Tinubu Ya ba da Umarni kan Gobarar da Ta Babbake Kasuwar Kano

Tinubu Ya ba da Umarni kan Gobarar da Ta Babbake Kasuwar Kano

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya jajantawa al'ummar Kano kan iftila'in gobara da ya afku a jiya Asabar 14 ga watan Fabrairun 2026
  • Tinubu ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan gobarar da ta sake aukuwa a Kasuwar Singer ta Kano
  • Ya nuna alhini kan yadda gobarar ta sake faruwa karo na biyu cikin makonni biyu, yana mai cewa lamarin ya zama abin damuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi alhini game da abin bakin ciki da ya faru a Kano a jiya Asabar 14 ga watan Fabrairun 2026.

Tinubu ya umarci a gudanar da cikakken bincike kan yawaitar gobarar da ke tashi a Kasuwar Singer da ke Kano.

Tinubu ya jajantawa yan kasuwar Singer
Shugaba Bola Tinubu da Abba Kabir. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Tinubu ya tura sako game da gobara a Kano

Kara karanta wannan

Abin da ake zaton ya jawo gobarar da ta laƙume miliyoyin Naira a kasuwar Singer

Hakan na cikin wata sanarwa da hadiminsa a bangaren yada labarai, Bayo Onanuga ya wallafa a X a yau Lahadi 15 ga watan Fabrairun 2026.

Hakan ya biyo bayan sabuwar gobara ta lalata dukiyoyin al'umma da ta ci har safiyar yau Lahadi 15 ga watan Fabrairun 2026.

Shugaban ya bayar da wannan umarni ne bayan gobarar da ta tashi a yammacin ranar Asabar ta ci gaba har zuwa safiyar Lahadi, inda ta jawo asara mai yawa ga ’yan kasuwa, Tinubu ya ce maimaituwar gobarar na jefa ’yan kasuwa cikin bakin ciki.

Sanarwar ta ce shugaban ya tuntubi gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, domin samun cikakken rahoto kan lamarin da ya bayyana a matsayin abin takaici.

Tinubu ya ba da umarni kan gobarar kasuwar Singer
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Halin da Tinubu ya shiga kan gobarar

An ce Shugaban ya damu matuka da cewa sabuwar gobarar ta faru ne kasa da makonni biyu bayan wata gobara ta lalata shaguna da kadarori da dama a kasuwar.

Sanarwar ta ce:

"Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya jajanta wa ’yan kasuwa da al’ummar Jihar Kano kan mummunar gobarar da ta tashi a kasuwar Singer ta Kano a ƙarshen mako.

Kara karanta wannan

Ramadan: Umarnin da Saudiyya ta ba al'ummar Musulmi game da duba jinjirin wata

" Shugaban ƙasar ya nuna matuƙar damuwa ganin cewa wannan lamari ya faru ne kasa da makonni biyu bayan wata gobara ta lalata shaguna da dukiyoyi masu yawa a kasuwar.
"Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan musabbabin gobarar kasuwannin, waɗanda sau da dama ke jefa ’yan kasuwa cikin halin ƙunci da takaici."

Ya jajanta wa ’yan kasuwar da al’ummar jihar Kano, yana mai tabbatar musu da kulawar gwamnatin tarayya yayin da hukumomi ke tantance asara da daukar matakan kariya.

Kwankwaso ya jajanta wa yan kasuwar Singer

Kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna alhini kan sabuwar gobarar da ta tashi a kasuwar Singer da ke Kano a ranar Asabar 14 ga watan Fabrairun 2026.

Tsohon gwamnan Kano ya aike da sakon jaje ga ‘yan kasuwar da suka yi asara, yana kira da a kawo daukin gaggawa.

Kwankwaso ya roki hukumomi, jami’an tsaro da masu hannu da shuni su hada kai wajen tallafa wa wadanda abin ya shafa domin saukaka masu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com