Ana Shirin Fara Azumin Ramadan, Farashin Kayayyaki Ya Sauka a Najeriya

Ana Shirin Fara Azumin Ramadan, Farashin Kayayyaki Ya Sauka a Najeriya

  • Hauhawar farashin kayan abinci da sauran kayayyakin amfani ya ragu a watan Janairu, 2026 yayin da ake shirin fara azumin Ramadan
  • Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ta bayyana cewa alkluman hauhawar farashi ya yi ka zuwa kashi 15.10 cikin 100 a watan Janairu da ya gabata
  • An danganta wannan raguwa da saukar farashin abinci kamar kwai, koren wake, man gyada, waken suya, man ja, masara da sauransu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta bayyana cewa alkaluman hauhawar farashi a Najeriya ya ragu zuwa kashi 15.10 cikin 100 a watan Janairu, 2026.

Wannan sauki da aka samu na zuwa ne a daidai lokacin da al'ummar Musulmi a Najeriya ke shirye-shiryen fara ibadar azumin Ramadan.

Kayan abinci.
Shinkafa, jan wake da wasu kayan abinci a cikin kasuwa a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa hukumar NBS ta tabbatar da cewa an samu saukin hauhawar farashin kayayyaki ciki har da abinci a rahoton da ta saba fitarwa na wata-wata.

Kara karanta wannan

Dalilan da ke sanya ranakun fara Ramadan sauyawa kowace shekara

Yadda aka samu raguwar hauhawar farashi

A cikin rahoton, hukumar NBS ta ce hauhawar farashin ta sauka daga kashi 15.15% da aka samu a watan Disamba 2025 zuwa 15.10% a watan Janairu 2026, wanda ke nuna ragin 0.05%.

NBS ta ce idan aka kwatanta da watan Janairu 2025, inda aka samu hauhawar farashi na 27.61%, alkaluman watan Janairu 2026 ya nuna an samu ragin kashi 12.51.

Wannan na nufin cewa hauhawar farashi a watan Janairu 2026 ta yi ƙasa sosai idan aka kwatanta da daidai wannan wata a shekarar da ta gabata.

Raguwar farashi a wata-wata

A ma’aunin wata-wata, hauhawar farashi a Janairun 2026 ta kasance -2.88%, wanda ya ragu da 3.42% idan aka kwatanta da Disamba 2025 (0.54%).

Wannan na nufin cewa a watan Janairu 2026, ƙarin da ake samu a matsakaicin farashin kayayyaki ya ragu idan aka kwatanta da watan Disamba, 2025, in ji Vanguard.

A cewar rahoton, manyan sassan da suka fi bada gudummawa ga raguwar hauhawar farashin sun haɗa da abinci da abin sha marasa giya (6.04%), gidajen cin abinci da masauki (1.95%), da sufuri (1.61%).

Kara karanta wannan

El Rufa'i ya amsa gayyata, zai kai kansa ofishin EFCC a yau

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da wasu kayayyakin abinci a kasuwa Hoto: @aonanuga1956
Source: Getty Images

Farashin abinci ya kara araha a Najeriya

Dangane da abinci, hauhawar farashin ya kasance 8.89% a ma’aunin shekara-shekara amma a ma’aunin wata-wata, ya ragu zuwa -6.02% a Janairu 2026, wanda ya sauka da kashi -5.66% idan aka kwatanta da Disamba 2025 (-0.36%).

An danganta wannan raguwa da saukar farashin abinci kamar kwai, koren wake, man gyada, waken suya, man ja, masara, dawa farin wake, naman sa, Egusi da rogo.

An samu saukin tsadar abinci a Taraba

A wani rahoton, kun ji cewa bincike ya nuna cewa farashin abinci na cigaba da sauka a wasu sassan jihar Taraba yayin da Ramadan ke kara karatowa a Najeriya.

Rahotanni daga kasuwannin Iware da Mutum Biyu sun gano cewa farashin hatsi ya sauka zuwa mafi ƙarancin farashi a cikin shekarun baya-bayan nan.

Farashin shinkafa, wake, gero da wasu kayyakin abinci da ake amfani da su a yau da kullum na cikin wadanda suka kara sauka a kasuwannin jihar Taraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262