na watan Fabrairu cikin gaggawa gabanin azumin watan Ramadan.

Gwamna Dauda ya umarci Akanta Janar na jihar da ya saki kuɗaɗen ba tare da ɓata lokaci ba.

Gwamnan Zamfara ya amince a biya albashi saboda Ramadan
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, na jawabi a wajen taro Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce amincewar ta fito ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da al’adu, Mahmud Dantawasa, ya sanya wa hannu ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Kano: Manyan mutane da suka ziyarci kasuwar Singer bayan mummunar gobara

Gwamna Dauda ya umarci a biya albashi

“Mai girma gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya umarci Akanta Janar na jiha da ya gaggauta biyan albashin watan Fabrairu ga dukkan ma’aikatan gwamnati a faɗin jihar.”

- Mahmud Dantawasa

Sanarwar ta kara da cewa wannan umarnin yana da nufin ba ma’aikata da wadanda suka ajiye aiki damar yin shirye-shiryen da suka dace domin fara watan alfarma na Ramadan cikin kwanciyar hankali.

Gwamnan ya yi kira ga ma’aikata, masu karɓar fansho, da kuma al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan lokaci mai daraja wajen yi wa jihar addu’a, inda ya buƙace su da su:

“Mayar da hankali wajen yin addu’o’in neman dorewar zaman lafiya, haɗin kai, da kwanciyar hankali a Jihar Zamfara.”

Gwamna Dauda ya bukaci a yi wa Zamfara addu'a

Ya jaddada buƙatar ci gaba da addu’o’i domin magance ƙalubalen tsaro da ke addabar jihar, da kuma neman dorewar haɓakar tattalin arziki da ci gaba, shafin Radio Nigeria ya kawo labarin.

Kara karanta wannan

Jerin sharudda 15 da Sarkin Musulmi ya gindaya wa malaman da za su yi tafsiri a Ramadan

Gwamna Lawal ya kuma sake tabbatar da kudurin gwamnatinsa na kyautata jin daɗin ma’aikata da wadanda suka ajiye aiki, da kuma ci gaban jihar baki ɗaya.

Gwamnan Zamfara ya amince a biya ma'aikata albashi
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Hoto: Mugira Yusuf
Source: Facebook

Ya ba da tabbacin cewa jin daɗinsu shi ne babban abin da ya sa a gaba.

Daga ƙarshe, sanarwar ta isar da saƙon fatan alheri na gwamnan, inda yake yi wa:

“Dukkan Musulmin jihar Zamfara da ma sauran wurare fatan gudanar da azumin Ramadan cikin zaman lafiya da samun lada mai yawa.”

Gwamnatin Jigawa za ta ciyar da masu azumi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Jigawa, karkashin jagorancin Malam Umar Namadi, ta amince da kafa cibiyoyin ciyarwa kyauta a lokacin azumin watan Ramadan.

Gwamnatin ta amince da kafa cibiyoyin ciyarwa kyauta guda 640 a faɗin jihar domin samar da abincin buɗa baki ga mutane miliyan 7.9.

Kwamishinan muhalli, Nura Kazaure, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta shirya samar da abinci sama da miliyan 23.8 ga talakawa da gajiyayu a lokacin azumi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng