Bukarti: Abubuwa 3 da Najeriya Za Ta Kiyaye bayan Sojojin Amurka Sun Sauka Borno

Bukarti: Abubuwa 3 da Najeriya Za Ta Kiyaye bayan Sojojin Amurka Sun Sauka Borno

  • Amurka ta fara tura dakarun ta da masana bayanan sirri har 200 zuwa jihar Borno domin taimaka wa Najeriya a yaki da ta'addanci
  • Rahotanni sun bayyana cewa za samu karin saukar sojoji da jiragen yakin Amurka a wasu sassan Najeriya da ke fama da 'yan ta'adda
  • Masanin tsaro, Audu Bulama Bukarti ya gargadi Najeriya da kada ta kuskura ta mika ragamar komai a hannun sojojin Amurka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Borno - Rahotannin kafofin yaɗan labarai na ƙasa da ƙasa a ƙarshen mako sun nuna cewa jiragen yaƙin Amurka da rukunin farko na dakarunsu sun isa Borno.

Ana ganin cewa, isar sojoji da jirgin yakin Amurka a jihar Borno na daga cikin yarjejeniyar taimakekeniya tsakanin Najeriya da Amurka kan tsaro.

Sojojin Amurka sun isa Maiduguri don taimakawa a yaki da 'yan ta'adda
Sojan Najeriya Manjo Janar B.T. Ndiomu (hagu) tare da sojan Amurka Kanal Patrick Doyle (dama). Hoto: STEFAN HEUNIS / Getty Images
Source: Getty Images

Jirgi dauke da sojojin Amurka ya isa Borno

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare: Jiragen yakin Amurka sun sauka da manyan makamai a Najeriya

A cewar rahoton jaridar The New York Times, wani jirgin yaƙin Amurka ya sauka a Maiduguri ranar Alhamis da daddare dauke da wasu jami'ai.

Jami'an tsaron Amurka sun bayyana cewa dakarun sun hada da masana bincike, masu ba da shawara, da masu horar da sojoji guda 200 da aka tura.

Aikin dakarun shi ne tallafa wa dakarun Najeriya wajen tsare-tsare, tattara bayanan sirri, da sauran ayyukan yaƙi da ta'addanci ba tare da shiga fagen yaƙin kai tsaye ba.

Wani jami'in tsaron Amurka ya ce:

"Wadannan jiragen su ne na farko a cikin jerin sufurin jiragen C-17 da za su rika sauka a manyan wurare uku a Najeriya.
"Wannan na nuni da cewa za a ci gaba da samun zirga-zirgar dakarun da kayan aiki a cikin makonni masu zuwa baki daya."
Sojojin Amurka sun isa Maiduguri domin taimakawa sojojin Najeriya don yakar 'yan ta'adda.
Wasu sojojin kasar Amurka a bakin aiki. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Matsayar hukumomin tsaron Najeriya

Hukumomin tsaron Najeriya sun jaddada cewa jami'an Amurka ba za su shiga sahun gaba na fafatawa kai tsaye da ƴan ta'adda ba, in ji rahoton The Guardian.

Hukumomin Najeriya sun ce dukkan umarni da ikon tafiyar da ayyukan tsaro za su ci gaba da kasancewa a hannun jami'an tsaron Najeriya ne kawai.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun kai wasikar kai hari kauyuka, mutane sun fara gudu

Masu lura da lamura sun ce wannan ci gaban ya yi daidai da yarjejeniyar tsaro dake tsakanin ƙasashen biyu wajen yaƙar ƙungiyoyin ta'adda a tafkin Chadi.

"Abubuwan da ya kamata a kiyaye" - Bukarti

A zantawarsa da BBC Hausa, wacce ya wallafa a shafinsa na Facebook, masanin tsaro, Audu Bulama Bukarti, ya yi gargadin cewa:

"A kula matuka ba a kai hare-hare kan fararen hula ba. Idan aka samu kuskuren kai hari kan sansanin 'yan gudun hijira, ko wani kauye, ko wasu masallata, to zai yi mummunan illa ga Najeriya da Amurka.
"Abu na biyu a tabbatar da cewa Amurka taimaka wa sojojin Najeriya za su yi kurum ba wai su karbe aikin sojojin Najeriya ba ta yadda idan suka tafi ba za mu iya kare kanmu ba.
"Abu na uku, a tabbatar aikinsu yana da kayyadadden lokaci, ga iya aikin da za su yi, kuma idan suka gama a tabbatar sun tafi, kada a basu sansani na dindindin a Najeriya bayan an gama yaki da Boko Haram."

Saurari tattaunawar a nan kasa:

Kara karanta wannan

Da sake: ADC ta dura a kan Tinubu saboda yunkurin kama El Rufa'i

Amurka za ta kafa tashar jiragen yaki

A wani labari, mun ruwaito cewa, Amurka ta fara tattaunawa da Najeriya domin kafa sansanin sojoji, wanda za ta rika zuba wa jirage marasa matuka mai.

Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta bukaci kafa wannan wuri a Abuja ko Legas, amma gwamnatin tarayya ta ki amincewa saboda wasu dalilai.

Wani jami'i da ke da masaniya kan lamarin ya ce a yanzu an fara duba yiwuwar bude wannan tasha a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com