Hukumar EFCC Ta Tsare El Rufai, an Ji Abubuwan da Take Bincikensa a Kai

Hukumar EFCC Ta Tsare El Rufai, an Ji Abubuwan da Take Bincikensa a Kai

  • Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta titsiye Malam Nasir Ahmad El-Rufai da jerin tambayoyi
  • EFCC ta tsare tsohon gwamnan na jihar Kaduna bayan ta fara yi masa tambayoyi a ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairun 2026
  • Majiyoyi sun bayyana cewa daga cikin abubuwan da ake binciken El-Rufai a kai har da zargin daukr nauyin ta'addanci

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya fuskanci tambayoyi daga jami'an hukumar yaki da cin hanci ta EFCC.

El-Rufai ya fuskanci tambayoyin ne bayan ya amsa gayyatar da hukumar yaki da cin hancin ta yi masa a ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairun 2026.

Hukumar EFCC ta tsare El-Rufai
Nasir El-Rufai cikin mota yayin zuwa wajen hukumar EFCC Hoto: @MuyiwaAdekeye
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoton cewa hukumar EFCC ta tsare tsohon gwamnan na Kaduna bayan ta yi bincike a kan shi.

Kara karanta wannan

Zargin kutsen waya: Lauya ya jero kuskuren da ke tattare da tuhumar El Rufa'i

Hukumar EFCC ta tsare Nasir El-Rufai

El-Rufai na fuskantar bincike da kalubale na shari’a da dama daga hukumomin yaki da cin hanci da na tsaro, biyo bayan sababbin abubuwan da ke fitowa daga hukumar EFCC, DSS, da kuma gwamnatin tarayya.

A daidai lokacin gabatar da wannan rahoto, majiyoyi daga EFCC sun tabbatar da cewa tsohon gwamnan yana nan tsare a hannun hukumar a Abuja.

Baya ga binciken EFCC, gwamnatin tarayya ta hannun hukumar DSS, ta shigar da tuhume-tuhume guda uku a kan tsohon gwamnan a jiya.

Wane bincike EFCC ke yi kan El-Rufai?

Majiyoyi a EFCC sun bayyana cewa an gayyaci tsohon gwamnan ne bisa zargin almundahanar kudi da kuma tallafa wa ayyukan ta’addanci.

“Akwai bincike guda biyu da hukumar ke gudanarwa a halin yanzu. Ɗaya shi ne zargin daukar nauyin ta’addanci. Ɗayan kuma ya shafi zargin almundahar kuɗaɗen jihar Kaduna lokacin da yake gwamna."

- Wata majiya

A jiya da safe, kafin El-Rufai ya isa hedkwatar EFCC da ke yankin Jabi a Abuja, wasu rukunin masu zanga-zanga sun mamaye ƙofar hukumar domin nuna rashin amincewarsu.

Kara karanta wannan

Yadda ta kaya tsakanin El Rufai da jami'an hukumar EFCC bayan ya amsa gayyata

Jaridar Vanguard ta ce ana binciken tsohon gwamnan ne kan basussukan da aka karɓa lokacin mulkinsa, waɗanda wani kwamitin bincike na musamman na majalisar dokokin jihar Kaduna ya yi zargin cewa an yi awon-gaba da su ko kuma an yi amfani da su ba tare da bin ƙa’ida ba.

El-Rufai ya musanta waɗannan zarge-zarge, inda ya dage cewa makirci ne na siyasa.

EFCC na bincike kan Nasir El-Rufai
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai Hoto: @MuyiwaAdekeye
Source: Twitter

Yadda matsalolin El-Rufai suka fara

Tarihi ya nuna cewa matsalolin El-Rufai sun fara ne jim kaɗan bayan samun saɓani tsakaninsa da wanda ya gaje shi, Gwamna Uba Sani, inda daga bisani ya fara sukar jam’iyyar APC da gwamnatin Shugaba Tinubu.

Bayan an kai sunan shi domin tantance shi a matsayin minista, majalisar dattawa ba ta yi na'am da shi ba, a karshe ya bar Najeriya sakamakon rasa wannan matsayi a karshen 2023.

A shekarar 2024, majalisar dokokin jihar Kaduna ta zarge shi tare da wasu hadimansa da suka yi aiki tsakanin 2015 zuwa 2023 kan zargin karkatar da fiye da Naira biliyan 4 na dukiyar jihar.

Dalilin kwace fasfon Malam El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar DSS ta yi tsokaci kan dalilin da ya sanya ta kawace fasfon tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai.

Kara karanta wannan

Bayan taawon kwanaki, an ji dalilin kwace fasfon Malam El Rufai a filin jirgin Sama

Wata majiya daga hukumar DSS ta bayyana cewa kwace fasfon na da nufin hana tsohon gwamnan sake koma wa birnin Cairo na kasar Egypt.

A cewar majiyar, bayanai sun nuna cewa El-Rufai ya shirya komawa birnin Cairo na kasar Egypt bayan kammala amsa tambayoyi a wajen hukumomin yaki da cin hanci da rashawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng