Abubuwan da Ya Kamata Ku Fahimta game da Kudirin 'Yan Majalisar Amurka kan Kwankwaso
Kano, Nigeria - A yan makonnin da suka shige, 'yan Majalisar dokokin Amurka sun gabatar da wani kudiri da ya zargi jagoran NNPP na kasa, Rabiu Musa Kwankwaso da hannu a tauye 'yancin addini a Najeriya.
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kudirin ya nemi Majalisar dokokin Amurka ta duba yiwuwar daukar mataki kan Kwankwaso da wasu kungiyoyi kan zargin muzgunawa kiristoci a Najeriya.

Source: Twitter
Bussines Day ta ce dan Majalisa Riley Moore da takwaransa, Chris Smith ne suka jagoranci gabatar da kudirin a Majalisar Amurka, inda suka yi ikirarin cewa sun gano abubuwa da dama.
Wannan lamari ya ja hankalin 'yan Najeriya, inda wasu daga cikin shugabanni da jiga-jigai suka fito suka yi fatali da zargin 'yan Majalisar Amurka kan Sanata Rabiu Kwankwaso.
A wannan rahoto, Legit Hausa ta yi nazari kan lamarin tare da tattaro abubuwan da ya kamata mutane su sani kan kudirin Majalisar dokokin Amurka da ya zargi Kwankwaso da cin zarafin Kiristoci.
Me yasa 'yan majalisar Amurka ke zargin Kwankwaso?
Duk da ba su bayyana dalilansu ba, amma ana ganin 'yan Majalisar Amurka sun fara zargin Kwankwaso ne saboda aiwatar da tsarin shari'ar musulunci da ya yi a Kano a 2000.
Kwankwaso da 'dan Majalisa Moore sun yi musayar yawu bayan tsohon gwamnan Kano ya fito ya yi fatali da matakin Amurka na sanya Najeriya a jerin kasashen da take zargi da tsauye hakkin Kiristoci.
A sakon da ya wallafa a shafin X, Kwankwaso ya nuna damuwa kan matakin da Shugaba Donald Trump ya dauka, yana mai cewa Najeriya kasa ce mai 'yanci kuma matsalar tsaronta ya shafi kowane addini.
Da yake maida martani ga Kwankwaso, 'dan Majalisar Amurka, Moore ya soki Kwankwaso, yana mai zarginsa da hannu a kisan kiristoci saboda ya kafa shari'a a Kano.
Moore ya ce:
"Gwamna, shin kana maida martani ne kan hannun da ka ke da shi wajen kisan Kirsitoci? Ka kafa shari'a, ka sanya hannu kan dokar da ta tanadi hukuncin kisa kan abin da ku ka bayyana da saɓo (batanci)."
Har zuwa yanzu, Legit Hausa ba ta da labarin Kwankwaso ya tanka Moore wanda yake cikin 'ya 'yan jam'iyya mai mulkin Amurka da ke kokarin kiristocin duniya.

Source: Getty Images
Yadda Kwankwaso ya kawo shari'a a Kano
Kano na daya daga cikin jihohin Arewa da suka amince da tsarin shari'ar musulunci bayan Zamfara da ta zama ta farko wajen kaddamar da shari'a lokacin mulkin Ahmad Sani Yerima.
An fara amfani da tsarin shari'a a Kano a shekarar 2000 karkashin mulkin Kwankwaso na farko, sai dai lamarin ya ja hankali matuka.
Rahoton BBC Hausa ya nuna cewa Kiristoci sun rika sukar matakin, wanda ya sa Kwankwaso ya rika jan kafa wajen aiwatar da tsarin yadda ya kamata a zangon mulkinsa na farko.
Bayan Zamfara da Kano, jihohin da suka biyo bayansu wajen kafa tsarin shari'ar Musulunci su ne Sakkwato, Katsina, Kebbi, Kaduna, Jigawa, Gombe, Bauchi, Borno, Yobe da Neja.
Shin Amurka za ta dauki mataki kan Kwankwaso?
Amurka na iya daukar mataki kan Kwankwaso idan kudirin da aka gabatar a Majalisar Dokokin kasar na kakaba takunkumi kan ’yan Najeriya da ake zargi da take ’yancin addini, ya samu karbuwa.
A ƙarƙashin kudirin, ana iya kakaba wa Kwankwaso takunkumi na musamman kamar hana ba shi biza zuwa Amurka da karbe kadarorinsa, kamar yadda jaridar Ripples Nigeria ta kawo.
Wannan na iya faruwa ne bisa Dokar Global Magnitsky Human Rights Accountability Act, wadda ke bai wa gwamnatin Amurka damar kakaba takunkumi kan waɗanda ake zargi da take haƙƙin ɗan Adam.
Kwankwaso ya samu goyon baya a Najeriya
Tun bayan gabatar da wannan kudiri a Majalisar dokokin Amurka, aka fara muhawara a kansa a Najeriya, inda galibin mutane suka nuna goyon baya ga tsohon gwamnan Kano.
A cewar wasu daga cikin wadanda suka maida martani, bai kamata a ga sunan Kwankwaso kadai ba domin ba shi kadai ba ne ya kafa tsarin shari'a, sannan sun ce tsarin bai saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya ba.
'Daya daga cikin sanannun mutanen da suka soki matakin Amurka akwai tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, wanda ya yi zargin cewa mai yiwuwa da hannun gwamnatin Najeriya.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa El-Rufa'i ya bayyana cewa ba daidai ba ne a ware Kwankwaso shi kaɗai, alhali jihohi da dama a Arewa sun aiwatar da tsarin Shari’a.

Kara karanta wannan
"Ƙila don ya ƙi APC ne": El Rufa'i ya yi tir da kai sunan Kwankwaso majalisar Amurka
El-Rufai ya ce:
"Jihohin 12 na Arewa ne suka aiwatar da Shari’a. Jiha ta farko da ta fara ita ce Zamfara. Ina ganin kamata ya yi a fara ambaton Zamfara idan har za a dora wa wani laifi kan wannan lamari.”
NNPP ta roki Tinubu ya wanke Kwankwaso
A wani rahoton, kun ji cewa NNPP ta roki Shugaba Bola Ahmed Tinubu da mai bada shawara kan tsaron kasa (NSA) su wanke Sanata Rabiu Kwankwaso daga zargin Amurka.
Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labarai na NNPP a jihar Kano , Injiniya Ibrahim Karaye, ya sanya wa hannu.
Jam’iyyar ta bayyana Kwankwaso a matsayin ɗan Najeriya mai kishin ƙasa, tana mai cewa tarihin aikinsa a fannin ilimi da yiwa talakawa hidimi ya isa shaida a kansa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


