Yadda Ta Kaya Tsakanin El Rufai da Jami'an Hukumar EFCC bayan Ya Amsa Gayyata
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya kai kansa gaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC)
- Jami'an hukumar EFCC sun yi wa tsohon gwamnan tambayoyi inda daga karshe suka ki barinsa ya koma gida
- Mai ba El-Rufai shawara ta musamman kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye, ya bayyana yadda abubuwa suka kaya tsakanin tsohon gwamnan da jami'an EFCC
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jami'an hukumar EFCC sun yi wa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai tambayoyi.
Hukumar EFCC ta tsare tsohon gwamnan jihar Kaduna, bayan an fara yi masa tambayoyi a ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairun 2026.

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta ce majiyoyi daga hukumar EFCC ne suka tabbatar mata da tsare Nasir El-Rufai.
A cewar majiyoyin, El-Rufai, wanda yanzu babban jigo ne a jam’iyyar ADC, ya mika kansa hedkwatar EFCC ranar Litinin bayan samun gayyata daga hukumar.

Kara karanta wannan
Bayan taawon kwanaki, an ji dalilin kwace fasfon Malam El Rufai a filin jirgin Sama
El-Rufai zai kwana hannun EFCC
Sai dai, zai kwana a hannun hukumar yayin da masu bincike ke ci gaba da yi masa tambayoyi kan zargin almundahanar kudi da aka yi a lokacin mulkinsa na gwamna.
El-Rufai ya rike gwamnan jihar Kaduna tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023.
“Yana hannunmu, kuma zai kwana a nan."
- Wata majiya
Yaushe EFCC za ta saki El-Rufai
Majiyar ta kara da cewa akwai yiwuwar a saki tsohon gwamnan bayan an kammala yi masa wasu karin tambayoyin a ranar Talata, ya danganta da yadda binciken ya kankama.
A shekarar 2024, majalisar dokokin jihar Kaduna ta zargi El-Rufai da karkatar da kudaden gwamnati har Naira biliyan 423, inda ta bukaci hukumomin yaki da cin hanci da su bincike shi.
Baya ga EFCC, hukumar yaki da cin hanci da rahawa ta ICPC ta aika wa tsohon gwamnan takardar gayyata, inda ake tsammanin za a gudanar da tattaunawa da shi a ranar Laraba.

Source: Twitter
El-Rufai zai zauna a hannun EFCC
Mai ba El-Rufai shawara kan harkokin yada labarai, Muyiwa Adekeye ya tabbatar da cewa tsohon gwamnan zai ci gaba da zama a hannun EFCC.
A wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a daren ranar Litinin, Muyiwa Adekeye, ya bayyana cewa ya tattauna da jami'an EFCC.
"Malam Nasir El-Rufai ya amsagayyatar da EFCC ta yi masa a yau. Ya yi tattaunawa ta gaskiya kuma mai ma'ana da jami'an hukumar, wadanda lauyoyinsa suka tabbatar da cewa sun nuna kwarewa sosai a cikin ayyukansu. Har yanzu yana tare da EFCC."
- Muyiwa Adekeye
Dalilin kwace fasfon El-Rufai
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar DSS ta bayyana dalilin da ya sanya ta kwace fasfo din tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai.
Wata majiya daga DSS ta tabbatar da cewa an kwace fasfon ne domin hana El-Rufai sake komawa birnin Cairo na kasar Egypt.
A cewar majiyar, bayanai sun nuna cewa tsohon gwamnan ya shirya komawa birnin Alkahira na ƙasar Masar bayan kammala amsa tambayoyi daga hukumomin EFCC da ICPC.
Asali: Legit.ng
