Ta Faru Ta Kare: Jiragen Yakin Amurka Sun Sauka da Manyan Makamai a Najeriya
- Rahotanni sun nuna jiragen sojin Amurka uku sun sauka a wasu jihohin Arewa maso Gabas dauke da alburusai
- Amurka ta fara turo jami’an leken asiri da masu horaswa 200 domin taimaka wa sojojin Najeriya a yaki da ‘yan ta’adda
- Masana tsaro sun ce hadin gwiwar Amurka da Najeriya zai kara karfin yaki da ta’addanci amma dole ne a kiyaye ikon kasa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Maiduguri, Borno - Rahotanni sun bayyana cewa akalla jiragen sojin kasar Amurka uku sun sauka a sansanonin soja da ke jihar Borno.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa matakin ya shafi wasu jihohin Arewa maso Gabas tsakanin ranar Alhamis da Juma’a 13 ga watan Faburairun 2026.

Source: Getty Images
Musabbabin kawo makamai daga Amurka
Rahoton The New York Times ya ce wasu manyan hafsoshin rundunar tsaro sun tabbatar da cewa jiragen sun dauko alburusai da gwamnatin Amurka ta aika domin tallafa wa Najeriya a yakin da take yi da ‘yan ta’adda.
Daya daga cikin jami’an ya ce bayan tattaunawar tsaro tsakanin kasashen biyu, Amurka za ta samar da kayan aiki da alburusai tare da turo jami’ai domin taimakawa.
Rahotanni sun ruwaito cewa jiragen sojin Amurka sun sauka a birnin Maiduguri, babban birnin Borno, inda aka ga ana sauke kayan aiki.
Wani jami’in Ma’aikatar Tsaron Amurka ya shaida cewa wadannan jirage na daga cikin jerin jiragen C-17 da za su ci gaba da sauka a wurare uku a fadin Najeriya.
A bangare guda, an ce jirgin sojin Amurka C-130J ya sauka a filin jirgin saman Kaduna daga Ghana, lamarin da ya haifar da hasashen cewa za a yi amfani da Kaduna wajen horas da sojojin Najeriya.

Source: Getty Images
Alkawarin turo sojoji Najeriya da Trump ya yi
Tun a shekarar 2025 ne shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa zai tura sojoji Najeriya idan ba a dakile kashe-kashen Kiristoci ba.
An ruwaito cewa Amurka ta fara turo jami’an leken asiri da masu horaswa 200 domin taimakawa sojojin Najeriya a ayyukan yaki da ta’addanci, cewar Punch.
Masana tsaro sun bayyana cewa Amurkawa ba su zo da sojojin fada ba, sai dai kwarewa ta fasaha, musamman kan amfani da jiragen yaki marasa matuki da hare-haren sama na zamani.

Kara karanta wannan
Bayan turo sojoji, Amurka za ta kafa 'tashar jiragen yaki' a a jihar Arewacin Najeriya
Sai dai sun gargadi cewa dole ne Najeriya ta tabbatar da cikakken ikon kasa, tare da guje wa duk wani abu da zai kawo cin mutunci ko tauye ‘yancin kai.
Amurka ta magantu kan zanga-zangar Iran
Mun ba ku labarin cewa rahotanni sun fito game da yadda kasar Amurka ta jawo karancin Dala a Iran domin tunzura jama'a su cika titunan kasar da zanga-zanga.
Ministan tattalin arzikin kasar Amurka, Scott Bessent ne ya fito da wasu bayanai game da zanga-zangar da aka yi a Iran da ta dauki hankali.
Shugaba Donald Trump ya sha gargadi ga kasar Iran a lokacin zanga-zangar, yana mai cewa zai kai dauki idan aka aka kashe matasa.
Asali: Legit.ng
