Cika Kwana 30: Masana Sun Kawo Dalilan Cewa ba za a Ga Watan Ramadan ba

Cika Kwana 30: Masana Sun Kawo Dalilan Cewa ba za a Ga Watan Ramadan ba

  • 'Dan kwamitin ganin wata a Najeriya, Simwal Usman Jibril ya bayyana cewa da wahala a ga watan Ramadan a yau Talata
  • Simwal ya bayyana cewa ya yi maganar ne bisa yadda ilimin taurari ya nuna cewa za a haifi watan amma ba za a iya ganin shi ba
  • Ya yi karin haske game da matakan da za a dauka idan jama'a suka ce sun ga wata duk da cewa ilimi ya nuna ba za a gan shi ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - 'Dan kwamitin mai alfarma Sarkin Musulmi, Simwal Usman Jibril ya bayyana cewa babu alamun za a ga watan Ramadan a yau Talata, 17 ga Fabrairun 2026.

Masanin ya bayyana haka ne dogaro da bayanin da masana ilimin taurari suka yi na cewa za a haifi watan amma ba za a gan shi ba.

Kara karanta wannan

Ramadan: Dabarun da za a yi a ga wata ido da ido a Najeriya

Dan kwamitin ganin wata, Simwal Usman Jibril
Simwal Usman Jibril da ya kware wajen duba wata. Hoto: Simwal Usman Jibril
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanan da Simwal Usman ya yi game da duba wata ne a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X.

Me zai hana ganin wata?

A shekarar 2026, Simwal ya bayyana cewa zai yi wahala a iya ganin watan Ramadan a ranar 29 ga Sha'aban, bisa lissafi irin na masana ilimin taurari

Masanin ya ce:

"Haihuwar jinjirin watan Ramadana na wannan shekarar zai kasance da misalin ƙarfe 1:01 na rana.
"Wannan na nufin cewa a lokacin da rana za ta fadi watan bai cika awa shida da haihuwa ba.

Kara karanta wannan

Dalilan da ke sanya ranakun fara Ramadan sauyawa kowace shekara

"Watan zai faɗi bayan minti 9 da faɗuwar rana a ranar Talata, wanda hakan ke nufin zai yi wahala a ga watan a ranar Talata a Najeriya".

Ya za a yi idan aka ce an ga wata?

Da yake karin bayani, Simwal ya bayyana cewa duk da maganar da masu ilimin taurari suka yi, ana samun mutanen da suke fitowa su ce sun ga wata.

A irin wannan yanayi, ya ce idan mutanen da suka ce sun ga wata suna da yawa, mai alfarma Sarkin Musulmi yana yarda da su ya sanar da fara azumi.

Simwal ya ce dama hakan shi ne koyarwar mazhabar Malikiyya kuma a kanta fadar mai alfarma Sarkin Musulmi ke tafiya wajen sanar da ganin wata.

Yadda ake duba wata a Saudiyya
Mai duba wata a kasar Saudiyya. Hoto: Inside the Haramain
Source: Facebook

Najeriya na bin ganin watan Saudiyya?

Da aka masa tambaya game da zargin cewa ko Najeriya na dogaro da ganin watan kasar Saudiyya, BBC Hausa ta rahoto Simwal ya ce a'a.

Ya kara da cewa abu ne sananne kwamitin ganin wata na Najeriya suna tsayuwa su yi aikinsu ba tare da dogara ga wata ƙasa ba.

Kara karanta wannan

Ganduje ya aika muhimmin sako ga Kwankwaso wajen zaman makoki a Kano

Ya kara da cewa wasu 'yan Najeriya ne suke karkata ga Saudiyya saboda kasar tana riga mu fara duba wata da sa'o'i biyu.

Ga bayanin da Simwal ya yi a bidiyo:

Ana shirin tafsirin Ramadan 2026

A wani labarin, mun kawo muku cewa Malaman Musulunci a Najeriya sun fara shirye-shirye gudanar da tafsirin Ramadan a azumin bana.

Shuaban Izala na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya tura malamai sama da 2,000 tafsirin Ramadan zuwa jihohi da kasashen waje.

A jiya Litinin Sheikh Muhammadu Sani Yahaya Jingir ya bude tafsirin Alqur'ani da ya saba yi duk shekara a birnin Jos, jihar Filato.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng